← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 98

Sashe 78

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi Tallahi bazan yafe wannan cin kashin da Aminu yayi mini ba, sai yayi nadamarsa dan sai na saka shi yayi kukan jini.

Ni kam Hauwa da za kiji shawara da kin saki komai kin barwa Allah dan wlh ni na sare da komai saboda babu nasarar da muka samu komai lalacewa yake yi ba biyan buƙata, jiya fa Alhasan kamar zai rufeni da duka saboda masifar da yake ta yi mini wai ai duk bakina ɗaya dake, dana nima kare kaina ya ce inna kuma magana abakin aure na wai ya gaji da halina kuma aure dai zai ƙara ya huta da baƙin cikin dana ke ƙunsa masa, yanzu ma ƙarya nayi masa akan zanje dubiya na shigo nan, ƙila daya san nan zan zo ba zai bari ba, dan sosai ya goyi bayan abinda Aminu yayi miki cewa yayi da zai samu dama shima da sai ya nakaɗa miki duka, saboda duk cikinku ke ce kika fita zakka ya rasa ina kika samo mugun hali.

To yanzu kin zo kina faɗa mini ne ki ƙara mini baƙin ciki ko jajenta abin da ya same ni, idan kin saduda ni ban sadudu ba kuma ki bar mini faɗar dama ban gayyace ki ba, zaki iya barin mini gida bana son damuwa.

Haba Hauwa abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa, ni na baki labari ne domin abin bai yi mini daɗi ba muyi wa juna jaje, kema kinsan muna tare, sai dai kawai na fita daga sabgar Aminu da Sameeha dama duk abinda ya shafesu dan in zauna lafiya, bana son na rasa aurena a karo na biyu kema shawarar da zan baki ki yi hakuri ki saki komai ki ɗauki haka a matsayin rubutaccen ƙaddara, ki kama 'yan uwanki ki zubar da makamanki.

Kutumar kaza kaza 'yan uwan, mutanen da suke son ganin bayana, to ganin bayana mana dan babu wanda yake goyon bayana balle a tsawatarwa Aminu wulaƙancin daya yi mini, sam basa ƙaunata saboda Aminu yana da kuɗi ni kuma fuƙara'u ce, dan haka na san duk yadda zan zauna da ko wani tsinanne ne wlh, banda nasan uwa ɗaya uba ɗaya muke da sai nace ƙila ni tsintoni aka yi aka saka ni a cikinsu. Da wanne zanji da sakin Adama da aka yi akan wannan tsinannen auren ko da wulaƙancin Aminu.

Haƙuri dai za kiyi Hauwa mu karɓi wannan ƙaddarar In Sha Allah Adama zata samu wanda yafi mijinta, muyi kokarin gyara kuskurenmu dan Allah, saboda in ɓera na da sata daddawa na da wari, Alhakin Sameeha ne yake binmu.

Laure tashi ki bar mini gidana tun kafin raina ya ƙara ɓaci na zageki.

Allah ya baki haƙuri yasa ki gane amma wlh ni dai na cire hannu na daga lamarin Aminu babu ruwana.

Tana kaiwa nan ta miƙe ta gyara hijab ta fice daga dakin, Hauwa ta bita da mugun harara, wanda tana fita ta fashe da kukan baƙin ciki, ji tayi duniyar tayi mata zafi ga mari ga tsinka jaka da wanne zata ji.

Aminu tunda ya bar gidan ya wuce gidansa sai da ya ɗauki kusan awa biyu a kwance a ɗakinsa, kiran sallar ya tashe shi ya gabar kana ya koma ya kwanta ko yunwa baya ji. A ranar dai baiyi barcin kirki ba domin kuwa ga yunwa ga kuma damuwa. Da safe da wuri ya shirya ya fita ta siyowa kansa abin kari yaci ya ƙoshi yana shirin sake fita sai gasu yaya Alhasan sun zo shi da Kamalu, da suka zauna suka gaisa kana suka jajanta masa abinda ya faru tare da bashi haƙuri akan ya yafewa Hauwa, Aminu ya nuna musu babu komai kuma komai ya wuce nan ya sanar dasu tafiyarsa London da zaiyi na shekara biyu, ya kuma faɗa musu yana so Baba Hansatu zata dawo nan babban gida ta zauna suna kula da ita kafin Allah yayi masa dawowa, suka yi masa murna da fatan alkhairi tare da tabbatar masa da zasu riƙe Baba a hannunsu, nan ya bar musu amanar gidansa su kula masa da shi har da yawo, ya kuma basu maƙudan kuɗi su raba da kuma kuɗin da zasu yi wa Salma gara in ta haihu, ya kuma sanar dasu hukuncin daya yanke akan yaransa na ya barsu a hannun Sameeha, sun ji daɗin haka kuma sun goyi da bayan duk hukuncin daya yanke, daga bisani suka yi hira sosai kana suka tafi ya rakasu har zuwa babban gida daga can ya wuce Zaria.

A ranar su Junaid suka zo da mota suka kwashe kayan Najwa, dama Aminu ya bar key ɗin gidan a hannun me gadi, tas suka gama kwashe komai suka rufe gidan tare da mayar da key ɗin a hannun me gadi suka wuce. A ɗakin Najwa suka zuba kayan tunda bata nan sai suka rufe ɗakin gabaɗaya, a lokacin ne kiran Saleema ya shigo wayar Baba yaƙi ɗauka.

******

Kano.

Tunda Saleema ta dawo sashinta sai ta shiga ɗakinta ta zauna bakin gado tana cike da damuwa kamar zata fasa kuka dan baƙin ciki, tunawa da tayi da Baban Najwa yasa ta fito ta amsa wayarta a hannun Najwa ta koma ɗaki ta kirashi, koda ya ɗauka ta zayyano masa duk abinda Mijinta ya ce da Najwa ba zata zauna masa a gida ba sai ta ɗaura da cewa.

Dan Allah yaya ka kirashi kayi masa bayanin abinda ya faru nasan in ka saka baki zai bari ta zauna da mu.

Hmmm Saleema kenan, kin ga tun kafin aje ko ina kin fara ganin sakamakon É—aukar Najwa, yarinyar nan amanar zumunci taci shiyasa ba zata ga dai dai tunda har yanzu bata yi nadama ba, dan haka babu abinda zan ce masa bazan hana shi yanke hukunci a gidansa ba, ke da kika ji zaki iya da ita ki san inda zaki kaita.

Haba yaya ya zaka ce haka...

Bata gama magana ba ya kashe wayarsa, Saleema takaici ya cikata da tunanin mafita, tana zaune a wannan yanayin ga yunwa daya dameta sai ga Malam ya shigo sashinta Allah yasa baiga Najwa a falonta ba ya wuce bedroom ɗinta ya sameta ta rafka tagumi, tana ganinsa ta miƙe tsaye a tsorace fuskarsa kamar zata fashe da kuka.

Me kike jira da baki sallameta ba?

Saleema samun kanta tayi da tsuguna masa akan guiwarta ta fashe da kuka tana cewa.

Don Allah kayi haƙuri malam ka duba zumunci ka barta ta zauna, yarinyar Yayanmu ne na Kaduna wacce aka yi bikinta jiya mijinta ya saketa a yau saboda baida lafiyar da zai kusanceta, ya ɓoye mana haka sai da aka yi biki muka sani yau daya sakota dan cewa tayi ba zata zauna da shi, yanzu ma na gama waya da yaya akan ya kiraka ya baka haƙuri yace bazai kira ba ba zai hanaka yanke hukuncin gidanka ba.

Saleema ta samu kanta da shimfiɗa ƙarya akan labarin Najwa, Malam ya sauke ajiyar zuciya yace ta tashi ta zauna gefen gado, Saleema ta miƙe da sauri ta zauna, shima zama yayi kusa da ita yana cewa.

Ni bawai na nuna ba zata zauna bane saboda na muzguna miki ba, kawai ina so na nuna miki ina da muhimmanci a gareki domin ki riƙa sanar dani duk abinda ya zama wajibi na sani, kinga da kin sanar dani komai a waya da babu yadda za ayi nace ba zata zauna ba, dan haka babu damuwa ta zauna damu Allah yasa hakan ya zama mata alkhairi ya zaɓa mata miji nagari, sai dai kinsan ina da sharuɗɗa, ki sanar da ita bana son yawo sannan ta zauna a nan ɓangaren karna ganta a farfajiya, idan ta samu natsuwa zan duba me ya dace da ita ko makaranta ko kuma auren.

Nagode Malam Allah ya saka da alkhairi amma ni nafi son tayi wani auren dan mu bawa maƙiya kunya masu yi mana dariya.

Ba dan Allah kike so tayi auren ba kenan, karma ki saka hakan a ranki ki taya ta da addu'ar mafi alkhairi a gareta. Duk abinda take so ta sanar dake ki faɗa mini Allah ya taya mu riƙo.

Saleema ta amsa da amin kana ta yi masa godiya sai ya tashi ya fita itama ta bi bayansa har sai da yabar sashinta kafin ta dawo cikin falon tana kwalawa Najwa kira, data fito daga É—akin yaranta ta zauna sai Saleema ta sanar da ita amincewar da malam yayi ta zauna a gidan, Najwa taji daÉ—i sosai domin ga dukkan alamu zata shimfiÉ—a duk abinda take so a gidan tunda suma masu kuÉ—i ne ba laifi gida ne me kyau, sai dai data sanar da ita baya son yawo tace ba damuwa amma a ranta tana cewa bata ga wanda zai hanata yin abinda take so ba. A ranar Najwa ta samu barcin da ta jima bata yi ba domin tuni ta watsar da damuwa ta fara tunanin yadda zata kafa sabuwar rayuwa, duk da haushin Aminu dasu Sameeha yana manne a zuciyarta.

Washe gari ne bayan sun karya sai Saleema ta tasa ƙeyar Najwa zuwa ɓangaren malam domin ta gaishe shi, koda suka shiga sun same shi da baƙi maza biyu nan suka gaisa Saleema ta gabatar masa da Najwa yace.

Baƙuwa da fatan zaki zauna damu da zuciya ɗaya, bana son yawo bana son na riƙa ganinki a farfajiya in ba kwakkwaran dalili ba, sannan ban yarda da bin shashin matana ba saboda bana son rikici.
Chapter 78 · 0% Book details