← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 98

Sashe 21

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Adama ta faɗa tana duban Mamanta, Najwa da ta ke cikin ɗakin Hauwa data idar da sallah ta miƙe da nufi fitowa falon ta tsinkayi maganar Adama, sai ta ja tunga ta tsaya taji me hauwan zata ce, saboda dama yawan zuwa gidan da take yi tana so taji a ina aka kwana, dan wata biyu kenan taga komai ya lafa babu wani rikici, gashi kuma ta daina zuwa gidan Sameeha tun lokacin data ce ba zata auri Zaidu ba, da kunya ma taje gidan tunda tasan bata shuka abin arziki ba shiyasa ta maƙale a jikin Hauwa, kamar yadda Nafeesa take bata shawara akan ta dage da zuwa gidan dan ta riƙa sanin meke faruwa, sai dai duk zuwan da take yi ba wani labari dan Hauwa sosai ta sake mata suke abin arziki, ban da 'yan siyayya da take wa Hauwa ta kawo mata tare da zagewa tayi mata aikin gida, wannan yasa Najwa ta ƙara shiga zuciyar Hauwa take jin dole ma tayi yadda zata yi ta auri Aminu dan tasan ta dalilin Najwa zata samu abubuwa sosai jikin ɗan uwanta, kuma zata yi mata biyayya sai abinda suke so zai wakana a gidan. Najwa ta maƙale kunenta sosai a jikin ƙofa tana jin Hauwa na cewa.

Adama ban faɗawa kowa bane amma naje gurin malam mai allon ƙarfe fa, shi ne yayi mini aikin da Aminu bai ɗauke Sameeha daga garin nan ba, babban damuwata da kuma abinda ya kashe mini guiwata malam yace Aminu ba zai taɓa ƙafa aure ba har sai in ya saki Sameeha, dalilin da yasa kenan guiwata tayi sanyi amma na bari sai mun gama bikin Salma kafin zan fara shiri akanta dan wlh ban haƙura ba, Sameeha dole sai ta bar gidan nan ta bawa Najwa ta shiga dan yarinya itace daidai da Aminu tana yi mini biyayya tamkar ni na haife ta, na gama magana da ita tace zata aure shi amma ba zata iya kishi da Saneeha ba dan hakan da kunya, to kinga itama ba zata yarda ayi auren ba sai in Sameeha bata gidan.

Mama amma hakan naga da kamar wuya gurguwa da auren nesa, yadda kawu Aminu ke son matarsa bana jin akwai abinda zai rabasu.

Kisha kuruminki zasu rabu cikin sauki In Sha Allah, yanzu tashi za kiyi ki tafi gurin Laure ki amso ankonku mu zo mu kai É—inki da wuri kan biki ya zo tunda saura sati huÉ—u. Kuma wannan maganar da muka yi kar inji kinyi magana da wani.

To tace mata ta miƙe ta fita zuwa babban gida, Najwa kuwa komawa tayi ta zauna a gefen gadon Hauwa tana jin damuwa a ranta, dan sosai maganar ta tsaya mata a zuciya akan ba zata samu auren Aminu ba sai in ya saki Sameeha, wanda abu ne mai kamar wuya gurguwa da auren nesa, kuma a kullun sonsa ƙaruwa yake yi ta gama kwaɗaitawa zuciyarsa aurensa domin a kullun kallon kanta take yi a matsayin Sameeha, jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin sai dai ta danne damuwarta dan kar Hauwa ta gane, ta zauna a cushing Hauwa tana cewa.

Har kin fito?

Eh, bari na wuce dama nace bari mu gaisa ne amma kasuwar sati zani na yi siyayya.

Aiko na gode Najwa Allah yayi miki Albarka, ya cika mini burina naga kin auri É—an uwana.

Murmushi Najwa tayi tana sunne kai ƙasa ba tare da ta amsa ba cike dajin kunya, sai ta miƙe tayi mata sallama ta wuce Hauwa tana shi mata da albarka tare da binta da kallo har ta fita cike da jinta a zuciyata, sosai take burgeta da natsuwarta da kunya da tarbiyyanta da yake ƙara sakawa ta samu gurbin a cikin ranta.

Najwa tana fita ta kira Nafeesa a waya ta tambaye ta tana ina? Nafeesa tace tana unguwar rimi gidansu cousin É—inta Binafa, Najwa tace tayi mata kwatance dan ba zata iya jira ba dole tazo su haÉ—u akwai magana mai muhimmanci da zasu tattauna, Nafeesa ta faÉ—a mata sunan layi kana tace in tazo ta kirata zata fito ta É—auke ta, a haka suka rabu Najwa ta tari napep ta sanar dashi unguwar da zai kai yace dubu É—aya, bata wani damu ba ta hau dan kuwa abinda ke gabanta ya wuce tsayawa tayi latsin kuÉ—in napep É—in, tunda ma tanada yan kuÉ—inta, saboda bata wasa gurin wanke samarinta da suka nace suna son aurenta.

Koda ta isa sai ta kira Nafeesa ba jimawa ta fito tare da wata 'yar budurwa da bata wuce sa'anninsu ba, Najwa ta hango su sai ta soma tafiya har ta isa suka haÉ—u suka juya cikin gida, Binafa da ta ga Kyawun Najwa ta haÉ—iye miyau ta kasa shuru tace.

Beb ina kika samo mai kyau haka?

Dan ubanki wannan sai dai ki ganta ki kyale dan ba 'yar hannu bace ki mai da baƙin miyau dan tafi karfinki.

Ta bata amsa cikin gatsali, Najwa dai tana jinsu dan bata gane ina zancen su ya dosa ba, sai da suka shiga cikin gidan Najwa ta gane cewar Nafeesa fa danginsu masu kuɗi ne dan gidan har yafi nasu Nafeesa kyau, gashi gidan sama ne hawa ɗaya kato, sai dai koda suka shiga ta ƙara raina kanta amma duk tsaruwar falon bai kai kyan na Sameeha ba, ita kam har yau bata ga gidan daya kai na Sameeha tsaruwa ba, sama suka haura zuwa ɗakin Binafa suka shiga ciki tare da sakawa ɗakin key dan kar azo a katse musu hirarsu, Nafeesa taja hannun Najwa suka zauna a kan gado tana cewa.

Kawata meke faruwa ne na ganki duk a cikin damuwa.

Najwa ta ja fasali ta soma bata labarin duk abinda taji Hauwa na faɗawa 'yarta, ta ƙara da cewa.

Kenan ni sai dai nayi ta dakon sonsa amma bazan same shi ba, duk daular da nake hangen kaina a ciki ya tabbata mafarki, Nafeesa yaushe burina zai cika ko haka dai zan ƙare da auren talaka.

Ta ƙare maganar idonta yana cika da kwalla, Binafa ta saki shewa tana tafa hannu tana cewa.

Yanzu ke akan namiji kike niman asarar hawayenki, wai ko wannan waye haka daya firgita tunaninki? wacece kuma take niman hanashi samunsa? Ku fayyace mini labari yanzun nan ku samu mafita.

Nafeesa ta soma bata labari a takaice Binafa tace.

Kice mini auren cin amana zaki kiyi, sannu da kokari Najwa da kike niman raba mata da mijinta, amma kuma karfin halinki ya burgeni haka nake son mace ta jajircewa akan duk abinda take so, kin ganni wlh duk yarinyar dana kyalla ido na ganta naji ta yi mini har naji sha'awarta tofa sai na lashi zumarta, danni zan iya komai domin cikar muradina.

Ai ke dabance Binafa tunda ke mata kike bi ba maza ba, Allah dai ya shiryeki ya rabaki da wannan mugun halin.

Hakan yafi mini wlh akan namiji ya saka mini ciwon zuciya, kema kinsan bana son wargi. Dan dai kinki yarda ki shigo cikinmu ne amma da kin gane namiji abin banza ne.

Najwa ta kalli Nafeesa ta koma ta kalli Binafa sai yanzu ne hankalinta ya tattara maganarsu ta gane cewar Binafa 'yar lesbian ce, zata buÉ—e baki tayi magana Binafa ta rigata.

Karki damu dani yan mata ni babu abinda zan miki tunda banji sha'awarki ba, amma kuma ni zan baki mafitar da zaki samu Aminu. Ku bani balarin ya tsarin gidan yake da ita kanta matar gidan.

Najwa jin zata samu mafita yasa ta shiga bata labarin Sameeha da komai data sani, Binafa tace.

Ai yazo gidan sauƙi tunda ba mai zama bane Aminun, dan haka ni da ƙawata Hanan zamu je mu farmaketa, tunda mace da mijinta ba a rabata da sha'awa, gashi Aminu ba mazauni ba kullun sai dai ta yi ta fama da ciwon mara, ga wannan maganin ki san yadda zaki bayar a saka mata a cikin abinci ko abin sha yana mugun tada sha'awa. Sauran aiki ki bar shi a hannuna, amma fa sai kun tabbatar mini da yaushe mijin zai dawo kafin komai zai wakana.

Kina nufin zaku je gidan kuyi kwartanci da ita ko me?

Kusan hakan ne amma sai mun tabbatar da mijin zai dawo ya ganmu dumu dumu kamar yadda dai miji ke maka kwarto a gidansa, wannan karan abin ya sauya salo mata zai kama da matarsa.

Wow wow wow amma wannan abin yayi sai dai ina tunanin anya zai yi aiki kuwa? namiji yafi jin kishin matarsa sosai in ya ganta da namiji.

Cewar Nafeesa, Binafa ta saki murmushi.

To yanzu mata sun karɓe kambun, in mace tana da aure basu cika yarda subi maza ba sai ɗai ɗai ke haka, amma da yawa sun bi bin mata 'yan uwansu, dan haka wnnan zai yi aiki fiye da lissafinku. Wannan maganin taya zai isa gidanta?

Binafa ta faÉ—a tana daga musu kwalin maganin, Najwa ta saki murmushi tana cewa.

Ina da wacce zata yi mini wannan aiki, saboda ina shiri da mai aikinta sosai dan haka bani kawai nasan yadda komai zai tafi cikin tsari, kuma itace zata riƙa bamu update ɗin dawowarsa, dan nasan zata yi mini komai musamman ma in na bata kuɗi.

To aiki ya kammalu sai ranar ƙaddamarwa. Ki fara ƙirga ranar fitar Sameeha daga gidanki.
Chapter 21 · 0% Book details