← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 98

Sashe 73

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga najwa nan a gabanku ku ji tabbaci idan sharri nayi mata, sannan ma akwai CCTV ɗin falona daya yi recoding komai, kuma akwai ƙawarta Nafeesa da zan iya kiranta yanzu tazo domin ta ƙara gasgata wannan labari. Sannan a hanyarmu ta zuwa saura kaɗan motar Tifa tabi ta kanmu Najwa data kama sitiyarin mota akan gwara ta kashemu dana tona mata asiri, idan muka fita zaku ga layin da motar tifar ya gogi gefen motata. Wannan dalilin yasa na buƙaci mu haɗu anan domin na bayyana komai na kuma wanke Sameeha akan sharrin da suka yi mata, yadda na godewa Allah maganar babu wanda yasanta sai mu nan kawai a yanzu. Amma Najwa ita ce ta aikata komai sannan ita tasan yadda ta haɗu da Hauwa har ta zaɓa mini ita a matsayin mata.

Salati kawai suke yi Inna kuwa ta kasa daurewa sai kuka take yi, Baba kam girgiza kai yake yi Yaya Junaid ya kalleta cike da takaici.

Kinyi asara Najwa ki rasa wacce zaki cuta sai Sameeha 'yar uwarki ta jini saboda son zuciyarki, babu mai mugun halinki a gidanmu bansan a ina kika samo shi ba, gaki da Ilimi amma sam baki yi aiki da shi ba Allah ya shiryeki.

Najwa kuka mai sauri ta fashe dashi dan tuni ma ta saki fitsarin daya matseta a gurin, ga gumi data ke fitarta na rashin gaskiya, tunda take bata taɓa jin ta muzanta ba a duniya irin yau, Sameeha ce ta jefa mata magana wanda yasa ta ɗago da sauri da take cewa.

Najwa me na tare miki a rayuwa dana cancanci irin wannan hukuncin a gareki? meye ribarki idan kin yi mini sharri an sakeni, ashe dama duk zuwan da kike yi kina gane mini sirrin gidana ne kina son ki auri mijina, nayi zaton Jamila 'yar aikina itace abin tsoro da nake takatsantsan da ita ashe kece abin tsoro ban sani ba.

Itama Jamila ai wu Hauwa suka turota domin ta riƙa faɗa musu duk halin da kike ciki, sannan Jamila da ita aka haɗa duk wani makirci, kuma Hauwa itace shugaban haɗa komai.

Najwa ta faÉ—a cikin kuka, Junaid ne ya wanka mata mari yana nunata da yatsa.

Saboda baki da kunya har kin samu damar yin magana ko, 'yar iskan yarinya mai mugun hali, wlh Najwa saina karyaki kinyi jinya, sheÉ—aniya mara imani da tausayi.

Najwa miƙewa tayi jikinta yana yararin fitsari tana kuka da ƙarfi dafe da kuncinta.

Yaya karka barni da rai ka kashe ni ku huta dama nasan ba ƙaunata kuke yi ba, da wanne zanji kowa ya tsaneni ya ɗaura mini laifi bayan ba ni kaɗai na aikata komai ba. Laifi ne dan naso mijinta? laifine dan na aureshi? ai ko a musulunci banyi haramci ba tunda ba da iskanci na yi ba, laifine dan na zaɓawa kaina auren mijin dana san zan huta a gidansa fiye da gidanmu, shikenan komai na ɗaukaka sai dai a ganshi a gunsu nice a baya.

Ai dolw ki ganki a baya tunda kin saka hassada da mugunta a zuciyarki, wlh Najwa kin bamu mamaki babu wanda zaiyi tunanin zaki aikata mana haka, to Alhamdulillahi kin rabata da gidan Aminu gashi ta samu kanta a gidan daya fi nashi ɗaukaka da komai, idan kina yi musu hassada to taki kike ƙara musu na daukaka, kuma ba dasu kike faɗar ba da Allah kike yi shiyasa ya nuna miki ikonsa, kaɗan ma kika gani.

Cewar Zaidu yana nunata da tsaya, Najwa taja guntun tsaki tana yatsine fuska.

Kai dai kaji haushi ne saboda nace bana sonka, kuma bana sonka É—in domin ba kada komai da zaka bani, dan a jikin Sameeha kake samun na kashewa, Allah ya kyauta.

Ke banason shashanci kinyi laifi amma kina da bakin da zaki yi magana, kaji min 'yar banza mara mutunci, zaki zauna ko sai na saka junaid yayi miki mugun duka da sai kinyi jinya dan mu huce takaicinmu.

Cewar baba cike da ɗaure fuska, Najwa ta koma ta zauna tana gunguni, itafa har yanzu ta ƙi karɓan laifinta shiyasa take zuba borin kunya, ta kuma nuna musu ba tada kunyar. Sameeha kam shuru tayi dasu umma dan abin nata yafi ƙarfin lissafinsu, Baba yace sai Najwa ta bawa Sameeha Haƙuri akan abinda tayi mata, Najwa tayi shiru taƙi magana, baba zai fara faɗa Umma ta dakatar dashi akan.

Malam ka rabu da ita har yanzu babu alamar nadama a tare da ita, dan haka ita Sameeha ko ta yafe ko bata yafe ba ta ga kyakkyawar sakamako kuma bata ma gama ganin Nasara ba In Sha Allah, Addu'a za mu taru mu yiwa Najwa akan Allah ya shirye ta, dan tuntuni na fahimci ta sauka daga tarbiyyar da kuka bata, sai kun saka ido sosai akan abokan da take hulÉ—a dasu.

Baba girgiza kai kawai yake yi yana cewa.

Dan Allah Halima kuyi haƙuri an cutar daku Allah ya saka muku, Aminu in ka gama magana mu zamu tafi.

Aminu ya gyara zama yana ciro farar takarda a haljiunsa ya aje a gaban Najwa yana cewa.

Ni Aminu na saki Najwa saki biyu ban ɗaura mata idda ba in ta samu muji tayi aure, sannan kuma na bada damar aje a kwashe kayanta a cikin makon nan dan zan rufe gidan na koma bakin aikina. Baba kuyi haƙuri akan hukuncin dana yanke domin koda Najwa bata yiwa Sameeha sharri ba bazan iya zaman aure da ita ba tana a matsayin 'yar uwarta, sannan ma ni bani da lafiyar da zan zauna da wata mace a yanzu. Sameeha ki yafe mini nasan na shiga hakkinki keda yara dana rabaku, dan haka a yanzu na yanke hukuncin yara sun dawo hannunki idan mijinki ya amince zai zauna dasu to ba damuwa, in kuma bai yarda ba ki barsu a gurin Umma nasan zasu samu tarbiyya mai kyau da kulawa, sannan zan riƙa biya musu kuɗin makaranta da duk wani hakkinsu dake kaina ban yarda kowa yayi ba, ina tunanin a cikin wata mai kamawa zan bar ƙasar nan zanje London yin wani aiki na shekara biyu In Sha Allah zan riƙa kira ina waya dasu Abi, umma ni zan tafi na barku lafiya ku yafe mini.

Allah ya yafe mana gabaÉ—aya kuma Baka mana komai ba Aminu, Allah yasa albarka a cikin tafiyarka ya baka nasara da lafiya mai inganci.

Aminu ya amsa da amin yana jin hawaye yana cika masa ido sai kewar mahaifiyarsa ya taso masa, ya mike yana yiwa su baba sallama suma fatan alkhairi suka yi masa sai ya wuce, Ikram ce ta kwalawa su Abi kira, da suka fito tace suje gurin babansu ya fita, Sameeha kam tausayin Aminu ne ya kamata sai ta miƙe ta shiga ɗaki tana matsar kwalla, Ikram ma tabi bayanta duk jikinta a sanyaye sosai itama taji tausayinsa, Najwa kuwa suman zaune tayi tana hawaye mara sauti sai yanzu ne jikinta yayi sanyi jin wai Aminu ya saketa bayan ya tona mata asiri sannan kuma ya rabu da ita ta zama bazawara, Abun da ciwo aure da kwana ɗaya an saketa, wannan wane irin mummunar ƙaddara ce yake binta, ita kam ta shiga uku ta lalace ta samu biyan buƙata a lokaci guda kuma a lokaci ɗaya ta rasa komai, sai kawai ta ruse da kuka mai sauti.

Shikenan na sara komai a lokacin da nake farin cikin na samu, ni kenan banda sa'a a rayuwata, jiya jiya aka ɗaura yau ya sakeni ina zan saka kaina naji saukin wannan baƙin ciki, inna dama sai da kika yi mini baki gashinan ya bini, kun tsaneni saboda na zaɓawa kaina abinda nake so.

Ta cigaba da muka baba ya miƙe yana cewa.

Najwa ai shi mugun abu É—an aike ne muddun ka aikashi wlh sai ya dawo maka, kaÉ—an ma kika gani Allah ya tsayar a kanki ya kuma shiryeki, ke Zulai tashi mu tafi gida, Halima mun gode Allah ya jikan Ahmadu ya yafe masa.

Baba ya ƙare maganarsa yayi gaba, Inna ma godiya ta yiwa Umma akan in an kwana biyu zata dawo sai tabi bayan baba Umma tayi mata rakiya har gate, Junaid ne ya tasa ƙeyar Najwa suka wuce tana kuka wiwi, Zaidu kam miƙewa yayi ya ɗauko buta ya zuba ruwa a inda Najwa ta zauna tayi musu fitsari, ya bi bayan umma data shiga ɗaki suka zauna jugum jugum Ikram ta katse shurunsu da cewa.

Ashe Najwa ta jima tana aikata mana mugun abu wlh ta bani mamaki, ashe makashinka yana tare da kai, gashi ba aje ko ina ba ta wulaƙanta ya saketa a gabanmu kuma jiya aka ɗaura aure yau an saketa, Allah ya kyauta ta gyara mana imaninmu.

Ameen, amma ina so mubar maganar haka dan ba tada daÉ—i, Sameeha sai komai ya wuce a ranki tunda gaskiya tayi halinta ki kama mijinki da kyau, sannan batun yara ki barsu a nan kawai in kin zo hutu kya gansu, bana so a takurawa Ibrahim.

Laaa umma ai baida matsala shima yace da Aminu zai bar mana su, yana da son yara.

Duk da haka ki barsu anan hankali na zai fi kwanciya.

Amma umma bakya ganin su Hauwa zasu nima takura miki in suna nan.

Cewar Sameeha, Zaidu yayi murmushi yana cewa.

Ai da ba yanzu bane Sameeha sun san munfi karfinsu, ai basu isa su kawo mana iskanci ba wlh dan sun san wanda kike aure.

Nan Ikram tasa dariya tana cewa.

Wlh kuwa ai ba zasu yi mana hauka ba, kunsan ni mai ya bani dariya Najwa harda fitsarin Zaune tsabar borin kunya, duk fa wannan maganganun tabarman kunya ta naɗe da hauka, Allah dai ya shieyeta amma tasan munyi gaba hassada kuma ta cigaba da yi muna samun ɗaukaka, zan saka Shamsu ya saka mana kare a gidanmu yadda duk randa ta tako ƙafarta tazo gidana nasa suyi mata rakiya shegiya.

Amma ba kida kirki Ikram nasan ma ba zata zo ba, ai abin da kunya.
Chapter 73 · 0% Book details