← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 98

Sashe 95

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwatsam wani mai napep ya fito yana son auren Adama, da farko taƙi amincewa amma daga bisani dole ta yarda dan ya sakar mata kuɗi, Hauwa ta ce bata amince ba ta bari ta fita takaba sai tayi auren, kuma itama tana son tayi auren dan karta jawo mata abin magana saboda duk abinda take aikatawa tana samun labari gurin yaranta maza, amma a yanzu dole ta haƙura da auren domin sana'ar da take yi shike riƙesu, Adama tace ita aurenta zata yi domin ta samu miji kuma kayan ɗakinta suna nan basu yi komai ba 'yan siyayya kaɗan zata ƙara, Hauwa ta ki amincewa duk da haka saboda ganin in tayi aure zasu shiga damuwa tunda bashi ke gareta ba, Adama ganin zata kawo mata cikas taje har babban gida ta haɗa Hauwa dasu yaya Alhasan, su ka zo suka samu Hauwa suka yi mata tas akan lallai dole ta barta tayi aure tunda ta fita idda, da kuma ta ɗauko musu magana dan sarai suna da labarin rayuwar da take yi gurin sayar da abincin gwara tayi auren, ba da son ran Hauwa ba Adama tayi aure ba, wanda sati biyu kenan da aurenta ta tare juma'ar data gabata, sai dai itama Adama zuwa yau tana dana sanin auren tunda abinda Isyaku ya nuna mata a waje to ba haka bane acikin gidan, babban family House ya kaita sannan yana da mata da yara shida, ga sauran matan ƙannensa duk a gidan da kuma uwarsa, ɗaki ciki ɗaya ya sauketa wanda gado ne kaɗai ya ɗauka da tarkacen kayan kitchen, kujerunta sai dai aka mayar dasu gida, kwananta ɗaya a gidan ta fara shiga damuwa dan hayaniyar gidan kaɗai bazai barta ta samu barcin rana ba da take tunanin in tayi aure zata huta, dan bata saba da wahala ba a gidan mijinta na farko, a hankali ta gane ta tsoma ƙafarta a gidan rikici dan tunda tazo gidan kullun sai an yi rikici a tsakanin kishin saurinta, idan kuma a ka fara sai a ɓata lokaci mai yawa ana abu ɗaya. Jiya da dare ma hakan ta faru akan shiga bayi suka kafa dambe basu suka samu yin barci ba sai kusan ɗayan dare, Adama ta sanar da Isyaku ya sauya mata gida ita ba zata iya da wannan hayaniyar ba, kallonta yayi yana 'yar dariya.

Haba Adama ai ya kamata ki saba da hayaniya, tunda kin yi zaman bakin titi hayaniyar mota mashin da mutane duk kin sanshi, kinga kuma hayaniyar gidan nan da bambanci da wancan tunda ba kullun ake rikicin ba kuma naÉ—an wani lokaci ne.

Wlh ban taso a gida irin wannan ba ba zan iya ba gaskiya.

A hankali zaki saba, dan bani da halin kama miki haya nan ne iya ƙarfina.

Hmmmm wlh da sake.

Ta faÉ—a tana girgiza kai dan ga dukkan alamu wannan auren nata bazai je ko ina ba, shiyasa kamar ta sani ta tsiri yin planning dan bata yarda ta samu ciki da wuri ba sai ta ga kamun ludayin auren, bata yarda tayi ta raba yara ba hakan yasa ta É—an samu natsuwa da tunanin fara shirin fita daga gidan.

Yau juma'a kamar yadda ta roƙi mijinta zata gida, bai hanata ba dan ba ita ke da girki ba, da wuri ta shirya ta bar gidan dan gabaɗaya ji tayi ta gundura da komai na gidan, wajen sha ɗaya ta nufi gida sai dai ko da ta isa ta tadda Hauwa bata nan ta fita niman musu abinci dan zama bai ganta ba tunda Adama tayi aure, kuma musulunci ya yarda mace ta fita ta nima abinci matsawar ba tada mai taimaka mata in tana takaba, hakan yasa Adama ta zauna zaman jiran dawowarta dan tazo ne suyi shawara akan maganar kashe aurenta da take son yi.

Hauwa kuwa rafin guza ta nufa taje wani gidan mai kuÉ—i da yake bayar da taimako, labarinsa ta samu shine tayi takanas taje dan ta samu rabonta, sai dai ta taki sa'a baya gari, dole ta kuma hawa napep da nufin dawowa gida, har sun wuce layin su Sameeha ta tuna wani abu sai ta sa mai napep ya sauketa ta biyashi ta wuce zuwa gidan, tana isa ta kutsa ciki tana sallama sai dai daga ciki aka amsa mata sai ta shiga falon ta tadda umma tana kishingiÉ—a a doguwar kujera, umma tana ganinta ta tashi ta zauna tana yi mata maraba fuska cike da fara'a, Hauwa ta zauna ta gaisheta kana ta É—aura da cewa.

Na zo wani dubiya ne can sama shine nace bari ba biyo mu gaisa sannan naga yarana na wajen Aminu dan ance suna nan.

Aiko suna nan amma suna makaranta driver taje É—aukosu. Ya kwana biya da yaran.

Lafiya lau Alhamdulillahi, nasan baku san mijina ya rasu ba ko, yanzu haka ina cikin takaba dole ce tasa na fito.

Allah sarki wlh bamu sani ba Allah ya jikansa da Rahma ya bada haƙurin rashi, na tausaya miki dan rashin miji ba daɗi saboda nima na san shi.

Hakane gashi ya tafi ya barmu cikin yanayin rayuwa abubuwa sun sauya komai ya tsaya mana, dan Adama ce ke nima mana ta yi aure sati É—aya kenan da tarewarta.

Allah sarki sai haƙuri da rayuwarki kam, Allah ya sanya alkhairi ya rufa mana asiri duniya da lahira.

Ameen ya rabbi, dama nace a faÉ—awa Sameeha in lokacin Zakka yayi a sakamu a cikin list dan nima yanzu na shiga jerin masu marayu, kuma dama Aminu ne mai taimakon to shima yayi fushi dani dan rabona da shi tun washe garin bikinsa ko gaisuwar mijina bai kira ko yazo ya mini ba.

Kai Amma lamarin bai yi daɗi ba, ai ba a fushi da ɗan uwa, In Sha Allah zan yi masa magana dan yana kira yayi magana da yaransa, kiyi haƙuri In Sha Allah komai zai wuce. Bari a kawo miki abinci.

A'a wlh ki barshi tafiya zanyi dan na baro yara a gida har É—an Adama data bar mini yana hannu na.

To yanzu abinda za ayi ki fita ki samo me napep ku zo tare zai ki tafi da wasu abinci, kiyi haƙuri yaran duk basa gida balle su taro shi.

Haba wlh ba komai bari nayi sauri na samo.

Hauwa ta faɗa cikin sauri da farin ciki, ta fita umma ta bita da kallon tausayi gabaɗaya Hauwa tayi laushi ta sauya, ga wani baƙin wahala da rama data yi, wato idan mutum yace shi mara mutunci ne to duniya kaɗai sai ta koya masa hankali. Hauwa bata jima ba ta dawo ta samu umma tana fito da kayan abincin data bata, da yake ɗakin kusa da kitchen shine suka mayar store sannan an gyara mata kitchen ɗin anyi cabinet da komai na zamani dan hatta falon umma Sameeha sun sauya mata shi da kayan zamani, kuma bata amfani da gawayi yanzu sai gas cooker, umma ta bata rabin buhun shinkafa, katom ɗin taliya sai makaroni guda takwas, da sugar loka biyu, indimie guda goma, madara rabin loka, maggi jaka da gishiri, har da garin tuwo umma ta ɗibar mata, haka ta haɗa mata kaya sha tara na arziki sannan ta ƙirga dubu ashirin ta bata na nefane, Hauwa har tsugunawa ta yiwa umma a ƙasa tana zuba mata godiya har da kukanta, umma ta kamata ta ɗaga tana cewa.

Haba Hauwa ai zumunci yafi ƙarfin komai, duk da Sameeha bata gidan ɗan uwanku amma yara sun haɗa mu, dan duk abu na taimako in dai muna da hali za muyi muku Allah dai ya jikansa da Rahma, In Sha Allah kafin azumi zaki ga aike ko Zaidu yazo ko kuma Anwar zasu zo har gida.

Nagode Nagode dan Allah ku yafe mini abubuwan dana aikata muku a baya, wlh sai yanzu nake jin kunyar komai ashe kune waɗanda zasu ji ƙaina tun ba aje ko ina ba, 'yan uwana ido suka zuba mini amma gashi ke kin yi mini taimakon da ban taɓa zato ba.

Mu ai tuni muka yafe komai ya wuce, dan haka ki saki ranka damu wlh babu wani abu, ki yi maza ki tafi kin bar yara.

Hauwa tace to tana ƙara cigaba da godiya ta share hawaye da gefen hijab ɗinta, sai ta fita ta yiwa mai napep magana ya shigo ya tayata kwashe kayan suka saka a napep ɗin, data gama ta kuma yiwa umma sallama kana ta fito suka wuce, haka Hauwa ta nufi gida da wannan kaya da ko a mafarki bata yi zaton samunsu ba, lokaci zuwa lokaci take share hawayenta wanda yake ƙunshe da tarin dana sani, Hauwa bata taɓa karaya da abinda ta aikatawa Sameeha ba irin yau, sai dai kuma takara kullatan Aminu a ranta dan in da ya yafe mata ya taimaketa ba zata zo ta yi abin kunya ba a gidan su Sameeha, dan Abin da Ciwo ace naka shi ke bada kai, haka ta isa gida mai napep ya sauke mata kaya ta sallameshi da dubu ɗaya ya wuce, sai ta leƙa gida ta kwalawa yaronta kira ya fito, yana ganin kaya jiki yana rawa ya kinkimi shinkafa yayi cikin gidan, Adama ganin haka yasa ta fito itama ta tayasu kwashe kayan suka shiga gida, Hauwa ta zauna a barandar ɗakinta ko shimfiɗa babu ta cire hijab tana fiffita da shi, Adama ta kalleta tana cewa.

Mamaa ina kika samo waÉ—annan kaya goma ta arziki.

Yau dai cire kunya nayi na yi roko kuma ya yi mini amfani, tunda ga kayan abinci na samo har da kuÉ—i dubu ashirin.

Ikon Allah ina kika je aka baki mama a irin wannan marra da muke ciki yadda rayuwa tayi tsada, amma ko ba ƙaramin masu arziki bane kuwa.

Gidan su Sameeha naje Ummansu ta haÉ—oni da alkhairi, kuma na dinga samu kenan dan tace zata yi mini aike.

Kai mama yanzu can kika je kika zubar mana da ƙimarmu, haba haba wani irin gidansu Sameeha, haka kurum kisa suyi mana dariya, gaskiya banji daɗi ba wlh ko kaɗan.
Chapter 95 · 0% Book details