← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 98

Sashe 33

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Binafa, nan dai suka ci-gaba da hira wanda duk rabi akan shagalin bikin da zasu yi ne idan aurenta da Aminu ya tabbata. Kiran daya shigo wayar Najwa shine ya katsesu ta buÉ—e jaka ta É—auko sai ta waro idonta waje tana ce musu.

Wallahi Hauwa ce ta kira ni fa.

ÆŠauka! É—auka muji me zata ce.

Cewar Nafeesa cike da zaƙuwa, Najwa tayi gyaran murya kana ta zauna gefen gado kafin ta ɗauki kiran da sallama wanda har ya kusa katse wa, Hauwa ta amsa sai suka gaisa kana tace.

Najwa na kiraki ne inyi miki albishir cewar Aminu ya amince da zai aureki, kuma nasan kin samu labarin ya saki Sameeha ko?

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yaushe? Me ya faru ya saketa?

Wlh kadarinta ne ya karye duk asirin da take masa munyi nasarar ya bar jikinsa, shi da kansa yace ya gaji da ita har saki uku yayi mata abu kamar almara.

Taf amma wannan abu da ban mamaki yadda yake mugun son Anty Sameeha ace lokaci guda ya saketa, anya ba wani laifin dai tayi masa ba ya saketa kuwa?

Ya tabbatar mana da ba laifin da tayi masa shine dai ya gaji da ita ya saketa, alamu sun nuna kamar ya haÉ—u da wata mace ne ta nima rikita masa kwakwalwa da har ya saki Sameeha.

Wayyo Allah banji mata daÉ—i ba wlh.

Najwa tace cikin marairaice murya. Hauwa da ta ji haushin maganarta.

Amma ban san ke sakarya bace sai yanzu, ke da zaki yi murna da rabuwarsu zaki aure shi, dan haka ki ma fara shiri Aminu baida wata mata sai ke dan ke tamu ce.

To Yaya ina godiya Allah ya bar ƙauna ya saka miki da Alkairi, ina jin daɗin yadda kike mini kuma In Sha Allah zan miki biyayya bazan taɓa baki kunya ba.

Amma naji daÉ—in furucinki Allah ya yi miki albarka idan komai ya daidaita zaki jini.

Najwa ta yi mata godiya sai suka yi sallama suka kashe wayar, Najwa ta kwashe da dariya tana cewa.

Da sannu kowai zai zama nawa, ai kunji hirarmu da ita, dan volume din wayata yanada ƙarfi ana ji.

Munji komai sai dai basu san ke ce shegiyar da kika haɗa komai ba, amma nayi mamakin yadda ya ɓoye maganar ya kamamu da ita, mai yasa ya rufa mata asiri? wlh naso kowa yaji yadda zata sha wuya kafin ta auru, daga nan sai ta faɗa irin harkanmu gadan gadan.

Cewar Binafa, sai a lokacin Najwa ta tuna da ya rufa mata asiri sai tace.

Wlh nima banji daɗi daya rufe maganar ba, naso ace kowa yaji yadda 'yan uwansa zasu ƙara tsanarta.

Amma kuma kun san dole yaso rufe maganar ko dan kare mutuncin 'ya'yansa.

Cewar Nafisa, nan suka gasgata zancenta akan ya rufe maganar ne saboda yaransa, Najwa tace.

Yo ni ko a haka kasuwa ta tashi ai ɗan koli yaci riba, koda bai fallasa ba buƙata ta biya, saura ƙiris dai na ganni a wannan tamfacecen gidan na zuba mulki na yadda nake zo.

Kina wuta ƙawata ina binki da fetur.

Cewar Nafisa sai ta bata hannu suka tafa, Binafa ta miƙe tana cewa zata yi wanka ta shirya ta wuce gida, sai ta shige bayi, Nafisa da Najwa suka cigaba da hirarsu cike da farin ciki.

*****

Hauwa.

Lokacin da suka baro gidan Aminu a hanya su Alhasan sai ɓaɓatu suke yi, rabin zancensu dai akan dole zasu nimawa Aminu maganin sammu domin sun gama yarda asiri aka yi masa, har suka isa ƙofar gidan Hauwa suka sauketa sai suka wuce gida. Hauwa da wani irin farin ciki ta shiga kamar an yi mata kyauta kujerar hajji, ta kasa rufe farin cikinta har sai da ta faɗawa yaronta maganar, yace Allah ya kyauta yanzu sai su aura masa wacce tasan darajan mutane, Hauwa tace.

Ai tuni ma na samo masa dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, ba zama an saci ɗan ɓarawo. Wlh yadda nake ji kamar na zuba ruwa a ƙasa nasha, kadarin Sameeha dai ya karye munga ƙarshen rashin mutunci da fitsara.

Ta ƙare maganar tana tafa hannu tare da 'yar dariya sai ta wuce ɗakinta ta zauna bakin gado ta lalubo number ɗin Adama, ta danna kira bata yi tunanin dare yayi ba haka, cikin barci Adama taji wayarta na ƙara a falonta, dan ta saka a chaji ta kwanta saboda basu ciki samun wuta ba a unguwarsu shiyasa bata wasa da saka chergy in sun kawo, kamar ba zata tashi ba mijinta Kamis ya juyo yana cewa.

Ke Adama tashi kamar wayarki naji tana ƙara a falo.

Wlh naji duk wanda ya damu da kiran ya ƙara kira da safe, yanzu kusan sha buyun dare fa.

Kika san kiran mai muhimmanci ne gwara kije kiji.

Ba dan ranta yaso ba ta fita falo wanda har kiran ya tsinke wani ya sake shigowa, a fusace taje ta É—auki wayar sai dai sunan wacce ta gani yasa ta É—an saki ranta tare da mamakin meyasa Mama zata kirata a wannan daren, kiran na gab da katse wa ta É—aga tana cewa.

Mama Allah yasa lafiya irin wannan kiran cikin dare, walh ina barci naji ƙara kamar bazan taso ba ashe ke ce.

Adama albishir na kira nayi miki akan Aminu dai ya saki Sameeha saki uku.

Kai dan Allah mama, me tayi masa haka? amma wannan labari ya min sugar.

Nan Hauwa ta kwashe komai daya faru a gidan Aminu ta faÉ—a mata a takaice, Adama cikin tsantsar farin ciki tace.

Ai dama ance ƙarshen alewa ƙasa wlh, aniyarta dai ta bita kuma Allah ya rabashi da auren wata mai kalar halinta dan bana fata a ƙara, ace mace sai baƙin hali da raina mutane tare da ɗagawa kamar wata ɗiyar gomna.

Kuma 'yar gidan malam Shehu ce ba, ai ɗan talaka wani bai iya samun guri ba Adama, Allah dai ya kyauta sai da safe in kin samu shigowa to sai ki zo mu kyarasa maganar dan yanzu zamu fara fafutukar aura masa wacce muka zaɓa masa kafin ya tubure.

Idan Kamis ya barni zan zo mama sai da safe.

Cewar Adama tana kashe wayar sai ta saka a silent ta mayar chergy ta koma ciki, Kamis duk yaji hirarsu, data koma ciki yake cewa.

Yanzu auren wata dan ya mutu ake kiranki a faÉ—a miki har kina murna, to naji kina inna barki zaki je? to ba inda zaki wlh.

Haba Kamis mama ce tace naje fa, kuma matar kawuna É—in nan da nasha baka labarinta ba tada mutunci itace aka saka.

To Allah ya kyauta ya tsayar akanta, amma fa ba inda zaki bana son yawan fitar nan.

Adama ta turo baki dan sosai take jin haushin wannan mulkin da yake zuba wa, dole zata nima maganin mallaka ta yi maganinsa.

ayi namiki sai kafiya da gadara kamar mutanen farko, aiko zan yi maganinka.

Tace a ranta tana gyara zama kwanciya.

Hauwa kuwa a wannan dare barci ɓarawo ya kwasheta dan tsabar murna ta kasa sukuni sai tunanin yadda zata haɗa auren Najwa da Aminu kawai take yi. Koda gari ya waye taso taje babban gida da sassafe amma sanin 'yan uwanta basu fita aiki yasa ta haƙura har sai kusan goma na safe kafin ta isa gidan, a tsakar gida ta soma kwalawa Sa'a da Laure kira dan hirar bana cikin ɗaki ba ne, tasan sun jita yasa ta koma ƙasan bishiyar mangoro ta zauna a kan wata ƙaramar kujera data gani, ba jimawa Sa'a ta fito can sai ga Laure itama ta fito nan fa suka shiga gaisawa Laure tana cewa.

'Yar halak kinƙi ambato yo shiri nake na garzaya gidanki kika rigani, ashe dai anyiwa shafaffiya da mai checking out jiya.

Wlh haka nima Kamalu yake faɗa mini duk hankalinsa a tashe da kyar yayi barci, ni ko barcina nasha cike da farin cikin an yi waje da ita munga ƙarshen wulaƙanci.

Cewar Sa'a tana dariya, Hauwa tayi shewa tana tafa hannu.

Daɗina da gobe saurin zuwa yau dai ƙaryar Sameeha ta ƙare, amma fa naso ace tana nan akayi bikin Salma dan taga yadda zamu tsaɓa ado ta gane ba ita kaɗai bace take shigar manyan atamfofi da leshi.

Ke gwara da akayi haka kinga zamu yi shagalinmu a gidan ba tare da ta saka mana ido ba muyi yadda muka ga dama.

Cewar Laure, Sa'a ta mele baki.

Allah yasa ya bari muyi taron a can dan kun san dai halin Aminu murÉ—aÉ—É—en mutum ne.

Yama isa ya hanamu shagalinmu a gidan, yo duk da gidansa ne ai muma muna da iko akansa dole ma ya barmu musha bidiri. Yanzu kunsan me nazo muku da shi so nake mu fara maganar bikin wannan yarinya Najwa da Aminu domin mu ƙara gunnusawa Sameeha ta haɗiye rai ta mutu dan ubanta. Kuma anjima nan zamu dira a gidansu su bamu yara dan bata isa tace zata riƙe su ba, koni zan riƙe 'ya'yan Aminu na basu tarbiyyar da ya dace.

Ina bayanki wlh dan ƙafata kafarki tare zamu je mu yaga biradi mu yarda leda son ranmu, yo ai yanzu ne lokacin da zamu rama duk wani cin mutunci da tayi mana wlh.

Cewar Laure tana tafa hannu, Sa'a ta riƙe haɓa tana cewa.

Ni dai ba zani ba dan nasan Halin Kamalu sai ya huce haushinsa a kaina, amma badan shi ba wlh sai na je na bawa ido abinci naga idon mara kunya.

Ai wlh ke ce kike bawa Kamalu dama yake yi miki mulkin mallaka, ki daina tsoronsa yadda zaki ji dadin rayuwarki, dan ni Wlh Alhasan bai isa ba ni da shi kar ta san kar ne, sai dai ya gama bambamin faÉ—arsa ya rabu dani.

Gaya mata dai Laure dan na kula kan Sa'a har yanzu yana a murfi bata san kan dawon garin ba, kinga dai su 'yan uwana ne ko amma wlh ban goyi bayan ku riƙa jin tsoronsu ba ai maza ba a yi musu haka tunda ba bayi suka aura ba, dole sai kin tsaya tsayin daka kin karɓawa kanki 'yan ci. Ni yanzu Sa'a ɗauko tabarma ku zauna mu tattauna batun auren Aminu da yarinyar nan tun kafin yazo yace ya fasa.
Chapter 33 · 0% Book details