Sashe 35
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka fice suna hirar abinda ya faru, Umma ta ce mutane da suka shigo su fice tunda an gama abin kallo, suna fita ta rufe ƙofar gidan ta dawo ciki ta wuce kitchen ta shiga haɗa wutar gawayi dan ɗaura musu ruwan wanka, su Zaidu zama suka cigaba da yi sunyi jugum jugum kamar waɗanda aka yiwa shegen duka, kowanne fuskar a dame tare da baƙin cikin abinda ya faru, Sameeha kam lokaci zuwa lokaci take share hawayen da suka gangaro mata, ba ƙaramin jarumta tayi ba data basu yaran, tasan sune sanyin idaniyarta in tana ganinsu zasu ɗebe mata kewa da kuma damuwar da take ciki, amma tasan halin su Hauwa idan bata bada yaran ba sun dinga jelar zuwa kenan aita ɗauki ba daɗi, shiyasa ta kawo karshen rikicin ta miƙa su tasan da wuya Aminu ya barsu a hannun Hauwa, ƙila ya dawo mata da su kafin ya shirya karɓansu a hannunta, wannan tunanin yasa ta ɗan ji sanyi a ranta da fatan Allah yasa ya dawo dasu.
***
Su Hauwa suna isa babban gida suka tadda Sa'a tana daka yaji tana gqninsu ta saki daka tana guda da murna akan sun yi nasarar kwato yaran, Hauwa tace.
Dalla matsa ki bawa mutane guri mai shegen tsoron tsiya, ai kam anyi bake dan sai da muka kwashi 'yan kallo kafin suka bamu yaran.
Ai shiyasa naga kun daɗe ashe anyi taraliya, to madalla tunda kunyi nasara. Laure Alhasan ya dawo fa ya tambaye ni ina kike nace kin leƙa gidan Hauwa, bai daɗe da fita sallar la'asar ba.
To sannunshi da dawowa, ina daidai da rigimarsa dan nasan sai yayi faÉ—a.
Cewar Laure tana taɓe baki tare da zama a ƙaramar kujera saboda gajiya da tsayuwar da suka yi a gidan su Sameeha.
Laure zama bai gambu ma mu tashi muyu sallah kafin mu zauna zaman labari, dan sai na huta sosai kafin zan wuce gida da yaran, idan ma Alhasan ya shigo ma faɗa masa, dan Wlh dole yara su dawo hannunsu tunda muke da alhakin riƙonsu.
Ke barni na huta wlh ƙafata minjirya take yi mini tsabar na daɗe a tsaye, ga nan muƙamuƙi na har riƙe mini yake saboda wage bakin da nayi ina masifa.
Hauwa taja wata kujera ta zauna, Sa'a ta koma gurin dakanta tana jefo musu tambayar ya suka kwashe dasu Sameeha, Hauwa ta shiga rattafo mata zance Laure na tayata, suna tsaka da hirar Alhasan ya dawo ya shigo gidan, ganin yaran Aminu da kaya sun rakuɓe a guri guda yasa shi kallon su Hauwa ya ƙarasa nesa dasu kaɗan ya tsaya.
Kar dai zuwa kuka yi ku ka É—auko yaran nan?
Wlh yaya zuma muka yi ni da Laure muka amso su, saboda ya dace yara su dawo dangin ubansu tunda muna a raye zamu iya riƙe su, saki uku yayi mata balle mu barsu a hannunta mu saka ran zai maidata. Kafin su bada yaran ma sai da muka yi bata kashi tukuna.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Aminu shine yace ku É—auko masa yaran ko gaban kanku kuka yi.?
Haba Alhasan sai yace aje a ɗauko su? ai ya dace dama su dawo nan mana tunda dai yara da wayonsu babu mai shan nono, kuma ai da uba ake ado, shi kanshi Aminu zai ji daɗin mun sauƙaƙa masa ɗauko su da zai yi.
Cewar Laure cike da ƙarfin guiwa, Alhasan ya kawo wuya sosai dan ransa yayi matuƙar baci.
Da izinin waye kika bi Hauwa É—auko su? ko nayi dake zaki je?
Abu na zumunci har sai na nima izini Alhasan, ai wlh Aminu tamkar É—an uwana yake shiyasa nima na tafi, an zam É—aya.
Lauratu ki tashi ki tafi gidanku na sakeki saki ɗaya kuma wlh idan kika ƙara wata magana sai na datse duka igiyar aurenmu dan na gaji da halinki, da ba haka kike ba amma yanzu da girma ya kamaki madadin ki ƙara hankali amma sai kike ƙara zama yarinya, to na gaji. Ke kuma Hauwa ki tashi ki mayar da yaran nan tun kafin na kai hannuna jikinki Wlh dan baki fi ƙarfin duka ba a guna, shegiya mai mugun hali, na rasa ina kika samo wannan halin naki na rashin hankali da son zuciya, kina yin abu sai kace jahila, zaki tashi ki mayar dasu ko sai na ɓallaki a gidan nan.
Ya kare maganar a fusace, Hauwa ta miƙe ranta a ɓace tana jin kamar ta ɗuɗɗura masa zagi sai dai ba hali, ta wuce inda yaran suke ta daka musu tsawa akan su tashi su wuce.
In kika kuskura kika huce akansu sai na baki Mamaki Hauwa kuma zan kira na tambaya naji ko kin mayar dasu shashasha.
Cewar Alhasan daya wuce zuwa part É—insu, Laure ta bi bayansa tana yi masa magiya.
Dan Allah Alhasan kayi haƙuri ba zan sake ba sharrin shaiɗan ne, yanzu ace sai da muka doshi hanyar tsufa zaka sakeni ga yara duk sun girma harda surukai, dan Allah ka rufa mini asiri kamar dani, dan wlh da kunya naje gida nace ka sakeni.
Na dai gaya miki ki tafi gidanku, da can baki san kin girma ba kike abu sai kace kina cin ƙasa, ashe kin san kina da surukai kike aikata duk iskancin da kika ga dama, to na gaji wlh.
Har suka shiga ɗakinsu tana bashi baki shi kuma yana yaɓa mata magana, Sa'a sai da suka kulewa ganinta kafin ta saki wani uban shewa.
Allah na gode maka daban bisu ba dani ma yau tawa ta sameni, yau dai Laure kina ruwa kusa da kada, ashe duk cika bakine akan baki tsoronsu gashi a gabana ya danƙara miki saki, da sannu kowa zai girbi abinda ya shuka, shiyasa tun wuri na samawa kaina lafiya na kama aurena In Saha Allah bazan sake biye ta taku ba ku kaini ku baro.
Sai ta cigaba da daka tana daga taɓarya tana wakar Marigayi Mamman Shata.
_Ku gargaÉ—i mai gina ramin mugunta..._
Tana yi tana murmushi. Hauwa kuwa tana fita gidanta ta wuce da yaran ta saka kayansu a ɗakinta tace su zauna a falo suyi kallo, sai ta shiga kitchen ta ɗaura girki tana yi yana sakin maganganu duk kuwa akan Alhasan, ba ƙaramin haushi taji ba akan sakin da ya yiwa Laure amma tasan dole zai mayar da ita tunda da igiya biyu, in ba haka ba ai zasu ja musu magana Aminu ya saki mata shima ya saki Laure abu kamar shirin film, ga bikin Salma saura kwana shida, tunawa da tayi da wani kawunsu ƙanin Umma yasa ta fito daga kitchen ta ɗauki kawayarta ta kirashi, bayan sun gaisa ta koro masa bayanin abinda ke faruwa, nan yayi ta salati ya shiga yin faɗa akan ya Alhasan da girmansa zai saketa wannan shirme ne yace, tabar maganar a hannunsa zai shigo da dare gidan, Hauwa ta roƙeshi akan karya faɗa musu ita ce ta kira shi, yace karta damu sai suka yi sallama.
Salma data dawo daga wajen gyaran jiki ta yada Zango a sashin Sa'a, nan take bata labarin abinda ya faru cikin faÉ—a Salma tace.
Allah ya ƙara, gwara da ya saketa suna abu sai kace basu girma ba, wannan ai jakanci ne da rashin hankali su jawa mutane zagi, aiko yanzu zan faɗawa yaya Aminu yazo ya ɗauke yaransa dan Hauwa ba tunani ke gareta ba.
Tana kaiwa nan a maganarta ta danna number É—in Aminu ta kira shi, yana É—auka suka gaisa kana ta shiga bashi labarin abinda su Hauwa suka yi, Baiyi mamaki ba dan yasan zasu aikata abinda yafi haka.
Allah ya kyauta yanzu haka muna hanya zan dawo Kaduna daga Kano zan zo gidan na É—auke su ki rabu da ita, sai dai ta ganni naje kawai.
Yafi, dan Wlh ni bana son abinda suke yi, ga Laure nan itama Yaya ya saketa, ayi mata sai kace tinkiyoyi basu san ciwon kansu.
Allah ya kyauta Aminu ya kuma cewa sai ya kashe waya yana jin wani baƙin ciki yana daɗuwa a zuciyarsa, shi kam bai san me zai yi ba ya rama abinda Hauwa take masa ba, hanya ɗaya ne ya yarda da aure data ce masa shine zai yi maganinta wlh, ya faɗa a ransa yana cije leɓensa.
Sai bayan sallar Magriba Aminu ya shigi kaduna, yasa driver ya wuce dashi gidan Hauwa, da suka isa ƙofar ya fito daga mota ya shiga gidan kai tsaye har zuwa falo ya yi sallama, yaransa suna jin muryarsa suka tashi daga abincin da suke ci faten doya, dan tusawa kawai suke yi badan suna jin daɗinsa ba sai dai Hauwa data matsa sai sun ci, Aminu yana shigowa Amrah ta ruga da gudu taje ta rungumeshi shima ya kamata, Abi shima yazo ya rungumeshi ta gefe, a lokacin Hauwa ta fito daga daki.
Aminu har ka dawo nayi zaton ai zaka kwana can.
Wlh ganin mun gama meeting É—in yasa nace bari na dawo, to da yake an sanar dani kin É—auko yara shiyasa na zo nan.
Halan su Sameeha ce suka faÉ—a maka, ai É—azun sai da muka yi tsiya kafin suka bayar da yaran.
Kin kyauta kuwa danni ma ina da niyyar amso su, amma yanzu zan tafi dasu gida mu kwana dan nayi kewarsu, jibi monday In Allah ya kaimu zan dawo dasu nan tunda a ranar zan koma Abuja.
To ba damuwa, kai Abi jeka É—auko jakar kayanku ku cire wanda zaku amfani dasu.
Yace to ya wuce da sauri ya kwaso akwatunan, Aminu yace.
Bari muje da kayan kawai in yaso sa kwaso na gida gabaÉ—aya su zo.
Hauwa bata kawo komai a ranta ba ta ce to dan sosai take jin farin cikin yadda ɗan uwanta yake binta sau da ƙafa saɓanin yana tare da Sameeha, shiyasa ta ƙara tabbatar da asiri tayi masa ta raba tsakaninsu wanda a da har rashin kunya yayi mata akan Sameeha. Har mota ta rakasu suka wuce kana ta dawo gida.