Sashe 57
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyaɗa kai Najwa tayi saboda zafin da zuciyarta ke yi mata ba zata iya magana ba, Nafeesa ta ɗauko mata buta dake bakin famfo ta kawo ta wanke fuskarta kana ta goge da gefen mayafin data yafa, dan musamman ta saya mayafin da zata ci biki duk da ba sakawa take yi ba, amma ganin bikin nasu ne kuma na masu kuɗi dole ta koyi shigarsu kamar yadda Nafeesa ta bata shawara, sai ta miƙe tana dafe bango Nafeesa ta gyara mazaunin gyalenta tana cewa zata ɗauko jakukunansu ta dawo, to Najwa tace kana ta cigaba da tsayuwa har Nafisa ta dawo ta kama hannunta suka fita, da yake gidan ya cika da mutane babu wanda ya kula da su har suka fita. Abin hawa Nafeesa ta samar musu suka wuce gidansu Najwa. Koda suka isa sun samu ba kowa a gidan dan ɗakunan a rufe suke ƙofar gidan ne yake a buɗe an jawo shi, Nafeesa ta ɗauki keyn ɗakin Najwa a jakarta ta buɗe ɗakinta suka shiga, Najwa ta faɗa gado dan sosai take jin jikinta ba ƙarfi tama buƙatar hutawa, ga tarin baƙin ciki goma da ashirin saboda tasan ta yiwa kanta mugunta, duk da Shamsu shi ya ɓoye mata asalinsa, amma da bata sanya son zuciya ba a lamarinta da yanzu shine mijinta, ko banza zata yi gogayya da Sameeha, Nafeesa ta fita can waje ta sayo musu ruwan sanyi a wani shago ta dawo ta bawa Najwa ta amsa ba musu ta tashi ta zauna tasha, sai dai ta aje leda dan duka ta shanye ta kalli Nafeesa tana cewa cikin rauni.
Yanzu miye abinyi Nafeesa, Abun da ciwo inna tuna nice na yiwa kaina, na ɓata goma biyar bata gyaru ba, ina jin ƙunci a zuciyata kamar na hada Sameeha da Ikram na cinna musu wuta su mutu kowa ya huta, gabaɗaya sune suka tare mini hanyar cigaba na.
Najwa sunyi miki fincinkau kima aje batunsu a gefe ki fuskanci gaba, dan yanzu ba ki da yadda zaki ki ja dasu, Aminun dai da kika samu ki kama shi hannu biyu dan shima ma ba baya ba da arzikinsa, kuma gabaɗaya yafi mazajen su Ikram kyau kuɗi kawai zasu nuna masa, kinga kina da miji na shiga taro wanda zaki kece raini, zan iya cewa duk ƙawayenmu babu wacce take da saurayi kamar naki, ko ba komai kina da tudun dafawa, kin fini ni da ba ni da kowa yanzu tunda na rabu da Hamis.
Nafeesa ta kai aya a maganarta tana kallon Najwa wacce ta zuba uban tagumi, sauke numfashi tayi domin duk maganar Nafeesa gaskiya ce kuma ta gamsu sosai wanda yasa tace.
Shikenan zan haƙura da komai na kama Aminu hannu biyu, amma bazan iya ƙarasa wannan bikin ba dan kar zuciyata ta buga. Bayan biki zanje naga ɗakunansu daga nan kuma munyi hannu riga.
Ina wlh baki isa ba ai dole ki ɗaure a ƙarasa dake kiga yadda aka tsara gidajensu kema kisa a tsara naki haka.
Bazan iya cigaba da bin lamarinsu ba dan ban'bu abinda zai haifar mini illa ciwon zuciya, ki rabu dani kawai Nafeesa na fuskanci gaskiya, na yarda sun fini kuma ba zan ƙara ja da haka ba zan yi daidai rayuwar da Allah ya zaɓar mini, damuwata duk randa Aminu ya san ni ya aura bansan ya zamu kwashe ba.
Najwa ko zamu koma gurin malamin nan da Binafa ta kaimu sai ayi miki aiki akansa koda ya ganki ya kasa rabuwa dake.
Bazan je ba domin wancen aikin dana bashi bana tunanin yayi, har takalmin Sameeha na kai masa sai gashi ta auri mijin daya fi na baya.
To ai ba akan haka kika saka yayi miki aiki ba, akan Aminu kika ce ayi aikin kuma baga shi kin samu nasara ba tunda yana kulaki kuna hira har kyautuka yake yi miki, ki zauna kiyi tunani dan wlh ina jiye miki ɓacin rana, duk da kince Hauwa zata yi miki aiki akai kema ya kamata ki yiwa kanki tanadi.
Kin san tunanin daya faÉ—o mini yanzu?
Najwa ta faÉ—a tana É—an murmushi, Nafeesa tace.
Sai kin faÉ—a.
Nafeesa babu abinda zanyi, idan ma yana ganina ya sake ni bazan damu ba domin yanzu Shamsu ne a tunanina, na ɗana arzikin gidan Aminu to ina da buƙatar ɗana gidan Sarauta, Shamsu ni ya fara so a rashina ne ya auri Ikram, na tabbatar in ya ƙara samun dama ta biyu a guna zai saurare ni.
Wani irin kallo Nafeesa takewa Najwa wanda yake ƙunshe da tarin magana, Najwa ta muskuta tana cewa.
Yadda na samu galaba akan raba Sameeha da Amunu ba tare da tayi mini komai ba, to tabbas sai na shaga tsakanin Shamsu sa Ikram tunda ta yi kokarin shiga gonata, domin ni ya fara so ta zo ta aureshi.
Taya zaki hukuntata da abinda bata sani ba? na tabbatar bata san saurayinki bane shi, Najwa ki tsaida tunanin ki guri É—aya ki tsaya a auren Aminu kawai.
Nafeesa ko bazan auri Shamsu ba wlh sai na saka Ikram ta shiga ƙunci, idan banyi haka ba bazan samu sassauci a zuciyata ba.
Kallonta kawai Nafeesa take yi dan ta kasa cewa komai saboda tsantsar mamakin Najwa, ta kula ba hassada kaɗai ke damunta dasu Sameeha ba har da mugunta da keta, ganin wanda yayi nisa baya jin kira yasa ta miƙe tana cewa.
Ni zan koma gidanmu tunda kin ce ba zakin koma gidan bikin ba, sai bayan kwana biyu.
Allah ya kaimu sai ta kwanta dan bata jin zata iya yi mata rakiya, Nafeesa ta fice tana mamakin Najwa da irin mugun tunaninta, ta rasa me su Sameeha suka yi mata da suka cancanci wannan ƙiyayya, gashi basu san tana yi ba kuma su sai nasara suke samu, a wannan karan ji tayi bata fata Najwa ta samu nasara akan abinda tace zata yiwa Ikram, tace a cikin ranta.
Nima zan bi sahunki ya saka takalmi irin naki na yi miki cindunduniya kamar yadda kika yiwa wasu, nima na rama musu, dan Ins' Sha Allah nima sai na auri Aminu.
Tayi maganar tana murmushi ta wuce zuwa bakin titi ta samu napep ta wuce gida.
******
Can gidan biki an cigaba da shagali kowa yanata hada hada ga ɗaukar hotuna da ake ta yi, amare suna shiga suna sauyawa gwanin sha'awa har zuwa bayan sallar la'asar, lokacin ne su Salma suka yiwa Sameeha sallama akan zasu wuce amma Hauwa da Laure sunce zasu je kai amarya ba dan komai ba sai dan su samu damar tariwo gulma yadda zasu ji daɗin bada labari, suga kuma irin daular da Sameeha ta samu, Sa'a dai tabi Salma da Adama dan tasan halin mijinta Kamalu bayi da sauki. Sameeha har cikin zuciyarta taji daɗin yadda su Hauwa suka muna mata kara duk da tasan da biyu zasu je kaita amma tasan sai dai su ga abinda zai damesu dan na gaba yayi gaba. Ikram tana zaune da ƙawayenta a ɗakin kusa dana Zaidu ta idar da salla suna hira, sai taji saƙo ya shigo wayarta, tana dubawa taga baƙuwar Number ta shiga wajen massage ta soma karanta saƙon kamar haka.
Amarya bakya laifi, ina taya ki murnan Auren Shamsu sai dai ba nan gizo ke saƙa ba domin kuwa ina ɗauke da cikinsa na wata biyar daya ƙunsa mini ya gudu ya barni, a gunku mutumin kirki ne shi amma tantirin mazinaci ne na nunawa sa'a, idan kuma baki yarda ba ni ina da hujja, kisha amarci lafiya tare da baban ɗan shege ko shegiya.
Wani irin gumi ne ya shiga karyowa Ikram innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, da kyar tayi yaƙi da zuciyarta ta aro jarumta ta miƙe da sauri, wata ƙawarta tana cewa.
Lafiya Ikram waye yayi miki saƙo? ko Aliyu ne ya tono miki da tsohuwar soyayya.
Yaƙe tayi mata kawai tace eh, sai ta fice daga ɗakin saye da hijab ɗin data idar da sallah sai jakarta a hannu, ɗakin umma ta wuce ta shiga can uwar ɗakan da Sameeha ke zaune da Khairy da wata ƙawarta sai ɗiyan Inna Rukayya, Tana zuwa ta kama hannun Sameeha ta ce.
Anty zo mu je ki gani.
Ikram ki barni na huta ina fama da gajiya.
Dan Allah ki zo mu je.
Yadda Ikram tayi maganar kamar zata yi kuka yasa Sameeha miƙewa tabi bayanta, har tsakar gida suka fice zuwa ɗakin yaya Zaidu, Ikram ta ciro key a cikin ƙaramar jakarta ta buɗe bakin kana suka shiga ta rufo ƙofa, ta miƙawa Sameeha wayarta tana cewa.
Kinga saƙon da aka turo mini yanzu da wata number.
Sameeha ta amsa ta shiga karantawa ko ɗar bata ji ba a ranta dan wlh tasan sharri ne, a yadda Khairy take faɗar Shamsu ba zai taɓa aikata haka ba, ta duba Ikram tana cewa.
Ki kwantar da hankalinki wannan ba komai bane face sharrin maƙiya, zan bincika komai In Sha Allah gaskiya zata yi halinta. Yanzu ki saki ranki kar a gane kina cikin damuwa kisa a ranki dukkan nasara yana tare da ƙalubale.
Humm tace kana suka fita daga ɗakin Sameeha tana riƙe da wayar Ikram bata mayar mata ba, ta koma ɗakin umma Ikram kuma ta koma ɗakin da take tare da ƙawayenta. Sameeha bata sanar da kowa ba ta adana wayar Ikram a hannunta sai ta cigaba da hidimar ta.