Sashe 49
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shi yaro ne a gun babban yayan Hajiyar su Khairy, kuma shi ne yake matakin Wazirin Zazzau bayan rasuwa mahaifinsu, Shamsu yana da yayyi maza da mata dan akwai waɗanda suke 'yan uba amma a ɗakinsu shine auta, ya samu ilimin boko da addini sosai dan a yanzu haka shike riƙe da companyn Ibrahim na fulawa shine manager kuma mai kula da duk wasu harkan kasuwancin Ibrahim, saboda riƙo da addininsa da kuma ƙoƙarin riƙe Amana, a gidansu Khairy yake zaune dan ya zama ɗan gidan. Iyayensa sunata so yayi aure domin yadda yake kama manyan kuɗi, anata bashi 'yan mata a dangi ya zaɓa amma yace shi bare zai aura. Basu takura shi ba hakan yasa ya dage wajen niman ta gari wacce ba zata zama lashe money ba. Watarana yana tare da Usman sun je gidan Khairy to sai suka biyu ta badarawa ranar kasuwar sati hanya ta tushe yayi gosilo, sai ga Najwa ta zo ta wuce sanye da uniform ɗin iskamiyya ta shiga layinsu, da sauri ya cewa Usman ya fito ya amsa motar ya wuce zai zo ya sameshi s gida sai ya bi bayanta, Usman ya zagayo ya shiga ya zauna, har gida yabi Najwa wanda data zo shiga ya yi mata sallama ta juyo tana kallonsa sai ta haɗe fuska tana malam lafiya? Yace lafiya kalau kana ya koro masa bayaninsa ciki har da sunansa, Najwa ta taɓe baki dan daga sunan nasa har shi ba suyi mata ba, sai dai kawai ta amsa masa ne ta samu na kati dan bata hango ma yana da kuɗin da take burin samu a jikinsa ba. Ta bashi number ya amsa suka yi sallama, tun daga lokaci Najwa ke garashi bata tashi nimansa sai tana buƙatar abu shi kuwa cikin rawar jiki yake yi mata, bata taɓa tambayarsa abu yaƙi yi mata ba, ganin yadda ta mayar dashi saniyar tatsa yasa ya fara shakku akanta a yadda naga shigarta da kuma ƙoƙarinta na niman ilimin addini sunyi hannunvriga da halayyarta dan sosai ya gane ba sonsa take ba sai abun hannunsa, daga karshe ma ta sallamashi, da ace shi mutum ne mara yafiya da sai ya yi amfani da ƙarfin dukiya ya rama duk abinda tayi masa sai yayi haƙuri ya kyaleta, sannan ya kikayi niman wata budurwa dan ya ce zai fara nima a cikin dangi ko zai dace. Cikin ikon Allah sai ga shi yana ganin Ikram yaji ta kwanta masa a rai harma yake hango yanayin kamarta da Najwa haske kawai Najwan ta fita amma tabbas akwai kama ta jini.
Haka ya cigaba da binsu, Ikram tana hankalce da shi data ga abin nasa da gaske ne yasa tace.
Anty wancen motar ta bayanmu mu take bi fa.
Kamar ya fa.?
Sameeha tace tana kallonta tare da mayar da kallonta gurin mota.
Allah kuwa mu yake bi wannan saurayin ne da Anty Khairy tace ya kaimu, da alama so yake ya ga gidanmu kuma ni wlh ina son Aliyu bazan yarda na bashi fuska ba.
Aliyun da yake ta yi miki yawo da hankali, kinga Ikram ki shiga natsuwar ki kisan me kike ciki wlh, shekarunki fa ashirin da shida ina kamarki na shekara kusan takwas da aure, dan yanzu shekara ta ashirin da tara ina shekara sha takwas aka yi mini aure, dan haka ki buɗe idonki ki bashi dama ba kisan inda ƙaddara zata kai ki ba.
Hmmm Ikram tace tana turo baki dan ita sam bata wani gamsu ba saboda Aliyun dai take so, Sameeha ta cigaba da cewa.
Na dai gaya miki ki bashi dama kuma wlh zan faÉ—awa umma da yaya Zaidu wannan jiran da kike yi masa yayi yawa, tun yana makaranta fa daya gama yayi service yanzu kuma wai yana short service NDA, ai yaci ace ya turo manyansa an fara magana kafin ya fito a saka rana. Karki mamakin yana fitowa ya sauya miki ko yace anyi masa mata a danginsu, dan wlh da yawan mutane haka suke yi saboda kar aci arziki da bare sai dai masu su ci.
Jikin Ikram yayi sanyi dan wlh ta fara sarewa itama da Aliyu sabods ko waya yi sai time É—in da aka basu saboda gidan soja doka garesu, kuma tana ta yi masa maganar ya turo yace sai in ya fito, maganar dai tuntuni suke yinta amma ba sauyi, ta sauke ajiyar zuciya.
To shikenan zan bashi dama amma saiku taya ni da addu'a Allah yasa na soshi dan wlh Aliyu ne a zuciyata.
Allah ya zaɓa miki na gari.
Sameeha ta faɗa Ikram tace Amin sai suka sauya hira zuwa irin tarban da suka samu a gidansu Khairy, har suka ƙarasa gida Sameeha tayi hon Anwar yazo ya buɗe musu gate Ikram ta fito Sameeha ta shiga da mota gida. Ikram motar Shamsu ta nufa yana ganinta ya sauko ya rufe motar har ta ƙaraso ta rungume hannunta tana cewa.
Sannu da ƙoƙari, lafiya kake ta binmu.?
Saboda inga gidan ku ba sai na sha wahalar sani ba. Ki shiga gida In Sha Allah gobe zan dawo muyi magana Allah ya huta gajiyarku.
Ta amsa da amin kana tayi masa saida safe ta wuce cikin gida shi kuma ya shiga mota ya juya ya hau titi ya wuce. Tun ɗazu Ibrahim ke kiransa bai ɗaga ba dan kar su Ikram su ɓace masa sai yanzu ne ya samu damar kira yana riƙe da waya hannu daya yana tuki, da Ibrahim ya ɗaga yace cikin faɗa.
Ina ka aje waya ina ta kira, duk inda kake ka dawo yanzu ka sameni a Part ɗin baƙi ina jiranka.
To yace masa cike da girmamawa kana ya kashe wayar ya mayar da hankalinsa kan tuƙi.
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
31.
Shamsu yana isa gidan ya wuce part ɗin da Ibrahim yake ya same shi zaune shi kaɗai a falo, ga security a waje suna aikinsu na tsaro, ya zauna a can carpet dan su tarbiyyarsu indai babba yana kujera to su a ƙasa zasu zauna, ya ce cikin natsuwa.
Yaya gani.
Yauwa, ya labarin company da fatan ba wata matsala.
Alhamdulillah komai yana tafiya yadda ya kamata.
To madalla, akwai wani kwangila da zan baka wanda in kayi mini aikin daya dace zan baka motar daka ce kana so in siya maka.
Cikin zumuÉ—i Shamsu ya gyara zama yana cewa.
In Sha Allah zan yi maka aiki mai kyau ka faɗa kawai yanzu na fara shi ba ɓata lokaci.
Good ina wannan ƙawar Khairy wacce ta zo tare da ƙanwarta suka tafi ash color mota.
Eh na ganeta dan har gidansu na sani.
Ya aka yi kasan gidansh?
Ɗazu na bisu a baya saboda ina son daidaitawa da ƙanwarta.
Ya ƙare maganar yana sosa kai, murmushi Ibrahim yayi ganin sunyi haɗaka akan abu guda, ya yi gyaran murya yace.
Ina so ka yi mini bincike akan me ya kashewa yayar aure da duk wani bayani akansu, wato bincike mai kyau nake so da gamsasshiyar amsa. Ina so ya zama sirri a tsakaninmu ban yarda ka faɗawa kowa ba, nan da sati ɗaya zuwa biyu nake buƙatar sakamako. Idan kayi aiki me kyau to zaka je gurin Isyaku ka zaɓi matar data yi maka kuma idan aurenka ya tabbata zan yi maka lefe da komai.
Cikin tsantsar farin ciki ya ce zai yi masa duk abinda yace, kana Ibrahim ya cigaba da cewa.
Aikinka ya fara daga yau kar ka sake kaje gurin Khairy niman satar amsa dan bana so kowa ya sani.
To In Sha Allah zanyi yadda kake so, ka fito lafiya.
Ya faɗa kana ya miƙe ya fito yana mamakin Ibrahim, mutumin da yaƙi yarda ya ƙara aure shine zai ɓige a bazawara, abin ya ɗaure masa kai duk da yasan so ba ruwansa a duk inda ya ga dama sauka yake. Ya wuce part ɗin Hajiya ya samawa kansa abinci yana jin wani farin ciki a zuciyarta tare da tunanin fatansa ya tabbata shi ya auri Ikram Ibrahim ya auri Sameeha, ranar ba ƙaramin shagali za a yi a kaduna ba kuwa.
*****
Aminu.