← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 98

Sashe 63

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barka da safiya mai babban suna fatan ka tashi lafiya ya kwanan iyali? Na duba ka a WhatsApp sai naga baka hau ba shiyasa na gaisheka ta nan, ka yini lafiya.

Guntun murmushi yayi yana cewa a fili.

Allah mai mutane kowa da irin halinsa da tunaninsa, ita Najwa da zan aura bata damu da saƙo haka ba amma ga wata ta damu dani.

Ya kuma sakin murmushi kana ya miƙe ya wuce zuwa bedroom dan yayi wanka ya fita zuwa gurin wani likita da aka haɗashi dashi domin tattauna matsalarsa.

****

Nafeesa.

Tunda ta bar gidansu Najwa take tunanin yadda zata kira Aminu, harta isa gida tana tunani, da yake ba wani aiki zata yi ba sai ta kwanta a gado ta hau facebook tana duba abubuwan da mutane suka ɗaura, a nan taci karo da wani video na wani malami da yake magana akan Monzon Allah s.a.w, yayi bayani sosai akai, wannan ne ya bata damar yin tunanin hanyar da zata ɓullowa Aminu kuma cikin ikon Allah tayi nasara har ya ɗauki wayarta kuma ya saurareta, wato taci arzikin Manzon Allah s.a.w kuma ga dukkan alamu zata cimma nasara tunda ta kula Aminu yana da sauƙin kai, koda gari ya waye ta duba shi a WhatsApp bai hau ba sai ta yi masa saƙo duk da bata saka a ranta zai mata Reply, ta ɗan tsaya kaɗan bayan ta tura taji shuru sai kawai ta kunna data ta cigaba da sabgoginta, ba jimawa Najwa ta kirata take sanar da ita abinda Shamsu yayi mata jiya, Nafeesa kamar zata kwashe da dariya dan ba karamin daɗi taji ba dama sai da tayi addu'a akan kar Allah ya bata nasara dan ta fara gajiya da son zuciyar Najwa, sai tace cikin kulawa.

Gaskiya banji miki daɗin haka ba, yanzu yasa kin ji kunya, amma ni shawarar da zan baki ki ɗaure kije har gidan Sameeha ki bata haƙuri na san zata yiwa Ikram magana ta yafe miki, kin ga saiku koma zumuncinku ba tare da wani tangarɗa ba.

Allah ya kyauta naje na sauke kaina gaban Sameeha, ai ni dasu mun raba jaha kowa tashi ta fissheshi, dama an gaya miki inna auri Aminu zan yarda muyi hurÉ—a dasu ne, hmmm nifa wlh bani ba su, kuma Shamsu yaci bashi saina yi masa mummunar tabo da ba zai manta ni ba, dani yake wasa.

Daɗi na dake Najwa riƙo baki da yafiya, kuma fa ke ce mai laifin amma sai kiyi kicin kicin ki azawa mutum, kawai ki bar komai ya wuce ki fuskanci aurenki tunda ya kusa.

Hmmm Nafeesa naga kin fara saduda kina bin bayan su Sameeha, kodai da wata a ƙasa ban sani ba.

Haba Najwa duk abinda nake faɗa miki domin cigabanki ne kuma kin san ke tawace bazan taɓa juya miki baya ba, kiyi tunani da kyau, ba kida kuɗi ko ƙarfin da zaki tunkari Shamsu ki rama abinda ya yi miki, dan wlh idan kika dage sai kin rama to kwaɓarki zata yi ruwa kuma ina mai tabbatar miki da zaki saka kanki a matsala, suna da mulki da kuɗi ke kuma ba ki da komai tunda baki auri Aminu ba balle kiyi tutiya dashi.

Hmmmm Najwa ta sauke ajiyar zuwa domin duk maganar Nafeesa gaskiya ce, hakan yasa ta karaya tace cikin sanyin jiki.

Shikenan na bar komai ya wuce, amma yaushe zamu haÉ—u mu fara shirin bikina tunda lokacin ya fara matsowa zan mayar da hankali akan haka.

Yauwa ko kefa, kibari next week mu huta sosai lokacin sai mu haÉ—u mu yi maganar, sannan ya batun zuwa gurin malamin dana baki shawara.

Sai kin zo muyi maganar.

Cewar Najwa, da haka suka yi sallama. Haka Najwa ta kama ƙumbiya ƙumbiyarta bata bari Inna ta gane komai ba, dan dagewa tayi ba tada lafiya shiyasa bata je gidajen Amare ba, saboda Inna ta matsa lallai sai taje amma ganin ba lafiya ce da ita ba yasa ta rabu da ita kuma yadda ma taga bata fita ko ina yasa ta yarda da rashin lafiyar nata har tana saka Sadiq yana siyo mata magani.

*****

Sameeha.

Satinsu ɗaya da amarci Ibrahim ya koma Abuja a cewarsa sati na sama zai zo ya tafi da ita, to tunda ya tafi ta tare a sashin Hajiya barci ne kaɗai ke mayar da ita ɓangaren ta, ba karamin daɗi Hajiya taji ba saboda yadda Sameeha ta mayar da ita mahaifiyarta, in dai tana sashin bata bari ta kauda ko tsinke ita ke komai hatta abinci ita ke dafa musu bata bari masu aiki su girka, cikin ƙanƙanin lokaci ta shaƙu sosai da Hajiya tun tana kunyarta har ta ware suke shan hirarsu. Ikram ma tazo a kwanakin ya kai sau uku Shamsu ke kawota ya tafi aiki sai dare yake zuwa ya ɗauketa, Khairy itama tana jin labarin yadda Sameeha ke yini a gidan Hajiya hakan yasa itama koda yaushe tana hanya da ita ake komai, yanzu ne suka san sun samu surukai, saɓanin Nabila da take nuna musu ko in kula bata damu dasu ba balle su saba suyi jiki da juna. Lokacin da Ibrahim zai tafi ne ya ɗauki Sameeha ya kaita gidan Nabila, baa ta wani sake fuska ba sai wani fuska take a dole ga uwargida, sai dai duk yadda tayi zaton ganin amarya tafi ƙarfin tunaninta domin ta ganta babu raini matar fita anguwa ga kyau ga diri dan har ta fita cikar halitta, ganin bata amshe su yadda ya kamata ba basu jima ba suka bar gidan, shi dama Ibrahim ya haɗasu ne dan su saba koda baya nan Sameeha zata iya zuwa mata suyi zumunci, amma ga yadda ta nuna bata yi marhabun da hakan ba shiyasa Sameeha bata ƙara bi ta kanta ba, ta tsaya iya gidan Hajiya.

*
Ranar Juma'a ya kama kwana sha uku da aurensu ranar ne suka shirya zuwa gidan Umma suyi mata yini, dan washe gari Ibrahim zai zo lahadi kuma su wuce Abuja. Atamfa Sameeha ta saka green mai kyau ɗinkin riga da siket, sai ta saka hijab bata ɗaura ɗankwali ba ta ninke ta saka a jaka, a ranar ta fara fita da sabuwar motarta, kafin ta wuce sai da ta biya sashin Hajiya tayi mata sallama kana ta fito ta wuce gidan Ikram ta ɗauketa a mota dan dama haka suka shirya, kuma Ikram bata iya tuƙi ba tukunna sai an koya mata, itama Ikram atamfa tasha pink tayi kyau masha Allah duk kansu sunyi kumari ga hasken hutu daya fara ratsasu, duk da Ikram baƙa ce amma tayi haske kaɗan kuma ta murje sosai, haka suka wuce gidan umma suna hira a tsakaninsu wanda duk rabi na kewar gida ne da suka yi. Dama umma tasan da zuwansu dan haka ta rangaɗa musu waina da miya da kuma lafiyyyen farfesun naman rago wanda yaji kayan haɗi, koda suka isa sun samu ta gama komai su take jira, Zaidu da Anwar sun tafi Masallacin juma'a ita kaɗai suka samu. Suma saida suka gabatar da sallah kafin suka zauna a falo suka kara gaisheta sannan suka shiga hirar yaushe rabo, umma taji daɗi matuƙa da ganin yaranta cikin kyakkyawar kamala, hakan yasa ta ƙara samun natsuwar ruhi da kuma godiya ga Allah daya nuna mata wannan lokacin da kuma ni'imomin daya yi musu, su Zaidu da suka dawo nan chapter ta ƙaru suka shiga hira sosai cike da farin ciki da annashuwa, bayan sun gama ciye ciyensu suka fito tsakar gida kan babban tabarma da suka saba zama suka ci-gaba da hira, a cikin hirar ne Zaidu ya sako zancen yaran Sameeha yana cewa.

Yanzu Sameeha gashi zaki koma Abuja kinga kin ƙara kusa dasu Amrah, da Aminu shi mai mutunci ne da ya baki su su zauna a gunki in sunyi hutun makaranta suje masa.

Taf kaima kasan ba mai yuwuwa ba ne yadda Aminu ya ɗauka da zafi, tun rabuwarsu ƙiri ƙiri ya ki kawo su balle ya iya bar mata su, kawai dai dole zata nima inda suke tana zuwa ganinsu ko ya kawo su suna yi mata yini.

Cewar Ikram, Umma ta ce.

Gaskiya ba zai bada yaran nan ba, nima nafi yarda da su riƙa zuwa gaisheta su tafi dan kar a takurawa Ibrahima ko.

Sameeha ta yi guntun murmushi tana cewa.

Ni Allah ya saka mini dangana akan yaran, in yaso ya kawo su in ma yace bazai bada ba ya riƙe abinsa dole in su girma zasu nima in da nake.

Haka suka ci gaba da hirar, nan umma ta sako zancen bikin Najwa tana cewa.

Bikin Najwa saura wata É—aya da sati guda yau, Sameeha zaki samu damar zuwa kuwa?

Haba Umma dole na zo saboda Inna ba abin yadawa bace, anko ne ma ba muyi ba, zan barwa yaya Zaidu kuÉ—i ya saya mana Anwar ya kai mana wajen telenmu zan yi waya dashi, In an É—inka sai a kawo umma ki aje mana, biki saura kwana biyu zan zo In Sha Allah har sai an gama komai.

Aiko kin kyauta, ke Ikram tunda kina gari duk abinda ya taso in ya kama ki zo zan kiraki ayi komai dake, ina so ku shiga cikin dangi sosai a dama zumunci daku.

Ni umma wlh banda Najwa taci darajar Inna da babu abinda zai kawo ni bikinta.

Me kuma Najwan tayi miki dan nasan da walakin goro a miya, sam bakwa shiri kamar annabi da kafiri.

Cewar Zaidu, Ikram zata yi magana Sameeha ta kwaɓeta.

Amma nace bana son zancen nan Ikram, magana ta wuce miye amfanin taso da ita.

Ikram faÉ—a mana me tayi? dan na kula sam Sameeha bata so ana faÉ—ar laifin Najwa.

Cewar Zaidu, Ikram tsalam ta miƙe daga gefen Sameeha ta tsallaka gefen Umma da yaya Zaidu ta zauna tsakiya dan kar Sameeha ta kai mata hannu, nan ta shiga basu labarin duk abinda ya faru lokacin biki, Umma salati ta riƙa yi tana tafa hannu sosai suka yi mamakin Najwa, Zaidu yayi 'yar dariya yana cewa.
Chapter 63 · 0% Book details