Sashe 32
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu abinda zaki ce dani kenan Anty? bayan nayi miki aiki domin cikar burinki.
To ai biyanki nayi ko kuma Hauwa ce ta saka ayi aikin ba ni ba. Zaki faÉ—a mini inda kike ko sai na kashe wayata kiji a salansa.
Najwa ta faɗa a ɗan tsawace, jikin Jamila da yayi sanyi da mamakin Najwa, sai ta faɗa mata inda take sai Najwa tace ta jirata a gun gata nan zuwa sai ta kashe waya, Jamila da mamaki yasa ƙafarta ta kasa ɗaukarta sai ta nima guri ta zauna tana jin ciwon abinda Najwa tace mata, wato kenan taci moriyar ganga ta yada korenta, haka ta rafka tagumi duk abin duniya ya isheta.
Najwa kuwa aje wayar tayi ta fita ta fara wanke wanke dan ba zata fita yanzu ba dole sai tayi aikin gida da ta saba yi dan kar inna ta fara yi mata mita da faɗa, sai da ta gama aikinta tsaf ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ta zuba hijab har ƙasa ta nima nikaf ta ɗaurawa fuskarta ta saka safa, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama komai ta fito zuwa ɗakin inna ta ɗage labule tana cewa.
Inna na wuce makarantar sai in na dawo.
Najwa ba kince yau ba makaranta ba saboda musabakar da kuka fara, sai monday in an cigaba da yi.
Inna kirana aka yi akan ana nimanmu a makarantar shiyasa zanje.
To a dawo lafiya amma karki daÉ—e dan nima zan fita zuwa anjima.
To tace mata kana ta saki labulen ta fita, sai da tayi tafiya mai ɗan nisa a ƙafa ta iske wasu 'yan shaye shaye dake a can sama layinsu, sai ta tsaya a gabansu tana cewa.
Yane Lawali, ina so ka haÉ—ani da yaranka guda uku zasu yi mini wani aiki yanzu.
Najwan Inna ke ce kika wani ɓoye a cikin niƙabi, wani aiki za ayi miki? ai ko mi zai naje da kaina kin san ke tamu ce ta mutunci, tunda kina bani hamsin ɗari ina kashe yunwar cikina ba wani eh yane.
Dariya Najwa tayi tace.
To kwata kwata sau nawa na taɓa baka kuɗi? bai wuce sau biyu ba.
To ai ni zuciyata bata mance alheri kuma duk mai bani ina yi dashi.
Hakane to mu je in ka shirya sai ka É—iba yara biyu, akwai wata yarinya da nake so ku bata tsoro ta yadda ba zata sake marmarin zuwa Kaduna ba.
Angama ranki ya daÉ—e, amma fa zaki bamu na makari dan yasin yunwa nake ji banci komai ba tun safe.
In dai wannan ne karka damu ina da nauyi.
Ta faɗa tana yin gaba, sai Lawali ya nuna mutum biyu daga cikin waɗanda suke tare yace su tafi, sai ya yiwa sauran sallama akan sai sun dawo. Haka Najwa tayi gaba suna binta a baya kamar dai ba tare suke ba, Napep ta tare musu da suka iso titi ta zauna a gaba gefen mai Napap su kuma jeru su uku a baya sai suka wuce. Dai dai inda Jamila ta faɗa mata suka sauka sai tace mai napep ya jirasu tana zuwa sai ta juya tana dube dube, can ta hango Jamila tana zaune jikin wani gida, ta yi gaba su Lawali suna binta har suka isa gaban Jamila suka tsaya, Najwa ta ɗaga niƙaf, Jamila da sauri ta miƙe dan sai a lokacin ta gane ta.
Anty Najwa ashe ke ce, tun É—azu nake zuba idon ganinki.
Eh wani uzuri ya riƙeni, muga wayarki.
Najwa tace tana miƙa mata hannu, Jamila da bata kawo komai ba ta miƙawa Najwa wayar ta amsa ta buɗe bayan wayar ta ciro sim ɗinta, sai ta balla shi gida biyu ta jefar a kwata, kana ta goge duka number ɗin da yayi saving akan wayar kuma ta goge dialing call, Jamila data gama shan gubar mamaki sai ta buɗe baki tana kallonta ta nisa tace.
Ya zaki karya mini sim? hakan me yake nufi?
Saboda bana so ki ƙara yin waya da duk wanda kika san ya sanni. Sannan ma ina so ki sani yanzun nan zaki bar garin nan in ba haka ba zan saka a ɓatar dake saboda asirinmu ya rufu. Lawali ina so ku gargaɗeta akan karta sake zuwa garin nan, in ba haka ba kuka ganta kasheta zaku yi har lahira.
Nan fa cikin Jamila ya É—uru ruwa ta soma cewa cikin tashi hankali.
Anty Najwa ya zaki yi mini haka, ban taɓa zaton haka daga gareki ba, ni ki bani cikon kuɗina in tafi ba sai kin saka sun tsorata ni ba.
KuÉ—inki ai kin gama amsa, dan dubu goman nan shine rabonki.
Wlh baki isa ba ai ba haka muka yi dake ba, haka kurum kin saka nayi miki aiki kin sakani a shiga uku gashi an koreni, kin samu biyan buƙata an saki matar gidan, ai bai dace ki saka mini da butulci ba kuma Wlh...
Bata ƙarasa maganarta ba taji saukar mari Lawali ya yi mata, kafin tayi aune sun rufeta da duka suna cewa ta isa ta ɗaga muryanta akan Najwa, sai da suka yi mata lilis tana ihu gashi babu masu ceto, dan unguwar shuru ba kowa sai tsilli tsillin mutane ke wucewa, Najwa ne ta dakatar dasu tana cewa.
Lawali dukan ya isa haka, ina so ku saka mini ita a wancen napep É—in ku rakata tashar mota ta shiga motar garinsu, kar ku baro gurin har sai motarsu ta bar tasha. Nawa zan biyaku.
Haba ai ke ta gida ne ki bada ko nawa ne Hajjaju Najwa.
Najwa ta saki murmushi ta buÉ—e jakarta ta dauko kuÉ—i ta basu dubu uku uku, sai ta basu dubu biyu su sallami mai napep, haka suka amsa suna godiya tare da washe baki dan rabonsu da su samu kuÉ—i irin haka sun mance, Jamila sai kuka take tsabar sun tsoratata ta kasa magana balle ta jerewa Najwa Allah ya isa da take ta yi a zuciyarta, Najwa ta kalleta tana murmushi.
Duk randa naji labari kin zo garin nan saina saka an kashe ki, kin san dai zan iya saboda ni fuska biyu ce kuma ga shi kinga É—ayan fuskar da baki sani ba, nice nan Najwa ga sani ga Shagala ina iya komai akan duk abinda zai shiga hanyata ya hana mini farin ciki, dan haka ki shiga hankalinki.
Tana gama faɗar haka ta mayar da niƙaf ɗinta ta wuce abinta, su kuma Lawali suka tasa ƙeyarta suka sakata a napep dan a tsakiyarsu ta zauna a baya, ɗayan ya zauna a gaba suka wuce tasha zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta dan baƙin ciki, Najwa ta tsayar da ita gubar mamaki tayi mata lumbu lumbu ɗaukar mara sani, ashe ita kara da kiyashi ne, yanzu ta tabbatar da ta aikatawa kanta babban kuskure wanda ya sauketa a tashar dana sani, ga koshi ga kwanar yunwa, abubuwan data aikatawa Sameeha ne kawai ke yawo a zuciyarta gashi tun ba aje ko ina ba ta soma ganin sakamako, Allah baya barci kuma Alhaki kuikuiyo ne, ga mari ga tsinka jaka, sannan ga babu albashin watan ga babu cikon kuɗinta ga kuma kari da duka, ga kuma alhakin Sameeha data ɗauka duk ita kaɗai, da ace zata samu dama tabbas da kafin ta bar garin nan sai ta towana Najwa da Hauwa asiri ko wanne zakararsa tayi cara kwaɓarsu tayi ruwa, ta fasa kwan da duk zai bure kowa da wari tunda abin na cin amana ne da yaudara. Haka ta dinga saƙe saƙe har suka isa tasha suka sakata a motar garinsu Lere, basu bar tashar ba sai da motarsu ta tafi, Jamila ɗimbin dana zani da cizon yasha ya gama kashe zuciyarta, sai matsar kwalla take yi cike da tarin baƙin cikin abinda Najwa ta aikata mata.
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
22.
Najwa tana isa gidansu Nafeesa sai ta samu Binafa a gidan a she nan taje ta kwana saboda jiya dare yayi kuma bata son faɗan yayanta Bello shiyasa ta nufi gidansu Nafeesa dan ta saba yin haka, da farin ciki Najwa ta ƙarasa gefen gadon dakin ta zauna tana dariya.
Gaskiya nayi farin cikin ganin ki Binafa anan, dama na zo ne domin naja Nafisa mu je gidanku.
Ai a nan na kwana ma ban je gida ba. Ya kin samu labarin an saki Sameeha.?
Cewar Binafa tana dafa kafaɗar Najwa cike da son jin ƙarin bayani.
Jamila ta faÉ—a mini ya saketa amma har yanzu ban ji labari daga family ba tunda da ace inna taji zata faÉ—a mini.
To yanzu meye abu na gaba tunda burinki ya cika Sameeha ta fita.
Cewar Nafeesa cike da farin ciki itama a fuskarta, Najwa taja fasali kana ta miƙe tayi tafiya taku biyu ta ƙara juyowa ta tako ta tsaya tana riƙe kugu.
Yanzu auren Aminu ne kawai ya rage mini inga ina kan matsayin Sameeha wannan shine cikar burina, mun riga mun takaitawa Hauwa hanya yanzu itace zata ƙarasa sauran aiki.
Da kyau ta wajena mata a gidan Aminu ko ba fosta, kuma ko anki ko anso kin zama ne.
Cewar Binafa ta ƙare maganar tana rafka guda.
Ai babu abinda zance miki sai Allah ya saka miki da alkhairi ya biya miki duk kan buƙatunki. In Sha Allah idan na auri Amimu kuɗi suka zo hannuna sai nayi muku kyautar bazata, dan wannan aikin da kuka yi mini dole ne na biyaku da abu mai tsoka, yadda ba zaku manta dani ba kamar yadda nima bazan manta daku ba bisa wannan gagarumin aiki da kuka yi mini.
Kar ki wani ji kin damu fatana ki shiga gidan ki samu kansa, idan kin samu natsuwa a lokacin sai ki sallame mu.