Sashe 27
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan take mai gani ya gane muryansa cikin sauri ya buɗe ƙaramin ƙofa ya shiga, yana kokarin jan gate yace ya barshi ba da mota yake ba, Mai gadi ya kwaso kaisuwa Aminu ya amsa kana ya wuce, daya ƙarasa falo kamar zai yi nocking dan yasan lokacin sun rufe kofa amma sai ya fasa ya kama handle ya murɗa sai ya samu a buɗe yake, cikin mamaki ya shiga ganin falon ma da haske basu kashe wutan ba, sai ya wuce center table ya aje jaka da wayoyinsa ya nufi ɗakin Sameeha direct dan yasan yanzu haka barci ne ya kwasheta duk bata yi aikin rufe ƙofa da kashe wutan data saba yi ba. Yana murɗa handle ya faɗa ɗakin, ganin mata akanta ɗaya tana ƙoƙarin cire mata rigar barci ɗayan kuma tana yi mata kiss a fuska, sai yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa ya saki salati da ƙarfi tare da.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Ya cigaba da maimaitawa sai ya juya da sauri ya bar ɗakin, zaman dirshen yayi a tiles daga gefen kofan ya shiga rusa kuka kamar an yi masa mutuwa, daga bisani ya miƙe da kyar ya koma cushing ya zauna kansa sai sara masa yake yi ga numfashinsa da yake yin wani irin fita cikin huci. Su Binafa duk da kusan tarkonsu ya kama kurciya sai da suka tsorata dan sun gane mai gidan ne, kuma basu ji daɗin dawowarsa yanzu ba dan sun so sai sun samu biyan buƙatar su akan ta.
Beb plan ɗinmu ya faɗa amma bamu samu biyan buƙata ba, gashi ko kaya bamu cire ba balle ya yi zargin ta sosai.
Cewar Binafa kamar zata fasa ihu, Hanan bata ce komai ba ta sauko jikinta yana rawa ta ɗauki hijab ɗinta ta saka, Binafa itama ta saka Hibab suka fito falo nan suka ganshi zaune ya dafe kuncinsa da hannu biyu yana hawaye. Koda yaji fitowarsu bai ce musu komai ba sumsum suka wuce dakin Jamila suka ɗauki tarkacensu suka fito, Jamila tana biyosu a baya, ganin Aminu yasa taja wani mugun burki ta koma da baya ta shige ɗaki ta saka key ta rufe ta shiga tsananin tashin hankali da tsoro ganin asirinsu ya tonu tunda ya dawo ya gansu, bata san cewar su a cikin tsarinsu hakan dama suke so ba, ta zauna a tile dirshen ta soma kuka tana ta shiga uku asirin ta ya tonu. Su Binafa har sai da suka kawo ƙofar fita suna tunanin zai dakatar dasu amma sai suka ga bai ce musu komai ba sai suka fice. Suna fita cikin zafin nama ya miƙe ya banko ƙofar ɗakin Sameeha ya sameta shurum a kwance kamar yadda suka barta, duk da rigar barcinta yana jikinta babu wani alamun sun taɓata, hawaye kawai take zubawa domin ta gama sanin makirci aka haɗa mata, damuwarta me ya dawo da Aminu a yanzu? Sannan duk abinda zata faɗa masa ba zai taɓa yarda ba. Aminu zaman dirshen yayi a ƙasa jikin ƙofa dan yadda ya ganta ya ƙara kashe masa jiki, sai ya soma cewa cikin kuka.
Sameeha sai da nace miki ki bari na sauwaƙe miki kije ki yi aurenki dan nasan ba lallai ki jure ba, kika ce zaki jure gashi yanzu na zo na kamaku kuna kokarin aikata mummunar ɓarna, nasan nima ina da laifi da tun farko na haƙura da ke da hakan ba zai same ki ba. Kin yi mini halacci kin jure na tsawon shekara shida ban kusance ki ba. Yanzu ne na tabbatar da dalilinki na ƙin bina Abuja, zan shedeki cewar da muna Lagos ba kya aikata komai nan ɗin ma baki daɗe da faɗawa wannan halakar ba ƙila, tun kafin lamarin yayi nisa ki kasa auren namiji gwara na sake ki akan ki faɗa tarko lesbian, dan mugun abune mai wuyar wahalar warkewa, mummunan fasadi ne da Allah ya halakar da mutanen Annabi Luɗ a.s. Batun yara Allah zai raya mana su zan kula da tarbiyyansu, dan ya zama dole mu rabu domin matsalata ba tada magani kullun cikin nima nake amma har yau ban dace ba.
Da matsanancin kuka ya ƙare maganar yana shassheƙa, itama Sameeha kukan take mai tsanani dan baƙin ciki, tama kasa magana gashi jikinta yayi nauyi ba zata iya tasowa ta matso kusa da shi ba, Aminu ya cigaba da cewa.
Rabuwarmu shine kawai mafitarki Sameeha, bana fatan ranar tashin ƙiyama ki tashi cikin mutanen da Allah zai hukunta, ina fatan duk mu kasance a aljanna, a dalilina bazan bari rayuwarki ta salwanta ba bazan bari ki wulaƙanta ba, zan sadaukar da soyayyarki domin kuɓutar da ke daga halaka, ina sonki Sameeha amma dole zan haƙura domin na fitar dake daga cikin gargada da zullumi. Wannan maganar ta zama sirri bazan taɓa faɗawa wani wai akan dalilin na kamaki kina lesbian ba, domin ni nasan ba halinki bane, zan sake ki ne akan dalilin kuɓutar dake daga faɗawa halaka tunda har kin fara kawo mata gidan nan, nan gaba ina tsoron ki faɗa zina duk da ina da kyakkyawar yaƙini akanki.
Dan Allah! dan Allah Aminu karka sake ni wlh ba abinda kake zargi bane shirya mini aka yi.
Ta faÉ—a cikin matsanancin kuma muryanta cikin sanyi da kuma sautin maye.
Sameeha har abin maye kike sha? Waye ya sauya min ke kika zama haka, ashe In bana nan ɓarna kike yi ban sani ba.? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Ya ƙara fashewa da kuka, wannan karan jikinsa har rawa yake yi duk ya fita hayyacinta, ya cigaba da magana cikin matsanancin kuka.
Abin da ciwo Sameeha, na sakeki Sameeha, na datse igiyar aurenmu guda uku wannan shine kawai adalcin da zan iya yi miki, idan ba haka ba nan gaba za a samu matsalar daga ni har ke mu shiga wuta, zanyi nesa dake ta yadda ba zaki sake ganina ba nima bazan ƙara ganinki ba. Nasan muna yiwa juna wani irin so, amma lokaci yayi da dole haƙuri shine zai zame mana magani. Rabuwar mu da ciwo amma a hankali zamu saba.
Sameeha wani ƙara ta saki da bata san sanda ta ari jarumta ba ta mulmulo ta faɗo ƙasa tim tana kokarin jan jikinta zuwa gare shi, amma Aminu ya miƙe da sauri yana wani irin kuka mai gunji, jijiyoyin kansa har sai da suka bayyana ɓaro ɓaro, jikinsa kuwa rawa yake yi ga wani sanyi daya ji yana shigarsa, nan take zazzaɓi ya kama shi ya wuce ɗakinsa da sauri ya rufe ƙofa ya faɗa doguwar kujera ya kankame jikinsa yana ci gaba da kuka. Sameeha ihu ta shiga yi tana faɗin ta shiga uku tare da cewa.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Shikenan sunyi nasarar rabani da kai Aminu, Wlh ba abinda kake zargi bane ban taɓa aika mummunar abu ba ina kokarin riƙe maka mutunci na, na yarda da cewar ko wace cuta da maganinta, wanda hakan yasa na keɓe sha'awa ga komai, domin nasan watarana zaka warke. Hauwa me nayi muku haka da zafi? dama kince ba zaki taɓa sona ba kin tsaneni. Na shiga uku naaaa.
Ta ƙare maganar tana cigaba da kuka sannan tana kwance a ƙasa, wanda a lokacin ma ta saki fitsari dan ba zata iya kai kanta bayi ba, jikinta rawa yake sosai ga wani zazzafan zazzaɓi ɗaya rufeta, kuka take mai gunji da ihu tana kwalawa Aminu kira.
_Masoyana... Masu maganar dan Allah kar auren Sameeha ya mutu, kar ku manta ko wani aure rai ne da shi idan har hakan yana cikin ƙaddarar mace duk yadda takai ga takacancan sai ya rabu ko kuma mutuwa ta raba. Sannan Sameeha tayi sakaci da abu uku na farko Addu'a, na biyu tayi saurin sakewa da su Hauwa ga yadda suka nuna mata kiyayya ƙiri ƙiri, duk wanda yace baya sonka to wlh in ya dawo yana sonka akwai dalili, maƙiyinki duk yadda kaso burgeshi wlh in dai yace saiya ga bayanta to ba zai taɓa kyaleka ba koda kullun zai faɗi ba zai fasa ba. Sannan abu na uku ta yi saurin yarda da Jamila har take bata aikin girki ta saka mata hannu, wanda tana da tabbacin agent ɗin su Hauwa ce. So tari makashinka yana tare da kai. Kuyi haƙuri haka labarin yazo na tabbatar muku akwai happy ending In Sha Allah._
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
19.
Sameeha ganin ba sarki sai Allah yasa ta fara ambaton istigafari da salatin Annabi s.a.w hawaye yana bin kuncinta, ta ɗauki kusan minti talatin a haka kafin ta iya ƙarfin hali taja jikinta zuwa bayi sai ta buɗe ta rarrafa ta isa ciki ta haɗawa kanta ruwan wanka ta shiga cikin baho, a hankali ta zame rigar jikinta ta gyara zama tare da yin lamo a cikin ruwan, sai barci ya fara fusgarta tare da jin zafin ruwan yana ratsata, ta ɗauki kusan minti ashirin a cikin ruwan dan har saida ya fara rage zafi, tana ƙoƙarin fitowa taji sallamar Hauwa ta shigo ɗakinta, dam dam taji ƙirjinta ya buga tana jan salati a zuciyarta, sai ta koma cikin ruwan tayi lamo dan bata san me zata yi ba a wannan lokacin ga jikinta sam ba ƙarfi.
Su Binafa suna fita suka kira Najwa suka sanar da ita komai, cikin tsananin farin ciki ta shiga zuba musu godiya tace zata zo gobe su haÉ—u dan suyi murna a tare, bayan sunyi sallama sai ta kira Jamila har wayan ta tsinke bata É—auka ba a kira na biyu ne Jamila ta rarrafa ta É—auki wayar dake kan gado ta É—auka tana sasshekar kuka tare da cewa.
Alhaji ya dawo asirinmu ya toni shikenan kin ja mini matsala na shiga uku.