← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 98

Sashe 53

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda aka sanar dashi an gama komai na aurensu an saka rana sai yaji hankalinsa ya kwanta, dan sosai ya kamu da son Sameeha da ko magana basu taɓa yiba a tsakaninsu, hakan yasa shi kiran Khairy yace ta tura masa Number ɗin Sameeha, domin yana so su ɗan saba kafin bikinsu. Data turo masa Number ne sai ya soma kiranta a lokacin, sai yaji call waiting, ya kira sau biyu duk tana waya hakan sai ya bashi mamaki da tunanin da waye take magana da shi haka, duk da yana da tabbacin ba tada zawarawa amma jikinsa yana bashi kamar da wani take magana, nan take ya ji kishi ya ɗarsu a zuciyarsa wanda bai taɓa tsammani ba saboda shi mutum ne da ba ruwansa da wani kishi shiyasa matarsa Nabila take yin yadda taso, bata zama a gida kuma hakan ba ya wani dame shi bane, amma kam yadda yake jin Sameeha a zuciyarsa komai ma zai iya faruwa. Bayan ya bada wasu mintuna sai ya kuma kira, a wannan lokacin ne yaji bata yin waya sai dai bata ɗaga ba, hakan yasa ya miƙe da sauri ya shiga bedroom ɗinsa ya sauya kaya ya fito falo ya samu Nabila tana cin abinci.

Sai ina kuma? Naji kace zaka yi barci da wuri saboda da safe zaka wuce Abuja.

Taɗi zani wajen ƙanwarki.

Kallonsa tayi sheƙeƙe tana 'yar dariya.

Wasa kake yi, dan nasan ba kada wata mata sama da ni Nabila. Kama daina wannan zencen dan nasan ba mai yuwuwa bane.

Allah ko Hajiya Nabila, to ki zuba ido kiyi kallo domin wannan karan da gaske nake ba wasa a ciki, idan naje zan kira ki ki gaisa da ita domin ki tabbar. Kuma ki fara lissafin abubuwan da kike buƙata na faɗar kishiya, sai na baki kuɗin ki haɗowa kanki.

Baki sake Nabila ta bishi da kallo har ya fice daga falon ta kasa yin magana, da farko ta ɗauka wasan daya saba yi mata ne yayi, amma kuma yadda taga yana maganar fuskarsa washar ta soma gasgata haka, nan take taji abincin ya fice mata a rai ta tura plate ɗin ta soma kiran wayar wata ƙawarta Shema'u, tana ɗauka ta koro mata bayani tana ƙarawa da cewa.

Allah zuciyata ta karaya ina ga da gaske yake duk da shi ya tabbatar mini da baya sha'awar mata biyu.

Hmmm kin zauna ya gama jirgaki kin hau kin zauna, an faɗa miki namiji ba ɗan kunama bane, sai kin saki jiki kin daidaita zama ya gantsara miki cizo, kina tunanin yadda kike yawo ƙasa ƙasa ba kya zama hakan ba zai dame shi ba ko, to ko wannan dalilin zai sa ya ƙara aure kuma dama 'yan uwansa tuntuni suka so ya ƙara, kinga kuwa dole watarana zasu ci galaba akansa ya amince, idan zaki tashi tsaye gwara ki miƙe dan wlh in kika bari wata ta shigo zata amshe komai na uwargida tunda ke baki ɗauki auren a bakin komai ba sai niman kuɗi.

Idan akan niman kuɗina ne to wlh yaje yayi ta auren ai ba kaina zata zauna ba, kuma nasan dai har abada bata isa ta kamo ƙafata ba tunda ni ina da kuɗi, kuma ba daga gidan talauci ya aureni ba.

Haka zaki faɗa ko? Wai ke kuɗi zai iya sayan darajarki da komai ko, ana maganar kishiya kina niman nuna baki damu ba akan kuɗi. To Allah ya tsayar akan ki, idan kin so zaki iya zuwa gidana muje gidan wani malami domin ayi aikin da zai hana auren, idan kin manta bari na tuna miki itama amayar zata zo ta haihu kuma duk dukiyar da Ibrahim ya tara da ita za aci, kuma yana faɗi ya mutu gado ya zana keda ita da yara kinga kin samu naƙasu a kasonki.

ÆŠan jim Nabila tayi dan sosai maganar Shema'u ya zauna a zuciyarta, sai ta nisa tana cewa.

Zan zo muyi maganar da safe In Sha Allah dan ban yarda kowa ya rabi dukiyar Ibrahim ba wlh.

Da dai ki zauna ki ga zama. Sai kin zo É—in.

Cewar Shema'u, nan suka yi sallama suka kashe wayar Nabila ta miƙe tana kwalawa mai aikinta kira ta fito daga ɗaki da sauri, sai tayi mata umarnin ta kwashe plate ɗin data ci abinci ta kai kitchen ta gyara gurin, sai ta wuce ɗakinta tayi shirin barci sai dai tunanin maganar auren Ibrahim ya tsaya mata a rai, gani take kamar wasa yake yi mata, sai dai maganar Shema'u na zancen ta miƙe taye akan kar wata tazo gidan ta rage mata samun wasu kaso na dukiyarsa, yayi matuƙar tasiri wanda take jin zata iya aikata komai ma dan kar hakan ta faru.

Ibrahim wajen tara da kwata na dare ya isa ƙofar gidansu Sameeha wanda ya samu motar Shamsu a Kofar gidan, hakan ya tabbatar masa da yana cikin gidan, ya kirashi yana ɗauka yace.

Sarkin zumuɗi ashe har ka iso, to ka yiwa Ikram magana ta sanar da yayarta ina ƙofar gida ta fito ina cikin mota.

Shamsu yana 'yar dariya yace to kana ya kashe wayar ya duba Ikram ya sanar da ita sakon Ibrahim, da sauri ta miƙe ta wuce cikin gida ta samu Umma a falo ta sanar mata, Umma tace.

Ki shiga ki faÉ—a mata tana ciki nasan dai bata yi barci ba.

Ikram ta wuce ciki ta samu tana kwance tare da danna waya kamar chart take yi.

Anty Yaya Ibrahim yazo yana waje a cikin mota.

Kije kice nayi barci bana cikin yanayin da zan fita masa.

Haba anty ba zai ji daÉ—i ba fa, kin san yau ne farkon zuwansa ki daure ki saurare shi tunda anriga an gama magana yana da damar da zai ganki, sannan ki aje batun Aminu dan wlh yayi hakane dan ya farraka farin cikinki.

Hmmm sarkin tsara zance, to jeki ce ina zuwa.

Sameeha ta faɗa tana zuro ƙafarta ƙasa, Ikram murmushi tayi ta fice. Sameeha babban Hijab ta zura ta saka wani plat shoe ta fito Umma tana cewa.

Ki dai saki fuskarki karki yarda ya gane kina cikin damuwa, kuma lokaci yayi da zaki yakice matsalar Aminu da 'yan uwansa ki fuskanci farin cikin daya tunkaro ki.

Humm tace bata iya magana ta fice, har jikin motar ta isa ta tsaya a waje, ya sauke gilass É—in mota yana cewa.

Ranki yadaÉ—e ayi mini alfarma a shigo mota saboda bana so mutane su gane nine a nan dan Allah, naso na shiga gida to Shamsu ya riga ni.

Bata ce komai ba ta je back seat ta kama zata buɗe sai ya cire motar a key ta buɗe ta shiga baya ta zauna ƙafarta suna waje, shima ya ɗaga glass ɗin motar ya ƙara AC ya juya yana dubanta, a hankali ta buɗe baki ta gaishe shi ya amsa fuska sake yana cewa.

Gimbiya ɗazun nine na kira na samu call waiting sai kuma na ƙara kira baki ɗaga ba, Allah yasa ba da x mijinki kike waya da shi ba, dan jikina ya ba ni da namiji kike magana.

Da sauri ta ɗago tana kallonsa dan taji mamakin fururucinsa, Ibrahim ya ɗage mata gira yana murmushin gefen baki sai ta sunne kai ƙasa ya cigaba da cewa.

Idan ina son abu na saka shi a raina ina iya hasashe akansa koda ba haka bane abinda na faɗa za a iya jiyo ƙamshin gaskiya. Dalilin daya saka na zo kenan dan ƙin ɗaukar wayata da kika yi, koda yake ƙila bakya ɗaukar number saboda tsaro. Da fatan kina cikin koshin lafiya.

Lafiya lau.

Ta bashi amsa a takaice, Ibrahim ya kira sunanta ta É—ago kai tana kallonsa ba tare da ta amsa ba.

Ina sonki har cikin zuciyata tun ranar dana yi tozali dake, ban taɓa kawo zan ƙara aure ba domin ni bani da ra'ayin haka, amma yanda kika samu gurbi a zuciyata naji bazan bari damar hakan ya kuɓuce mini ba tun sa'ilin dana samu labarin ba ki da aure, na tabbatar mijinki yana cikin cizon yatsa da kaicon rabuwa da ke domin kuwa ke Zara ce a cikin taurari, a ɗan binciken dana yi na tabbatar kina da tarbiya da kuma kyakkyawan hali, dan haka nake muradin zamowarki mata a gareni domin ki zame mini sanyin idaniyata, da fatan zaki zamo mini cikon addini na.

Tun sadda ya soma magana ta sunne kai ƙasa take saurarensa har saida ya kai aya kafin ya yi shuru, amma ta kasa magana, saboda tunaninta yafi karkata akan Aminu da maganganun da ya gaya mata ɗazun, sai tsinkayo maganar Ibrahim tayi yana cewa.

Nasan ban isa na samu gurbi lokaci guda ba a zuciyarki, saboda bansan irin ginin da Mijinki na baya ya gina ba a zuciyarki, hakan yasa nake jin rauni da sarewa musamman a yadda naga kin fito fuskarki ba walwala, hakan ya sa mini tunanin ko na takuraki ne da aurena, dan na san nayi miki katsalandan ban fara jin ra'ayinki ba na turo magabata na, dan haka har yanzu kina da zaɓi ina son duk abinda kike so, ni zan iya janyewa na haƙura muddun hakan zai saka ki cikin farin ciki Sameeha, nasan zan jima ina jinyar zuciyata amma dole zan haƙura na jure.

Nan ma Sameeha bata yi magana ba sai hawaye data ji yana ciko idanunta, ba zata ce Ibrahim yana da makusa ba dan tabbas taji zata iya zama da shi, amma tasan ba zata sake son wani sama da Aminu ba, tabbas ƙaddara tayi mata kutse a rayuwarta dan tunaninta da komai ya koma gun Aminu, gani take so da kishi yasa shi kasa danne damuwarsa har ya kirata ɗazun, mamakinta taya aka yi ya samu labarin aurenta. Ibrahim shuru yayi shima dan ya kula ba zata yi magana ba sai da suka ƙara minti goma a haka kafin ya kuma cewa cikin sanyin murya wanda yake nuna damuwa a tare da shi.
Chapter 53 · 0% Book details