← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 98

Sashe 67

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cewar umma cikin faɗa, Ikram bata kuma yin magana ba dan Wlh sosai take jin Haushin Najwa akan abinda tayi mata, nan umma tace ta tashi ta sauya kaya ta shiga kitchen ta ɗaura musu abinci, haka ta miƙe ta shiga uwar ɗakan umma ta sauya kayan jikinta ta fito zuwa tsakar gida dan ɗaura girki, su Umma suka cigaba da hira Anwar ya fito dan ya yiwa Ikram jajjage. Da yamma umma ta tafi gidansu Inna su Sameeha kuma suka wuce gidanta ita da Ikram da yaran gabaɗaya a motar zaidu daya kaisu, daga nan Sameeha zata ɗauki tata motar dan suyi amfani da ita gurin biki.

****

Hauwa.

Suna can babban gida ana ta aikin biki ba kama hannun yaro, dan sosai suka yi gayyatar 'yan uwa da abokan arziki saboda su nunawa duniya wannan karan biki nasu ne sai abinda suke so yake faruwa, shiyasa tun biki saura kwana biyar ta koma babban gida da kwana uzuri mai ƙarfi ke kaita gida ta yi ta dawo, tun jiya take zuba ido taga 'yarta Adama tazo dan haka suka yi da ita in biki saura kwana biyu zata zo ta kwana har sai an kammala biki washe gari ta koma, ta kuma kiranta a waya bata ɗagawa hakan yasa ta ce in yamma tayi bata zo ba zata aika ɗanta yaje yaji ko lafiya. Ɓangaren Adama kuwa tun shekaran jiya laraba take yiwa mijinta mitar ya barta Alhamis taje gida bikin kawunta yace shi bai amince saboda ya gaji da yawan fitanta, ta bari ranar bikin Asabar sai taje washegari kuma ta dawo wato kwana ɗaya ya bata, tace ita fa hakan bai yi mata ba nan ya fice ya barta tana surutai. Washe gari haka ta kuma yi masa magana zata tafi yace bai amince ba saboda baƙin ciki har da kuka tayi masa amma ko a jikinsa ya ficewarsa. Yau Juma'a tana ganin ƙila ya barta taje tayi kwana biyu amma sai yace sai fa ranar biki zata je, nan ne Adama ta zage tayi masa rashin mutunci ta inda take shiga bata nan take fita ba, haushi ya rufe mijin nata bai san sadda ya rufeta da duka ba ita kuma ta shiga auna masa zagi tana yi masa Allah ya isa, takaici yasa mijin yace cikin fushi.

Tunda baki san darajata ki je gida na sake ki saki uku, na gaji da halinki kullun cikin ƙunsa mini baƙin ciki kike yi, sannan nasan kina yi mini asiri amma na jure saboda nasan baya tasiri akaina domin duk abinda kike yi kin fallasa shi a kunne na ji, darajar yaranmu naketa dubawa amma tunda lamarinki ya zama haka na gama datse igiyar auren, yara kuma mahaifiyata zata riƙe mini su sai ki tattara ki tafi gidan ubanki kisha shagalin biki da hujja, ko ki yiwa Kawun naki zaman ɗaki tunda kin zama sakakkiya.

Na shiga uku Basiru ni ka saka, dan Allah na tuba ka janye sakin nan wlh ko bikin ba zani ba, wayyo Allah na tono mini asiri dan Allah ka rufa mini.

Hmmm daga baya kenan, kuma saki uku nayi miki ko ke mahaukaciya ce baki tantance saki.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, a cikin fushi kayi dan son Manzon Allah da darajar Umma ka mayar dani ɗakina, saki uku cikin fushi saki ɗaya ne, Basiru nice fa Adamarka karka mance soyayya da ƙauna.

Ina cikin hankali nayi wlh sarai nasan me nake yi, saki uku nayi kuma babu zancen gyara ki tattara ki bar mini gidana tun kafin inyi miki watsi dasu, 'yar iska mara tarbiyya sai yanzu nasan na yiwa kaina zaɓen tumin dare nabi hasken fata.

Yana gama faɗar haka ya fice fuuu kamar guguwa, Adama ihun kuka ta fashe dashi tana ambaton ta shiga uku ta lalace, ga wajen idonta daya kumbura mata da duka har idon ya tara jini, ta miƙe ta zauna gefen gadonta ta shiga tuna rayuwarsu ta baya tasan Basiru yayi haƙuri da ita saboda ta jima tana bashi matsala, duk kuwa da tutiyarta asirin mallaka da tayi masa shiyasa take samun galaba akansa baya yi mata wani hukunci, yau kam tasan kadarinta ya karye ta kashe aurenta da kanta a dalilin auren kawunta Aminu, bata san ya zata yi da wannan ƙunshin baƙin ciki data haɗawa kanta ba, tana kallon wayarta tana ringing amma ta kasa zuwa ta ɗauka wanda tasan bai wuce maman ta ne ke kira, haka ta cigaba da kuka tana tunanin yadda makomar rayuwar zai ƙare in ta koma gidansu zawarci, ta ina zata fara? Yadda tasan halin mamanta sai a hankali tasan dole zasu riƙa kai ruwa rana musamman a gurin abinci, yaranta guda uku ta duba kiri kiri yanzu ba zasu tashi a gabanta ba, na goyen ne ya rarrafo yazo ya dafata ya miƙe yana gwalan gwalan biyun sun tafi makaranta, ɗaukanshi tayi ta goya a baya dan dama ta gama shirya shi kenan suka fara rikici da mijinta, kaico da dana sani ne ya cikata tana cizon yatsa, musamman in ta tuna irin kulawar da mijin ke bata, bata rasa ci da sha ba balle sutura dai dai gwargwado yana sauke hakkinsa na miji akanta, tana kuka ta saka hijab ta ɗauki jakar kayanta data haɗa na cin biki da kuma ƙaramar jakar gayu da takalmi da ta saya sabo na biki ta rataya ta fito ta rufe ɗakin ta ratsa matan gidansu da suke jiran fitowarta suna gulma, suna ganinta suka yi gum sai kallonta suke kamar sun samu madubi, to me ya rage mata da zata ɓoye, sakinta dai aka yi kuma ba kome, hawayen dake zuba bai fasa fita ba haka ta ratsa ta wuce, tana saka ƙafarta a waje yaji yo shewarsu dan dama gidan an haɗa makirai, shiyasa bata shiri dasu sosai saboda saka ido da gulmarsu, baƙin ciki goma da ashirin ga abin faɗa amma ba halin tayar da kwanji, dole ta wuce jiki a sanyaye ta isa titi ta samu abin hawa ya wuce da ita gidansu.

Data isa gida kayanta ta aje ta fito zuwa babban gida lokacin anata ƙoƙarin tafiya masallacin juma'a, tana shiga ta tadda mata da yawa a tsakar gida ana ta hada faten tsaki a ƙatuwar tukunya, ganin basu ganta ba sunata hira yasa ta ratsesu ta nufi can ɓangaren Laure tasan Mamanta tana can, tana isa kuwa ta same su sun baje a tabarma sunata shan rake ana hira, Adama ganin Hauwa yasa ta saki kuka dan sosai kukan yazo ta kasa danne shi, Hauwa ta miƙe da sauri tana faɗin lafiya ina sauran yaran? Mutanen da suke gurin suma tambayar lafiyar suka yi kowa ya baza kunne, Hauwa ta isa gurin adana ta tsaya sai Adamar ta faɗa jikinta tana.

Mama Basiru ya sakeni.

Da sauri Hauwa ta toshe mata baki tana wato ido waje dan tayi matuƙar kaɗuwa da sakin, kuma bai dace mutanen da ke gurin kowa ya ji ba, qi kamar ta tona musu asiri ne maƙiya suyi dariya, sai ta jayeta daga jikinta ta kama hannunta suka wuce ɗakin Laure, matan dake gurin wannan da kallon wannan ana gulma da ido, sunƙi magana saboda tsoron rashin mutuncin Hauwa. Da suka gisha ciki har sai da suka dangana da bedroom ɗin Laure wacce suka samu ta gama shiri zata fito dan wanka tayi, ganin Adama tana kuka ta tsaya turus tana kallonsu har suka ƙaraso ciki, Hauwa cike da tashin hankali tace.

Me kika yi masa ya sakeki, Adama kin tona mini asiri ina cikin tsaka da farin cikin bikin Aminu zaki zo mini da labarin daya hautsina mini hanjin cikina, Allah yasa saki É—aya yayi miki akau kome, dan wlh bazan jure ganinki a bazawara ba a gidana, ai ABIN DA CIWO.

Adama ta ƙara rushewa da sabon kuka ta shiga cewa.

Akan zanzo biki tun jiya ya hana ni, yau nace masa zanzo ya tubure dole sai gobe na koma jibi, shine rikici ya ɓarke a tsakaninmu daga bisani ya rufeni da duka yana zagina nima ina ramawa, shine daga ƙarshe yace ya sakeni saki uku.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, na shiga uku ni Hauwa ina zan saka kaina da wannan ƙunshin baƙin cikin Adama, meyasa zaki biyeshi ki jawo ya sake ki har uku? da kin kirani ko kin ɗauki wayata da naketa kira da zance ki haƙura goben kya zo, yanzu dan ubanki ina kike so zan tsoma zuciyata tayi mini sanyi. Ashe haka saki yake da zafi? ashe ABIN DA CIWO har haka, Laure kinji tashin hankalin da yarinyar nan ta jawo mini ina tsaka da farin ciki.

Sai muryan Hauwa sirƙe tayi baya zata faɗi dan sosai jikinta yayi sanyi taji kamar an cire mata lakka, Laure tayi saurin riƙeta ta zaunar a gefen gado tana cewa.

Dan Allah kibi komai a hankali Hauwa In Sha Allah komai zaiyi dai dai, karki jawowa kanki wani ciwon yanzu maƙiya suyi mana dariya. Ke kuma Adama baki kyauta mana ba meyasa zaki biye shi? ai in Namiji ya kafe akan abu haƙura ake abarshi dan in kika matsa sai naki ran ya ɓaci, gashi nan kin jawo mana abin magana, Allah ya kyauta.
Chapter 67 · 0% Book details