← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 98

Sashe 44

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meyasa zaki yanke mini hukunci ko kinji nace miki ina zarginki da wani abu ne? kawai dai ni tsoro kika saka mini dan gaskiya ina tsoron mutane musamman waɗanda nake ganin suna da damar cutar dani, da yawan matan masu kuɗi wasu ɓata gari ne kema kin sani, jiya muka haɗu sai gashi kin zo gidanmu yau kinga dole na cigaba da jin tsoronki, amma jin bayanin yayarki akan nayi miki kama da 'yar uwarku data rasu yasa na ɗan ji na rage shakka a kanki. Amma zan so ki nuna mini hotanta dan hakan ma zai ƙara kore mini shakku.

Khairy bata ce mata komai ba sai duba wayarta data soma yi har sai da ta lalubo hotunan Mubeena wanda ciki har da na ɗaurin aurensu, ta miƙa mata Sameeha ta shiga duba hotunan tabbas suna yanayi da ita amma kuma Sameeha ta fita haske da shekaru, inda taga kamarsu sosai wani hoton Mubeena da tayi dariya wushiryarta ta fito da dimple, wanda yasa Sameeha yin murmushi ta ɗago tana kallon khairy dake kallonta.

Na yarda da tayi maka dani musamman a wannan hoton, sai dai ita ta fini yarinya da kuma duhu.

Shiyasa kika ga na nace miki saboda wlh ina ganinki a shagona na hango kamarki da ita, kinji dalilin daya saka naketa binki kenan, kuma wannan hotunan kusan shekara goma sha da suka wuce.

Allah mai iko munyi kama a fusge, to Allah ya gafarta mata.

Ameen, amma ina ƙanwarki ko itama ba ta nan?

Ni kaÉ—ai ce a gidan, sunje gidan kakanmu nan da bayan sallar la'asar zaki gansu.

Allah sarki to Allah ya dawo dasu lafiya, kiyi hakuri na takuraki, wlh zaman gidan ba daÉ—i ni kaÉ—ai shiyasa nazo dan na rage lokaci, ga babansu baya gari sai jibi zai dawo, yau kuma bama fita kasuwa, shiyasa nace bari kawai nazo gunki muyi hirar dana ce zan baki, sai kuma yaya Amina tazo ta rufeni da faÉ—a a waya.

Ta ƙare maganar tana turmuke fuska, murmushi Sameeha tayi.

Ai gaskiya ta faÉ—a kuma kema kin sani sai dai idonki ya rufe.

Hmmm hakane, bari na baki labarin dalilin da yasa na saka mijina ƙara aure. Wlh tunda muka yi aure na fahimci shi mabuƙaci ne sosai haka na jure har muka baro ƙasar Sudan dana muka shafe shekara biyar a can, da yake ina gama secondary aka yi mini aure kuma muka tafi can, da muka dawo nan kowa yanata surutu na lalace, a haka har na haifi 'yata ta uku to ganin har lokacin ban dawo daidai ba yasa yayata Amina da kuma Aisha suka taso ni a gaba akan na sanar dasu damuwata dan sunga babu wata wahala a gidana sannan ma ga dukiyata ina juyawa, gaskiya ban so faɗa musu ba sai da suka matsa mini na faɗa musu halin da nake ciki, shine fa suka rufeni da faɗa akan zan kashe kaina akan sa tunda ba zan jure masa ba dole in bashi dama ya ƙara aure, in ba haka ba sai ya kasheni tun lokaci na bai yi ba kuma ya samu wata ya aura, maganar har gaban Hajiyarmu taje shine ta rarrashe ni dan taga su faɗa suke ta yi mini. Ni dai jinsu kawai nake amma ban jin zan yarda ya ƙara aure saboda mugun kishinsa da nake,'. To bayan shekara biyu na yaye Khadija sai na samu cikin Humaira kinsan maza suna masifar jin ɗanɗanon mai ciki, hakan yasa Ahmad ya matsa mini da takura, wanda ya jawo mini zubar jini ba ƙaƙƙautawa kamar zan sheƙa lahira, to wlh tunda na dawo hayyacina nace yaje ya nima aure bazan iya ba ko mu rabu. To kinji dalilin ƙara auren dana ce yayi duk da har gobe bawai ya daina matsa mini bane sai dai bana bashi fuska sosai dan gaskiya ina cutuwa, shiyasa kika ganni da ƙibata yanzu, amma da shekara uku baya ne wlh sai kin zata ciwo nake yi.

Ta ƙare maganar cikin 'yar dariya, Sameeha ma dariya tayi tana cewa.

Wannan shine kishiyar dole, wato ba dan wannan matsalar ba ba zaki yarda ta ƙara ba. To Allah ya baku hakurin zama.

Ameen, ai kishiya Sameeha ba tada daɗi wlh sai dan dole in tana cikin ƙaddarar mace, amma da zafi fa kawai dai tawakkali na ɗauka yasa muke zaune lafiya, sannan karin samun kwanciyar hankalina ba gida ɗaya muke ba dan ban yarda ya hadamu ba. Amma ke ai ba kida kishiya ko a gidan baban yaranki.

Ni kaÉ—ai ce matar Aminu kuma ina ganin ni kaÉ—ai ce zan kasance matarsa saboda wani dalili.

Amma meyasa zaki ce haka? bayan kun rabu ai dole zai yi ƙoƙarin yin wani auren.

Abin da ciwo shiyasa bana son tuna komai, amma ni nasan Aminu ba zai iya ƙara wani aure ba.

Zan zo nasan labarinki amma bazan matsa miki ba dan naga har yanzu baki fita daga raÉ—aÉ—in rabuwarku ba.

Bai wuce wata huÉ—u ba, ni yarana ma nake son gani ya ki kawo su.

Ba'a garin nan suke ba?

Nan ne ahalinsa suke, amma yana aiki a Abuja.

Kiyi hakuri In Sha Allah watarana zaki gansu ki bashi lokaci wataƙila shima yana cikin damuwar da kike ciki ne. Allah ya baki juriya yasa kinci jarabawarsa dan wlh mutuwar aure ba ƙaramin ciwo gare shi ba sai a hankali zaki saba. Bari nazo na tafi wannan material ɗin ki ne na jiya dana ce zaki saya to na sayan miki, saura kice baki so tunda dai yanzu mun fahimci juna.

A'a fa hajiya yanzu dai zamu fahinci junan, ba zan karɓa ba haka kurum na karya miki jali.

Na dai yi niyya ba zaki saka naƙi samun ladanki ba wlh, dan narantse bazan tafi dashi ba in kin so ki bayar ko ki ƙona, Ki gaida su umma in sun dawo naso ma na gansu mu gaisa amma zan dawo wataran.

Ta ƙare maganar tana miƙewa Sameeha itama ta miƙe riƙe da ledar kayan, tabi bayan Khairy zuwa bakin gate tana cewa.

Ni dai wlh kin takurani da amsar kayan nan, haba wannan irin hidima, yo irin wannan kirkin naki ai sai mutum yaji tsoronki.

Khairy ta kwashe da dariya.

Ni dai ba mayya bace balle mai yankan kai, na dai gaya miki in baki so ki yar. Sai anjima

Ta wuce ta buɗe motarta data yi parking a daidai ƙofar gate ɗin, Sameeha ta ware dan kwalinta ta yafe ta leƙo kai waje tana yi mata a sauka lafiya da godiya, sai da Khairy ta wuce kafin ta koma cikin gida tana jinjina wannan kirki na Khairy, ta zauna tana juya material ɗin tabbas yayi mata kyau sosai amma zata barwa Ikram ta ɗinki dan ita kam harga Allah ba zata yi amfani da shi tunda ma tana da kaya sosai. Sai bayan sallar la'asar su umma suka dawo sun tadda ta ɗaura tuwo a gawayi miyar kuka kuma a electric, ita da umma suna zaune a bisa wannan tabarmar da suke shan iska a kanta, Ikram ta fito daga ɗakin umna tana cewa.

Anty wannan matrial É—in fa na waye? na ganshi akan kayana.

Na baki ne ki É—inka.

Kai amma anty nagode Allah ya saka da alkhairi.

Ameen, matar jiya ce ta kawo mini, É—azun tazo.

Ba dai matar nan ta kasuwa ba da kuka haÉ—u?

Ikram ta faÉ—a taba waro ido waje cike da mamaki, Sameeha tayi murmushi tana cewa.

Ita fa, zauna dai kisha labari umma ma taji yadda ya wakata tsakani da ita.

Nan fa Ikram ta zauna ta baza kunne umma ma da bata gane zancen su ba tana sauraren me Sameehan zata faɗa, sai ta shiga basu labari tiryan tiryen har da nuna musu hoton Mubeena da khairy ta tura mata, Umma itama taga kamarsu sosai tace haka Allah ke ikonsa, amma tayi mamakin yadda Khairy ta shige mata sosai, tace tabi a hankali duk da haka karta sake mata sosai dan bata son damuwa, Ikram dai tace wlh ɗinkawa zata yi taci bikin ƙawarta da bata samu yin anko ba, haka suna dinga hira gwanin sha'awa.

*****

Aminu.

Tunda suka tafi Ilori yake fama da busy dan in ya fita tun safe sai dare yake dawowa hotel ɗin da suka sauka, da yake Baba Saude tana tare da yaran shiyasa bayi da wata damuwa, ya kama musu falo da ɗaki biyu a ciki da bayi ko wane daki tamkar dai gida. Sai da aka ɗauki sati kafin ya samu kansa ya gama abinda ya kawo shi, sai ya shiga yawo dasu suna zaga wajen shaƙatawa suna ganin yadda tsarin garin yake, duk da dauriya yake yana danne zuciyarsa saboda kewar Sameeha daya dame shi, yaso ace suna tare a wannan tafiyar dan yasan Sameeha tana son tafiya haka musamnan garin da bata sani ba. Damuwarsa yadda yanzu Hauwa ta takura masa da kira akan batun Najwa da ta tura masa numbernta ya kirata, shi kuma sam baya ƙaunar kiranta dan in ya kira bai san me zai ce mata ba tunda ba sonta yake ba, sannan ma ga siraɗin daya ɗaura auren akai na zai yi ne domin ya hukunta Hauwa, sannan damuwarsa akan bai san ya Sameeha zata ji ba in aka ce zaiyi aure, dole zata yi zargin ƙila ya warke ya barta tana ta wahala ko kuma ya munafinceta. Kwana uku kenan da Hauwa tana kiransa yaƙi ɗagawa, dan yasan zencen nata baya wuce magamar auren wanda harta fara damunsa akan ya fara turo da kuɗin kayan siyan lefe, kwatsam sai gashi ta kirashi da wata number, yana ɗauka ta rufeshi da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba, ya bata hakuri yace in ya dawo daga Ilori zai zo kaduna suyi magana, bata kuma magana ba ta kashe wayar alamar bata sauko ba tana fushi da shi, murmushi yayi yana ƙara mamakin ƙarfin halinta. Yana kwance a gado wajen goma na dare ga Abi yana kwance a gefensa yana barci, kira ya shigo wayarsa da number, ya duba da kyau bai san mai number ɗin ba sai ya ɗaga da sallama, Najwa da taji gabanta yana dukan uku uku yasa ta amsa a hankali cikin sanyin murya, ta gaishe shi ya amsa a daƙile da cewa.
Chapter 44 · 0% Book details