Sashe 68
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ƙare maganar tana jan dogon tsaki, Hauwa ta fashe da kuka dan shine kawai zata yi taji sauƙin baƙin cikin daya turniƙeta, Adama ma kukan ta cigaba da yi Laure kuma tana tausarsu. Duk yadda Hauwa take burin in an kammala fate zata sha sai gashi ta kasa ko da loma ɗaya ne, Adama ma ta kasa cin komai Laure ce ta ɗan tsakura dan ta gusar da yunwa, itama abin ya dameta dan duk abinda ya samu Hauwa tamkar ita ya sama saboda shaƙuwarsu, haka suka yini a ɗakin Laure sun kasa fita har aka kira sallar magrib, zuwa lokacin labarin sakin Adama ya shiga cikin gidan sai gulma ake yi, su Sa'a da salma har ɗaki suka samesu suka jimanta, dan abin bai yi musu daɗi ba ko kaɗan, haka su yaya Alhasan da Kamalu sam basu ji daɗin lamarin ba, Aminu ma daya samu labari lokacin daya zo sosai abin bai yi masa daɗi ba, haka suka taru suka dinga lallashin Hauwa akan tayi haƙuri ta sake ayi biki bayan komai ya lafa zasu bi zancen, in da yuwuwar gyara sai a gyara auren, dole yasa ta saki ɗin duk da na ciki yana ciki.
****
Gidansu Najwa.
Ya cika da mutane ana ta gyaran kayan abincin gobe ɗaurin aure in Allah ya kaimu, itama tanata nata hidimar dan sosai take shirin zuwa gidan miji, Nafisa kuwa ita ce amara ƙirjin biki dan komai ita ta tsara sai sauran ƙawayensu na biki, Binafa sun so zuwa amman saboda kar Sameeha ta gansu yasa suka bari sai bayan biki suje suga ɗaki ita da ƙawarta Hanan. Kowa ka gani yana cikin farin cikin bikin, umma ce takewa Inna maganar kai kayan amarya tace.
Zulai ya batun kayan É—akin Najwa ko an kaine? naga baki yi maganar ba.
Wlh in gaya miki 'yan uwan ango suka sama mana sauƙi, tun saura kwana biyar suka turo da mota akan a kwashe kaya su zasu gyara mata ɗaki, mantawa nayi ban faɗa miki amma tuni aka yi gyaran ɗakinta, kaita ne ya rage.
Amma kuwa sun sama mana sauƙi sun kyauta, da haka ake dangin miji aiko da ko wace mace ta dace, lallai Najwa tayi dace da dangin miji sai dai fatan zaman lafiya ya kauda sharrin shaiɗan a ciki.
Inna ta amsa da amin tare da sauran matan da suke gurin, haka suka cigaba da hirar suna yabon dangin da Najwa zata shiga.
Washe gari.
Da wuri su Sameeha suka shirya suka tafi gidansu Najwa dan basu tsaya jiran umma ta dawo ba balle su zo tare, duk da ba haka Ikram taso ba Sameeha ce ta matsa su tafi da wuri, a motarta suka wuce tare da yara da Anwar. Suna isa É—akin Inna suka fara shiga suka gaisheta tare da Allah ya sanya alkhairi, kafin daga bisani suka fito suka samu su Umma a tsakar gida suka gaishesu sannan suka saka musu hannu wajen gyaran alayyahun miyar tuwon shinkafa, yara kuma suka haÉ—u da sauran yara suka soma wasansu, Anwar kuma ya fita waje saboda shi da girmansa. Najwa koda tagansu É—auke kai tayi zata wuce Sameeha ta ce cikin zolaye.
Najwa Amarya ba magana ne ya shirye shirye, gaskiya me kwalliyar nan ta fito dake da kyau, bari nazo na ɗaukeki hotuna kuma muyi tare kafin mu ɓata namu kwalliyar.
Au Sameeha ashe kun zo ya gida.
Ai sai Ikram da Sameeha suka kalli juna yadda ta iya kiran sunanta ba anty gatsar cike da rashin kunya, Sameeha jiki a sanyaye ta amsa da lafiya kafin ma ta kuma magana Najwa tayi gaba, Ikram cike da takaici tace ƙasa ƙasa.
Ai gashi ta nuna miki ita din mara mutunci ne, meyasa ma kika kula ta, wlh Anty Sameeha na rasa wani irin zuciya ce dake.
Ki rufe mini baki bana son maganar.
Sameeha ta faɗa cikin ɗaure fuska, sai Ikram taja bakinta tayi shuru zuciyarta tana tafarfasa dan burinta ta samu damar da zata nakaɗawa Najwa duka ta yadda nan gaba zata shiga shakkarsu. Wajen ƙarfe sha ɗaya da kwata aka ɗaura auren Najwa a masallacin bakin titi na unguwarsu, wanda ɗumbin mutane suka shaida kuma Aminu da 'yan uwansa sun je dan Alhasan ne ya karɓan masa auren, Zaidu yana daga can gefe yana kallon ikon Allah dan sosai lamarin ya bashi mamaki tare da girgiza lissafinsa, wai Aminu ne ya Auri Najwa, ya rasa yadda zai lissafa lamarin yayi daidai da kwakwalwarsa, haka jikinsa yayi sanyi kalau ya kasa miƙewa ya fito daga masallacin har sai da mutane suka watse kafin ya iya yunƙurawa ya fito, a daidai lokacin su Aminu suna tsaye da wasu abokansa mutum biyu, ido cikin ido suka kalli juna da Zaidu amma ya kasa ce masa komai ya saka takalminsa ya wuce zuwa gidansu Najwa, koda ya ƙaraso ƙofar gidan yaga Anwar sai yace masa yayi sauri ya kira masa Ikram da Sameeha su zo, yace to kana ya shiga gidan ya samu ganin Ikram ya faɗa mata Sameeha kuwa tana can gurin saka tuwo a leda ana kullewa, Ikram bata kirata ba dan tasan halinta ko tace tazo ba zata zo ba, sai ta fito waje ta hango Zaidu fuska a mugun ɗaure, ta ƙarasa tana cewa.
Yaya lafiya naga fuskarka a É—aure, ko ba a faura auren bane?
Ikram ina Sameeha?
Tana cikin gida tana aiki kasanta ko na kirata ba lallai tazo ba.
Ki shiga ki kirata tazo mu tafi gida.
Saboda me? Meya faru yaya?
Hmmm Zaidu yayi ajiyar zuciya yana girgiza kai saboda ɓacin rai, yace cikin takaici.
Kinsan wai Aminu mijin Sameeha shine ya auri Najwa, ko baku ji sanarwa bane.
Mun ji mana ance Muhammad Al'amin, amma ai bamu gane shi bane, kutumelesi Najwa ta iya cin amana ta rasa wanda zata aura sai Aminu.
Ta faɗa cike da ɓacin rai ta juya a fusace tayi cikin gida a guje, tana faɗawa tayi sa'a Najwa tana tsakar gida da kawayenta suna hotuna, Ikram bata yi wata wata ba ta isa gabanta ta sharara mata mari tare shaƙo wuyanta ta maƙureta ta kaita ƙasa ta shiga dukanta kamar Allah ya aikota, ƙarfinsu bazai zo ɗaya ba saboda Ikram Aljanunta ne suka tashi suke hukunci, nan fa gida ya hautsine aka shiga ƙoƙarin kwatar Najwa amma ina Ikram ta hau ruwan cikinta tana dukanta iya ƙarfinta, nan fa aka fita aka kira maza wanda Zaidu yana ganin haka ya nufo gidan da gudu ya shigo, ga Sameeha ta yi kokarin kama hannun Ikram amma ina ƙarfinsu ba ɗaya ba, Ihu kawai Najwa take saki tana aceceta zata kasheta, da kyar Zaidu ya kama Ikram ta baya ya matse hannyenta da jikinta iya ƙarfinsa ya shiga tofa mata addu'a, yayan Najwa Junaid shima ya saka ƙarfi ya taimakawa Zaidu suka ɗaga Ikram daga cikin Najwa, Najwa kuwa marayan kuka ta saki ga bakinta ya fashe yana jini fuska tayi jajir dan wahala, a haka su Zaidu suka fitar da Ikram da kyar suka saka a motarsa ya rufe ta ta waje, ya koma cikin gidan ya samu ana gogewa Najwa fuska ya kalleta cikin jajayen idonsa ya koma da kallonsa gurin Sameeha yace cikin fusata.
Ina umma, je ki kirata mubar gidan nan yanzu.
Yaya meye haka? Dan Allah ka tafi sannan umma.
Bata rufe baki ba ya daga hannu zai kwasa mata mari saboda haushin musun data tsaya yi masa, sai ya riƙe hannunsa tunawa da wani abu da yayi ya kalleta rai ɓace a mugun fusace.
Dan ubanki ki tattaro yaranki kizo mu wuce, Umma Umma kina ina.
Gani nan Zaidu wai lafiya kake abu kamar wanda ya sha kwaya, Ikram ta gama nata kaima zaka É—aura.
Haba Zaidu in rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba, kayi haƙuri ka faɗa mana me ya faru, ina kuma ka kai Ikram.
Cewar Innar Najwa, Zaidu ya danƙara mata wani mummunar kallo yace cikin ɓacin rai.
Dole zaki faÉ—i haka mana tunda burunku ya cika kin aurawa Najwa Aminu mijin Sameeha daya saka, sai yanzu ma kwakwalwata suke haÉ—o mini abubuwa akan 'yarki Najwa mara godiyar Allah rashin kunya da tarbiyya.
Ya faɗa yana zuba guntun murmushi, Umma ce ta matso ta wanke shi da mari akan rashin kunyar da yayi wa Inna, duk da taji maganar Najwa ta auri Aminu ya daki zuciyarta amma haka ta danne, Sameeha kuwa tun sa'ilin daya faɗa ta wuce suf suf ta fice daga gidan, Zaidu ya kalli umma yana son yin magana ta daka masa tsawa akan ya fita tare da nuna masa hanyar fita, bai ce komai ba ya fice ransa a matuƙar ɓace, Inna kuwa mutuwar tsaye tayi tana jin abinda yafi ƙarfin kunnen ta, Umma kuwa ɗakin Inna ta shiga ta ɗauko hijab ta saka bata cewa kowa komai ba ta fito daga gidan, ta samesu a wajen motar Zaidu, tace.
BuÉ—e motar mu wuce anjima zai kazo ka É—auki motar Sameeha.
Ba musu ya buɗe motar umma da Sameeha suka zauna gidan baya suka saka Ikram a tsakiya da taketa kukan baƙin ciki, Anwar dasu Abi suka shiga gaban mota sai Zaidu ya zauna mazaunin driver ya tada mota suka nufi gida.
_Hmmm an zo gurin..._
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
42.