← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 98

Sashe 31

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta miƙa masa farar takardan hannun ta, Zaidu da Ikram suka kalli juna ko wanne zuciyarsa cike da zullumin abinda ke takardan, Zaidu ya sa hannu ya amsa ya buɗe takardan ya soma karantawa, wani irin bugawa zuciyarsa tayi tare da sakin salati yana tasbihi ga Allah, Ikram data ruɗe ta shiga tambayarsa meke faruwa? ganin bai bata amsa ba sai salati yake yasa ta fisge takardan ta soma karantawa, wani irin jiri taji ya kamata wanda yasa dole ta zaune a gefen gadon tana jin tsigar jikinta yana tashi alamun aljanun jikinta sun motsa dan tana da su, kuka ta fashe da shi tana ambaton sunan Allah.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

21.

Sameeha ta kallesu tana jin wani kukan baƙin ciki yana turnuƙota amma haka ta shanye tace cikin dakiya.

Ƙaddarata ce da jarabawa, addu'a zaku taya ni da shi akan Allah yasa naci. Yanzu taimaka mini za kuyi na haɗa kayana na kwashe su kafin ya dawo gidan nan. Ko da yace ya bar mini kayan funitures ɗin ɗakin nan da kuma kayan kitchen da komai na falo, to Amma ni dai ba zan ɗauki komai ba face kayan sakawana da sauran abubuwan da suke muhimmi nawa.

Meya faru Sameeha? ki faÉ—a mini laifin me kika yi masa daga dawowarsa ya sake ki.

Kamani yayi da 'yan mata guda biyu muna masha'a shiyasa ya sakeni.

Wani mugun zabura Zaidu yayi ya ƙara ja da baya yana nunata da yatsa.

Ko duk duniya zasu taru akan wannan maganar wlh bazan taɓa yarda ba, na san wacece ƙanwata ba zata taɓa aikata barna irin wannan ba. Ki faɗa mini gaskiya kafin hannuna ya sauka a jikinki.

Ya ƙare maganar a tsawace kamar zai daketa, a lokacin ne ta fashe da mugun kuka ta fara basu labarin tun dawowarta daga gidan kakansu da komai daya faru, dama zuwan da su Binafa suka yi ranar monday, nan take Ikram ta miƙe ta tsandara uban ƙara sai ta zube a ƙasa Aljanu sun tashi ta fara surutai akan makirci aka ƙulla mata, kuma na kusa da ita ne suka shirya mata haka kuma ba zasu yarsa ba sai sun ɗauki fansa, nan ta zabura ta miƙe zata fita da sauri Zaidu ya kamata ƙam ya kwantar da ita kan gado ya danne mata hannu da ƙafa ya soma tofa mata addu'a, faɗe suke.

Kabarmu mu É—auki mataki, ku barni nayi magana, ku bari na faÉ—a muku waÉ—anda suka aikata wannan aikin.

Amma ina Zaidu yaƙi basu dama ya cigaba da addu'a, har sai da ya samu nasarar korasu kafin ta saki atishawa sai ya saketa ta tashi ta zauna duk jikinta yana yi mata tsami. Zata yi magana Zaidu ya hanata ya mayar da dubansa kan Sameeha.

Kenan bai tsaya yaji daga bakinka ba ya yanke miki hukunci? kuma bai yi bincike ba kawai ya sakeki. Gaskiya Aminu bai kyauta mana ba yaci amanar yardan da muka yi masa.

Ba wannan ne yasa ya sakeni ba.

To akan menene yayi sakin?

Akan tsawon shekara shida baya iya sauke hakkin aurensa akaina, saboda accident ɗin da yayi ya samu matsala wanda yanata niman magani har yau ba a dace ba, to shine ya sakeni akan wannan dalilin, saboda wai adalcin da zai yi mini kenan dan kar na faɗa aikata zina da ɓarna.

Wani irin kallo Zaidu yake jifanta da shi wanda yasa ta sunne kai ƙasa tare da tsoron abinda zai ce.

Dan ubanki kina cikin irin wannan matsalar baki taɓa faɗawa wani ba, ko umma data haifemu ai yaci ace tasan da maganar dan a tayaku niman magani, bansan meyasa kike da mugun zurfin ciki ba Sameeha, to ga abinda shurunki ya jawo miki, dan haka Aminu ba zai taɓa yarda ba amanarsa kike ci ba tunda yana da hujja, haka kurum ki kashe kanki abanza saboda namiji, gashi ai bai tsaya duba halaccin shekara shida da kika yi masa ba ya lafta miki saki uku lokaci guda bai tsaya bincike ba, kuma yasan tarin laifin nasa ne koda kuwa kin aikata haka. Kinga rashin wayonki ko, komai ki mayar dashi ba komai ba sai kace 'yar fari, sai ki tashi mu wuce gida dan wlh koda saki ɗaya yayi miki kin bar aurensa tunda shi bai da mutunci. Wlh yanzu haka rabon wasu yaran ne Allah ya kawo rabuwarku tunda kuwa inda lafiya lau ne da yanzu Amrah tayi ƙanne biyu, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.

Ikram tace Amin wanda itama haushin zurfin cikin Sameeha take ji, haka suka miƙe suka fara haɗa kayanta, Zaidu yace tunda har shine yace ta kwashe kayan gidan, to wlh ba zasu bar masa ba sai sun ɗiba idan ta tashi wani auren tayi amfani dasu, Sameeha dai jinsu take yi duk jikinta a sanyaye itama yanzu take ganin laifinta na ƙin faɗar matsalar Aminu ga su Umma, wata ƙila da an tayasu niman magani, ta tabbatar da ta tafka wauta da kuskure,wanda hakan yanzu ya zame mata izina. Zaidu ya fita daga ɗakin yaje falo ya duba number ɗin wani abokinsa Sani, yana ɗaukan kiran ya tambayeshi ina zai samu motar kwashe kaya babba, Sani ya sanar dashi akwai wani a unguwarsu bari ya kira ya tambaya yaji ko yana gari. A haka suka rabu ya kashe waya ya koma ciki yana cewa.

Ikram idan kin dawo dai dai ki tashi ki fara haɗa kayanta ki zuba su a kwati, ni bari naje naga kitchen ɗin na fara fitar da kaya dan a yau nake so mu kwashe kayan In Sha Allah ba zai dawo ya samu komai ba, dan magana ta ƙare da ba sauran igiya balle a tsammaci jiran ya mayar da ita. Kema Sameeha dauriya zaki yi ki tashi ki kama mata haɗa kayan dan hannu daya baya ɗaukar jinka, dole sai mun yi da jiki zamu kammala komai akan lokaci.

Ikram ta miƙe tana cewa to Sameeha kuwa gyada kai tayi dan zama bai ganta ba tunda saki ya tabbata, Zaidu ya fice zuwa kitchen ya soma haɗa kaya yana sauke su daga kanta dan cewa yayi tas zai kwashe su tunda shi yace ya bar mata. Ba daɗewa sai ga kiran Sani sai ya ɗauka Sanin ke ce masa mutumin yana gari, sai Zaidu yace ya tura masa number ɗinsa suyi magana, Sani yace to sai ya kashe kiran bayan mintuna sai ga number ɗin mutumin ya turo masa, Zaidu ya yi copying number mutumin ya kirashi nan suka yi ciniki akan dubu goma zai kwashe kayan, sai Zaidu yayi masa kwatance yace in ya ƙaraso zai kirashi.

Sun kai kusan ƙarfe ɗaya na rana suna aikin haɗa kaya, dan har mai motan daya zo shima ya saka musu hannu, sannan drivernsu shima ya taya su da mai gadi, nan suka tattara komai suka yiwa mai mota lodin farko sai suka tafi tare da Zaidu suka isa gida, da yake a gidansu akwai wani empty ɗaki da kuma garejin mota da umma ki zuba itace a da data yi yayin sayarwa, nan suka juye kaya tas umma tana tambayar lafiya? Zaidu yace sai in sun dawo tukuna, haka suka bar umma cikin tunani da zullumin meke faruwa tunda ta gane kayan daga gidan Sameeha ne, Haka suka ƙarasa kwashe kayan dakin Sameeha, har kayan store sun kwashe tas basu bar komai ba, dan a takaice sai da mai motan yayi sahu uku kafin Zaidu ya sallame shi, Ya amsa key ɗin motar Sameeha yace su fito su shiga su wuce, a lokacin ne Sameeha ta fashe da sabon kuka tana ƙarewa falonta kallon ƙarshe sai da Ikram ya kama hannunta ta jata kafin suka fice daga falon. Ta tsaya tana kallon mai gadi da driver.

Nagode bisa ɗawainiyar da kuka yi Allah ya saka musu a mizani , ni zan tafi dan zamana ya ƙare a gidan nan yau, Allah ya sada fuskarmu da alkhairi.

Sai ta cigaba da share hawayen dake gangaro mata, suma suka shiga yi mata fatan alkairi tare da yi mata jaje dan sosai lamarin ya taɓasu, basu ji daɗin abinda ya faru ba dan Sameeha tana matuƙar yi musu alkhairi, haka ta shiga mota Zaidu ya jasu suka wuce ko wanne ransa a jagule suka nufi gida, umma kuma tana can cike da damuwa da ƙosawar su dawo su amsa mata tambayoyin da suka cika mata zuciya, dan kwashe kayan Sameeha yayi matuƙar girgizata da tunanin ba lafiya ba, hakan yasa ko abincin rana ta kasa ci.

******

Najwa.

Da tsananin farin ciki ta wayi gari kamar anyi mata babban kyauta, tana zaune a tsakar gida tana son yin wanke wanke data haɗa, dan so take tayi saurin gama aiki ta fita zuwa gidansu Nafeesa ta ɗauketa su je gidansu Binafa, sai ga kira ya shigo wayarta ta miƙe ta isa bambun ruwa data ɗaura wayar akai, ta ɗauka sai taga Jamila ce sai da ta ɗan yamutse fuska kafin ta ɗauki kiran, sai dai kuma ta yanke kiran nan ta tuna bata kira sai dai a kirata, Najwa ta shiga ɗakinta ta zauna a gefen gado kafin ta kira Jamila, tana ɗauka Jamila ta fashe da kuma.

Anty Najwa Alhaji yau da sassafe ya koreni, tun ɗazun nake niman number ki yaƙi shiga zai yanzu.

To ni da kika kirani yanzu me zan yi miki?

KuÉ—ina zaki cikasa mini, sannan ba kince zaki cigaba da aiki dani ba in kin auri Alhaji.

Hahaha ashe ke wawuya ce ban sani ba, kina tsammanin zan yarda dake ne Jamila? Bayan dake aka haÉ—awa 'yar uwata tuggu, na sani nan gaba ki haÉ—a baki da wasu a cuceni, ai sai dai kije ki nima wani aikin amma ba Najwa ba tunda ko auren ma ba a yi ba. Batun kuÉ—inki ki faÉ—a mini inda kike a yanzun nan zan zo na kawo miki sai ki wuce garinku.
Chapter 31 · 0% Book details