← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 98

Sashe 56

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faɗar kyawun da su Sameeha suka yi ɓata lokaci ne, domin wani tsadadden leshi suka saka su uku anko, umma da Sameeha ɗinkin doguwar riga buba, Ikram aka yi mata riga da siket saboda tace tafi son shi, musamman Khairy ta kawo mai makeup aka yi musu, sai zuba ƙamshi suke gwanin ban sha'awa, su Najwa ma sun saka anko tare da yin kwanliya sunyi kyau, Nafeesa kuma da bata samu anko ba ta saka atamfarta me kyau tasha kwalliya itama. Wajen ƙarfe goma sai ga su Hauwa, Laure, Sa'a da kuma ƙanwarsu Salma, sai 'yar Hauwa Adama data ce zata zo ta bawa ido abinci, dan har gida Zaidu ya kai musu katin gayyata da Umma tace akai musu saboda 'ya'yan Sameeha da suka haɗasu zumunci, koda suka shigo suna yatsine fuska Hauwa da Laure, ba wanda ya kula da su, su inna suka basu masauki a cikin tampol aka karramasu da abinci da nama zuƙu zuƙu a ciki dan kula guda aka basu da plate ɗin da zasu zuba, sai abin sha ruwan gora da kuma drinks, babu kunya suka buɗe ciki suka ci suka koshi, Hauwa har da cewa zata juye saura a leda ta tafi dashi gida dan dama ta yi alkawarin ɗibar abinci in ta samu da damar haka tunda ba kunya ce da ita ba, lokacin da su Sameeha suka fito har gunsu taje ta gaidasu suka amsa faran faran tare da taya ta murna, Adama da biyu tazo domin ta samu damar gayawa Sameeha baƙaƙen magana, amma yadda suka ganta tayi mugun haɗuwa ta sauya a Sameehar da suka sani yasa tayi musu kwarjini sosai, dan ta cika musu ido wanda a zahiri sun san tafi ƙarfin lissafinsu a yanzu, sai suka koma suna borin kunya tare da amsa maganarta cikin sauri kamar mai yi musu umarni, data gama dasu ta wuce ta koma inda take zaune dan ance zasu zauna guri ɗaya har sai an ɗaura aure, suna hango Ikram amma bata zo gunsu ba dan ba tasu take ba, Najwa kuwa tazo ta kwashi gaisuwa kamar dai irin sanin da ne data yi musu bata wani sake ba dan kar a gano wani abu, suna gaisawa ta wuce cikin gida.

Da yake ɗaurin auren safe ne tunda ya kama ranar asabar, ƙarfe sha ɗaya da minti goma aka ɗaura auren anan ƙofar gidansu wanda aka zuba tempol da kujeru waje da cikin gida, mutane sun zo wannan biki dan unguwar Rafin Guza a ranar sai da suka tabbatar da ana biki, saboda tarin mutane da manyan 'yan siyasa dama manyan motoci da Sarakuna, dan hatta Sarkin Zazzau ya halarci ɗaurin aure da gomna Kaduna mai ci a yanzu, faɗan yawan security ba a magana domin unguwar gabaɗaya aka zuba su tun daga farkon shigowa Rafin Guza har can ciki, kuma masu shigowa sai an duba motarsu dama mutanen da suke ciki, lamarin yayi matuƙar gigita tunanin al'umma dan babu wanda yayi zaton irin wannan ɗaurin aure. Bayan an ɗaura auren Sameeha da Ibrahim aka ɗaura na Ikram da Shamsu, a hankali mutane suka fara tafiya masaukinsu domin yin walimar da Ibrahim ya shirya musu a gidansa dake unguwar rimi, hatta sarki ya tafi can dan Ibrahim ya hana su tafi da sauran abokansa na 'yan siyasa, Gomna ne dai ya tafi saboda babban uzuri dake gabansa, bayan mutane sun ragu sai ga Zaidu ya shigo yana cewa Angwaye zasu shigo gaisuwar iyaye yanzu a gyara, hakan yasa mata duk suka kame gefe guda aka bar musu babbar tabarma dake shinfiɗe a tsakar gida, saura kuma suna rumfa a zaune a kujeru. Maroƙa ne da masu busa sarewa sune suka fara shigowa gidan suna busa sarewa wanda yake nuni da sarauta, sai maroƙa da suke nasu fadancin, Shamsu shine farkon shigowa fadawa suna zagaye dashi maroƙa suna yi masa kirari.

Taka Lafiya Shamsuddeen jikan wazarin Zazzau ɗan Wazarin Zazzauna, mulki a jininka take miji a gurin Ikram diyan Amadu da Halimatu Allah ya jikan Amadu domin kayi farar Haihuwa 'yarka ta dangwalo muku arziki wanda zai riƙa binku har 'ya'ya da jikoki.

Takawarka lafiya mai girma Senator Ibrahim Ali Turaki jikan Limamin Zazzau, ga ilimi ga nasaba, Allah ya ja kwananka ya ƙara lafiya ya kuma saka albarka a cikin wannan auren naku.

Wani daga cikin maroƙa yake jero nasa wannan kirari lokacin da Ibrahim shigo tare da securty ɗinta, nan fa kallo ya koma sama mata suka rikice kowa yana mamakin ganin Senator Ibrahim a cikin gidan, su Hauwa sai miƙewa suka yi suka zo suka tsaya dan tabbatar da abinda kunnensu yaji. Su Shamsu zama suka yi a tabarma Umma ta fito sanye dq hijab da sauran 'yan uwa da ƙawaye suka gaisa kana fa suka koma ciki, sai su Shamsi suka miƙe zasu wuce maroƙa suna ta kirari tare da ambato matsayin angwaye, a lokacin ne Khairy ta riƙo hamnun Sameeha suka fito daga dakin umma, Ikram tana a bayansu tare da Najwa da sauran ƙawayensu, Khairy ta ƙarasa da su gurin angwaye tana cewa.

Yaya ku tsaya ayi muku hotunan tarihi.

Sai ta kara Sameeha gefensa tana cewa mai hoto ya ɗauka, nan fa gida ta ƙara hargitsewa ganin Sanator Ibrahim shine angon Sameeha, su Hauwa suman tsaye suka yi suna rarraba ido, sosai suka tsorata da razanar ganin wannan lamari, Najwa kuwa gigicewa tayi ta tsaya tana kallonsu ana yi musu hoto jikinta har rawa yake saboda mamaki da tsoro, bata ƙara kurɓan gubar mamaki ba sai da taga an kara Ikram jikin Shamsu da har ta mutu ba zata mance fuskarsa ba yadda ta tsane shi saboda baƙinsa, wasu taurari suka soma gilmawa ganinta numfashim ya soma fita da kyar jikinta ya shiga kakkarwa, ga wani tururin zafi daya gewaye illahirin jikinta, dan sosai taji numfashi mai zafi take shaƙa ta fitar, sunan tsaye tayi dan kwakwalwarta lokaci guda ya daina aiki, har aka gama hotunan suka wuce ta nan a tsaye bata san wainar da ake toyawa ba, mutane kowa sai sambarka suke yi suna yaba wannan daraja da su Sameeha suka samu kamsu a ciki lokaci guda, su Hauwa kuwa giuwa sake suka koma mazauninsu suna mayar da numfashi, dan sosai suka yi mugun kaɗuwa da mazajen su Sameeha, hakan ya tabbatar da Sameeha ta take darajarsu ta shanye, yanzu sai dai su zama almajiranta ko 'yan koronta amma tafi ƙarfinsu, tayi musu nisa da tazarar da babu dawowa wanda dole ne a cewa mijin iya baba, dole su kwashi tsummar kunyarsu su ƙara gaba dan ko kallon banza basu isa su yiwa Sameeha ba in ba haka ba suna yin wata wargi zasu kwashi kashinsu a hannu. Najwa kuwa bata dawo hayyacinta ba sai da Nafeesa ta kamo hannunta ta kiran sunanta da cewa.

Najwa Najwa!

Jin bata motsaba yasa ta jijjigata sai taga ta biyota luuuu ta faÉ—a jikinta wanda ya tabbatar mata da a sume take.

*Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.*
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

37.

Nafeesa cikin dabara ta kamata ta jata zuwa wajen bayi da yake kamar lungu, ta shiga jijjigata tana kiran sumanta a firgice, da kyar Najwa tayi yaƙi da numfashinta ta fizgoshi da ƙarfi ya dawo jikinta, sai ta sauke anjiyar zuciya mai nauyi, nan take kuma jini ya soma fitowa daga hancinta yana gangarowa, jikinta ya mutu sosai yana rawa ta kasa tsayawa, sai ta kama hannun Nafeeda ta tsuguna tana fidda numfashi da ƙarfi dan a riƙe yake, Nafeesa itama tsuguwa tayi tana cewa.

Najwa kashe kanki za kiyi ne akansu? wlh ki dawo hayyacinki dan kema baki wuce ki ganki a matsayinsu ba, kar ki bari a gane halin da kike ciki ki jawa kanki magana dan Allah.

Nafeesa! Nafessaaa ba ba mijin Sameeha bane kaɗai ya girgizani, saurayina Shamsu shine angon Ikram, ban zata yana da arziki ba, ban ɗauka daga gidan sarauta yake ba, ya ɓoye mini komai saboda in zai zo hira gidanmu wlh bada mota yake zuwa ba, baƙin fatarsa yasa nake ganin muninsa har yasa na koreshi, na zalunci kaina na yiwa kaina illa yanzu dani ne a matsayin Ikram, shikenan ni banda sa'a, ashe arziki yana tare dani na guje masa.

Ta ƙare maganar cikin gunjin kuka mai tsanani wanda yasa Nafeesa ta toshe mata baki, dan itama maganar Najwa ya taɓa ta, yanzu take tuna Shamsu da take bata labarinsa, ashe shine mijim Ikram, lallai dara taci gida ba aje ko ina ba Najwa ta fara karɓan sakamako, ta raba Sameeha da mijinta gashi saurayin data wulaƙanta akan talaka ne Ikram ta aureshi kuma ɗan masu kuɗi gidan sarauta, sannan ga Sameeha tana auren Senator, wato dai hassada ga mai rabo taki, ta raba ta da mijinta akan ita ta shiga ta kwashi arziki sai ga Sameeha ta samu wanda ya fishi komai, har abada bata jin Najwa zata kama ƙafar Ikram balle ma Sameeha, ta sauke guntun numfashi daga zancen zuci da ta yi ta kalli Najwa tana cewa.

Yanzu tashi za kiyi mu fita daga gidan nan, amma karki yarda a gane halin da kike ciki kuma ki ɓoye zancen Shamsu saurayinki dan karki tada wani ƙura, muje gidanku muyi magana cikin natsuwa.
Chapter 56 · 0% Book details