Sashe 2
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amra gyaɗa mata kai take yi tana murmushi dan itama ta na son su koma can. Duk zuwansu a family hau ɗinsu Aminu suke sauka dan babban gidane da akewa laƙabi da gidan Alhaji Ado Meyare. Sai dai Allah yayi masa rasuwa tare da matarsa Amina shekara ɗaya ke tsakanin rasuwarsu, su asalinsu 'yan garin meyare ne daga Alhaji har Umma 'yan can ne aikin gomnati ne ya kawo Abba cikin garin kaduna da yake ɗan boko ne sosai. Yanzu shekara shida kenan da rasuwar Umma Amine, wanda yayi dai dai da shekarun Amrah an haifeta da sati biyu Umma ta rasu sanadin ciwon sugar, sun bar yara biyar. Alhasan shine babba kuma ya manyanta sosai dan yaransa shida ya aurar da mata biyu da babban ɗansa Namiji, saura su uku da suke gabansu duk kamaranta suke yi, matarsa ce Lauratu a nan gidan suke zaune amma a wani part duk nan ta haifi yaranta tun tana amarya take a gidan, shiyasa komai da zai shiga ya fita tana da masaniya, kamar yadda mijinta yake babba itama haka take nuna isarta, sai Kamalu da yake bin Alhasan shima abnan gidan yake zaune da matarsa Sa'adatu, yaransu huɗu ya aurar da babbar 'yarsa sai namiji daya ke karatu a jami'a me bi masa kuma tana kokarin kammala secondary sai autarsu da take da shekara bakwai. Sai Hauwa take bin Kamalu tana da yara biyar ta aurar da biyu mace dana miji saura uku da suke gabanta, ita tana zaune a gidan gadonsu tare da mijinta, gidan yana nan kusa da family hause ɗinsu saboda mijinta bayi da karfi Abbansu ya basu gidan akan su zauna har sai yayi nashi, sai kuma Aminu da yake bi mata shekara goma kenan da aurensu da Sameeha yaransu Adam ɗan shekara Tara sai Amratu da take shekara shida. Sai kuma autarsu Ummu Salma ta kamma digree ɗinta tana koyarwa a secondary wanda a yanzu haka ana shirin yin aurenta da wani Junaid ɗan kasuwa ne.
*
Lokacin da Abban Amra ya dawo bayan yayi wanka yaci abinci yara duk sunyi barci, ita da shi suna zaune a falo ta yi filo da cinyarsa suna kallo, Sameeha ta É—ago kanta tana dubansa.
Abban Amra ashe su Yaya hauwa ce suka je yi mana gyaran gidanmu.
Kamar ya? ni ban san sun je ba, amma naga kin ce su Zaidu zasu je kuma haka na faÉ—awa yaya Alhasan.
Aiko tare taje da yaya Laure su suka cewa su Zaidu su tafi har sun gama gyaran gidan.
Ikon Allah, wannan aikin ai ba nasu bane, da alama sun ƙosa mu koma.
Murmshi tayi mai sauti dan tasan Aminu ba zai faÉ—i wani abu mara daÉ—i akansu ba, dan ba lallai ya hango abinda take hange ba duk da bata yi musu zargin saka musu mugun abu a cikin gidan ba, dan tana yi musu kyakkyawan zato na basa bin malamai, amma munafurci da gulma da mayar da karamar magana a zama babba to sun shahara a wannan fannin, haka ta sauya musu hira da wani zancen, daga bisani suka tashi suka isa bedroom É—insa suka kwanta.
Washe gari.
Da wuri suka gama shiryawa dama tuni sun sayar da kayan dake gidan na katako dama gidan gabaÉ—aya, kayan sakawansu da É—an abin amfani kamar su kayan kitchen duk sun loda a buhuna da komai, tuni mota tazo suka kwashe su suka kama hanyar kaduna ya rage sune da 'yan jakan hannu. Sha biyu a airport tayi musu bayan mintuna aka fara kiransu, nan suka je suka yi duk abinda ya dace kana suka wuce filin jirgi suka shiga, minti goma da shigarsu jirhinsu ya É—aga zuwa garin Kaduna, wanda suke cike da farin ciki mara misaltuwa a dalilin komawarsu kusa da dangi. Bayan sun iso Kaduna suka fito suka tadda motar yaya Alhasan dana yaya Kamalu suna jiransu, cike da murna suka isa garesu suka shiga gaisawa daga bisani Aminu ya shiga motar yaya Alhasan tare da Abi, ita kuma Sameeha ta shiga motar Kamalu ita da Amrah, suka wuce zuwa gidansu dake nan Unguwar dosa 'yan majalisu, yaya Alhadlsan sunata hira da Aminu akan sauyin gurin aikin daya samu, ita dai Sameeha ba um ba um um dan bata wani yi sabo da Yayyinsa maza ba, tana matukar basu girma tamkar iyayen Aminu ne, shiyasa tayi gum har suka isa gidansu wanda ya buga hon mai gadi ya wangale gate, nan ta hango mata cike a gidan suna ta hada hada tamkar ana biki, gabanta ne yayi mugun faÉ—i da tunanin meyasa zasu taru a gidan dan zasu dawo kawai, bayan sun saka sati mai zuwa ne ranar da kowa zai zo suyi walima murnar dawowarsu da tarewa a sabon gida.
Ummu Sultan da Samha ce.
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *ABIN DA CIWO*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 2.
Bayan yaya Kamalu yayi parking sai ga matan dake gidan da yara sun zo sun zagaye motarsu suna faÉ—in oyoyo tare da yin guda, Sameeha dai fitowa tayi tana kallon ikon Allah wanda a yadda suka tsara ba zasu sanar da sauran dangi yau ne dawowarsu ba har sai an kwana biyu kafin za a faÉ—a tare da gayyatar su walima da suka shirya yi, yadda taga suna ta yi mata sannu yasa ta saki fuska tana amsawa, bayan sun shiga cikin falon ne suka ganshi kaca kaca anci abinci da ruwan gora da lemukan gora an zubar wani gurin an zubar da ruwa yayi dama dama falo dai ya fita hayyacinsa, ga cushing da suke sababbi anci abinci akai duk an zubar, cabar mamaki da haushi yasa Aminu bai tsaya a falon ba ya wuce zuwa falonsa ya buÉ—e ya shiga ciki ya zauna a cushing, kana ya cire hular kansa ya tallabo fuskarsa da hannu bibbiyu, sai ga su Yaya Alhasan sun biyo bayansa suna balbale faÉ—a, Sameeha itama ta shigo ciki da yara sannan su Hauwa suka biyo su suka tsaya cirko cirko suna sauraren faÉ—an da Alhasan ya ke yi musu akan yadda suka mayar da gida kamar ana hidimar biki ko suna, har murhu suka dasa a tsakar gida suka yi girki, Yaya Alhasan ya dubesu yana cewa.
Da izinin waye kuka zo gidan nan kuka dasa shagali kamar za a tarbi amarya, wannan ai hauka ne da rashin hankali, fisabilillahi ya dace ace Aminu ya dawo yaga gidansa haka. Ina ce mun tsara sai bayan kwana biyu za a faÉ—awa dangi lokacin walimar da za a yi na dawowarsu.
Yaya mu wlh munyi ne dan suga tsantsar murna da farin cikin dawowarsu da muka yi, ba da wani nufu muka yi haka ba, kuma In Sha Allah yanzu zamu gyara ko ina..
Cewar Hauwa, Kamalu ya daka mata tsawa.
Ai na tabbatar ke ce kika yi shelar sun dawo saboda bakinki ba farsa kamar radion daya samu matsala, rarara haka kike, shiyasa ni inyi sirri da ke Allah ya kyauta, ke kuma wa kika tambaya da kika kwaso jiki kika zo.
Ya kare maganar akan matarsa Sa'a da sai raba ido take dan tabbas su suka shirya abinsu ba tare da mazan sun sani ba, Hauwa itace shugaba sai Laure data karfafa lamarin, Laure ce ta yi magana cikin jin haushi.
Haba daga taya murna sai cibi ya zama ƙari, mu munyi abinmu domin Allah ne da kuma zumunci amma baku yaba ba sai kushewa. Hauwa kun ga ku zo mu tattara mu tafi tunda suma wanda muke damonsu basu ji daɗin ganinmu ba, hmmmm ba shakka Aiziki kashi tun kafin abu yayi nisa an fara nuna mana wariyar launin fata, to Allah ya horewa kowa.
Dama ai ke girman jiki gareki amma da kina da hankali ke ce zaki hana wannan haukar da kuka shirya, amma kika biye su kuka aiwatar da abin takaici.
Cewar Alhasan cikin zafi, ƙanwarsu Salma ce tace cikin fuskar tausayi.
Dan Allah yaya kuyi hakuri yanzu zamu gyaran gidan. Anty Sameeha fatan kun dawo lafiya.
Lafiya lau Alhamdulillah, da fatan mun same ku lafiya, yaya Laure yaya Hauwa anty Sa'a dan Allah ku yi hakuri ni sam banga laifin da kuka yi ba, ku rabu dasu yaya, kuma nayi murnar wannan tarba da kuka yi mana dan soyayya ce ta kawo haka, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.
Dalla rufe mana baki munafurcin banza.
Cewar Hauwa data katseta ta wuce fuuu kamar guguwa, suma sauran suka bi bayanta bayan Laure ta sakar mata wata uwar harara suka fice. Sameeha sauke ajiyar zuciya tayi ta koma ta zauna tana bawa su Yaya hakuri akan subar maganar haka komai ya wuce, ita sam bata ga laifin su ba tunda mai kaunarka shine zai tarbeka da farin cikinsa, duk da a cikin ranta ba haka bane amma dole ta nuna kawaici dan tasan faÉ—an suna yi ne saboda ba zata ji dadin faruwar abinda suka yi ba, Aminu ma nuna musu yayi komai ya wuce, nan suka yi salama da su suka wuce, suna fita Aminu ya rufe kofar falonsa da key dan sam baya son hayaniya ya shige bedroom É—insa ya bar Sameeha da yara a falo itama tana mamakin wannan rashin lissafi da suka aikata mata sai dai ta san da biyu suka yi, kuma taji daÉ—in yadda su Yaya Alhasan suka kwarkwance musu ko banza ba zasu kara yi mata wannan shisshigin ba.
***
Laure da Hauwa.