← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 98

Sashe 1

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ABIN DA CIWO*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 1.

*Gargad'i*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

Sameeha tana cikin wani irin farin ciki mai matukar girma gaya, kullun cikin ɗoki da kosawa take yi akan komawa mahaifatarsu da zasu yi gabaɗaya ita da iyalinta, tunda Abban Amrah ya sanar da ita ya samu transfer na aikinsa zuwa Abuja kuma an kammala ginin gidansu da yake kaduna an saka komai sai tarewa, hakan yasa ta fara shiri tana haɗa kaya tun kafin ya saka ranar da zasu bar garin lagos, tayi alkawari ba zata sake zama a wani gari ba sai kaduna kusa da 'yan uwanta, kasantuwar Abuja ne ya koma yasa ta samu natsuwar ruhi ganin in mutum yaso a ranar zai iya zuwa kaduna daga abuja ya koma, ta san ganin Abban Amrah ba zai yi mata wahala ba shiyasa ta sanar da shi kaduna zata zauna in yaso duk karshen mako yazo ya gansu, kuma ya amince da haka saboda yana matukar son farin cikinta tunda itama tana iya kokarin ta wajen faranta masa. Dole ma Sameeha tayi doki domin sun shafe shekara biyu da watanni rabonsu da kaduna tana cikin tsantsar kewar ahalinta, kuma tsawon shekara goma kenan da suka yi a lagos sakamakon aiki da ya kai Aminu mijinta tare da kasuwanci da yake taɓawa, amma duk da daɗewarsu a nan bai sa ta saba da zaman garin ba kuma a nan duk ta haifi yaranta, ɗanta na farko Adamu ya ci sunan mahaifin babansa suna kiransa da Abi, shekarunsa tara sai Amratu da take da shekara shida bata sake samun wani haihuwar ba, suna dai fatan samun kari nan gaba duk da tsawon shekaru shida da suka ɗauka rabonsu da samun wani karuwa. Kullun burin Sameeha bai wuce ta wayi gari ace sun bar lagos sun koma kaduna ba, saboda kowa nata yana can haka shima mijinta Aminu duk danginsa suna can, banda aure wajibine wani sa'ilin ji take kamar ta barshi ta dawo kusa da ahalinta, musamman in aka ce ana taron biki bata samu zuwa ba ji take kamar tayi tsuntsuwa ta buɗe ido ta ganta a kaduna, ita dai macece mai mugun son 'yan uwanta daga dangin uwa har na uba, tana kokarin bautawa zumunci sosai dan in akace abu ya taso ko bata zo ba zata yi aiken kuɗi. Mijinta Aminu yana iya kokarinsa gurin kyautata mata bata rasa komai ba na jin daɗi ba domin za a iya cewa tana ɗaya daga cikin mata masu gata a gidan aurensu, dan kuwa tayi dace da miji nagari na nunawa sa'a, rayuwarsu tamkar su suka samu takarsa da biro suka tsara yadda suke so ta kasance, duk da mutum tara yake bai cika goma ba kuma duk faɗin jin dad6in akwai kaddara da ka iya faɗawa bawa ko ya zama silar samuwar aljanna ko kuma mutum ya faɗa tarkon dana sani. A lissafin Sameeha kwanaki sun shuɗe har lokacin barinsu Lagos yayi saboda gobe In Sha Allah zasu hau jirgin rana ya sauke su a garin Kaduna garin gomna, kira ne ya shigo wayarta ta ɗauka da sauri ganin mahaifatarta ce ke kirata.

Assalamu Alaikim Ummaaa.

Ta faÉ—a cikin fara'a da farin ciki, sai da umma ta saki murmushi kafin tace.

Na'am É—iyar umma ya shirye shirye dan na san ba zaki bar kanki ba sai kin ganki a kaduna.

Hmmm umma ɗoki nake duk na ƙosa na ganku, da fatan su Yaya Zaidu dasu Anwar sun je sun kakkaɓe mana kurar gidanmu.

Ai ko sunje sai dai sun tadda Hauwa da matar wan mijinki Laure a gidan, suka ce su dawo sun gama gyaran ko ina.

Amma ya aka yi key yaje hannunsu ni Abban Amra bai faÉ—a mini zasu je yin wani gyaran gida ba, ni bana son irin wannan shisshigin.

Haba Sameeha ina laifin anyi miki hidima, to karki yarda ki fara halin da zasu tsaneki, ina ruwanki in sunje ina ce 'yan uwan mijinki ne, idan ma sunyi abinda ba haka ba sun fi kusa da shi, ni bana son ki fara korafi da su.

Amma umma wlh gulma ce yasa suka je gidan na tabbatar Hauwa ta kitsa komai ta amsa key gidan a hannun Yaya Alhasan.

Koma dai miyi bana son ki jawa kanki damuwar dangin Aminu ki zauna da kowa lafiya dan yanzu ne ya kamata ki kwantar da kai ki gane halinsu dan ki san yadda zaki zauna da su.

Hakane Allah yasa mu dace. Idan mun shigo In Sha Allah zan zo dan a nan gunki zan kwana muyi hirar yaushe gamo.

To É—iyar umma Allah ya kaimu goben ya kawoku lafiya.

Ta amsa da Amin kana suka yi sallama Sameeha ta aje wayar tana mamakin wai Hauwa da Laure sun je gidansu sun yi musu gyara, mutanen da sam basa kaunar cigabanta ƙiri ƙiri Laure take nuna mata tsana saboda taki yarda taja ragamar gidanta, dan a yadda ta lissafa taso ace Sameeha ta mayar da ita abokiyar shawararta, domin ta rika sanin duk abinda ke wakana a tsakaninta da mijinta da kuma irin rufin asirin da suke ciki, amma Sameeha ta nuna mata kar take kallonta ta ki bada kofa balle fuskar da zata yi mata kutse a zaman gidan mijinta, wannan yasa ta tsaneta ta kasa danne hassadarta akan rayuwar walwala da suke ciki domin kaf danginsu Aminu yafi rufin asiri yana da kadarori da kuma aikin da yake yana samu kudi sosai, dan duk wani hidima in ya taso shine mutum na farko da ake fara faɗawa ansan zai yi da karfin guiminsa ba tare da ƙorafi ko gori ba, in ya bayar to baya so ma a ambaci sunansa, yana matukar kaunar 'yan uwansa da son hidimta musu, itama Sameeha tana kara masa kwarin guiwa sosai akan abinda yake yi bata taɓa hanashi yin alkhairi ba tunda itama yana yiwa yan uwanta hidima, bata san wahalar sana'a ba domin duk abinda ya taso nata yana yi mata, duk wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya kawo mata bakin jini a gurin Laure da kuma 'yar korarta Hauwa ganin Aminu ya tare akanta da 'ya'yanta, banda surutu da suke yi akanta wai ba ta son shiga cikinsu ta ware kanta, tare da kai sukarta da gulmarta a gurin Aminu, har cewa suke in ta koma Kaduna Allah yasa ta riƙa bari ana zuwa mata gida dan sam bata son shiga cikinsu, Aminu sai dai ya toshe kunnensa tare da basu hakuri dan yasan matarsa tana da kirki ba tada wani abun da za a kushe tana da son mutane dan tasha bashi sako in zai je kaduna akan ya kai musu, amma basa gani kullun sai binta da sharri suke yi, wani labarin ma a bakin Sa'a matar yaya Kamalu take ji saboda ita bakin ganga gareta, tana tare da su kuma tana tare da Sameeha, abinda ta guntsa na gulma a gunsu sai ta kira Sameeha ta fesa masa, haka kuma in ta bigi ruwan cikinta ta kwashe ta faɗa musu, a hankali sai magana ya rika dawo mata tasan kuma da Sa'a kaɗai tayi zancen, tunda Sameeha ta farga ta ganeta sai ta iya takunta da ita dan ta kame bakinta duk labarin da ta ɗauko nasu ta faɗa mata to bata faɗar wata magana da zai zame mata kilu ta ja bau, sannan bata yarda ta bata nata labarin sai um da um um hakan yasa itama Sa'a ta rage shige mata. Ta tabbatar da komawarta kaduna sune mutane na farko data san zasu kawo mata tasgaro da farin cikinta, dan sosai Laure ta mayar da ita kishin saure kuma ance yafi asalin zama da kishiya zafi, ga kuma Hauwa da take yayar Aminu dan ita ce ke binsa ta fiye nuna mata isa da son girman tsiya, dole ita sai ta nuna gadara da iko akan Aminu sai dai yadda ta gode Allah Aminun shima ba baya ba, sam baya yarda da duk abinda tazo masa da shi matawar zata yi kutse a cikin rayuwarsa ta takura masa, ta tabbatar da zuwa gidan da suka yi a matsayin gyaran gida ba alkhairi ya kaisu ba, wani munafurcin ya kaisu wanda Allah kaɗai ya sanshi, amma tunawa da tayi anyi musu saukar Alqur'ani da sadakar abinci a satin daya gabata wanda ɗan uwanta Zaidu ne ya jagoranci komai, saboda shima akwai key da ya amsa na gidan a hannun yaya Alhasan, sai ta sauke ajiyar zuciya tana cewa a fili.

Allah ya sa alkhairi a komawarmu Kaduna, ka kauda idon munafukai da makiya akanmu.

Amin Mamanmu.

Amra tace tana karasa shigowa É—akin ta zauna kusa da ita tana cigaba da cewa.

Mama ai babanmu zai sauya mana makaranta mai kyau a can ko, kuma wanda anty ba zata riƙa dukanmu ba ko.

Sosai kuwa har ya sama muku ma da mun koma zai je yayi muku register, makaranta ce mai haɗe da boko da islamiya. Sannan batun anty in baki yi laifi ba taya zata riƙa dukanki haka kurum, ni dai ina so ki zama daliba mai ilimi da kwazo da kuma jin magana. Allah dai ya kaimu gobe lafiya dan iyanzu haka muna cikin gidan Umma In Sha Allah.
Chapter 1 · 0% Book details