Sashe 23
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ok Allah ya kiyaye hanya sai dai ki dawo da wuri dan nima fita zanyi wata ƙila sai yamma.
To tace mata kafin ta miƙe ta wuce zuwa ɗakinta. Sameeha wajen ƙarfe tara da rabi ta bar gidan ta rufe duk ɗakunansu ta bar kitchen a buɗe saboda tace Jamila in ta dawo ta gyara mata kayan miya ta niƙa ta dafa shi saboda ya soma lalacewa kar suyi asara, kafin ta wuce gidansu a motarta ta kwashi yara da kayansu daga nan zata biya gurin telanta, Tana fita ba daɗewa Jamila ta bugawa Najwa flashing sai gashi ta kirata nan take.
Kin fito ne Jamila?
A'a ki zo gida anty Sameeha ta fita kuma sai yamma zata dawo.
Ok tace tana kashe waya, Jamila ta koma ta kwanta dan dama ta faɗawa Sameeha zata fita ne saboda haɗuwa da Najwa amma data ji itama fita zata yi sai ta fasa, karin takaicin ta tace zata fita amma ko na mota bata ce mata gashi ba, tunda tazo gidan wani kuɗi bai taɓa haɗasu ba a matsayin kyauta sai dai albashinta kawai take bata, sosai take ganin rowar Sameeha dan a ganinta yaci ace zuwa yanzu ma ta ƙara mata albashi, ga yadda take bautar da ita da aiki kamar jaka, sauƙin ta ma abinci tana ci tana koshi sai kuma in bata nan ta zabgi nama taci mai mata, kuma bata taɓa yi mata magana ba ƙila bata ganewa ana ɗiba naman ne. Bayan kamar minti talatin da shida sai ga Najwa tazo gidan, ta yi nocking da sauri Jamila ta fito ta buɗe mata ƙofa dan ta rufe ta ciki, suka ƙarasa suka zauna tare da gaisawa, Najwa ta dafa kafaɗar Jamila da yake kujera ɗaya suka zauna tace.
Jamila wani aiki ne Yaya Hauwa ta sakani sai dai ni zaiyi wuya na iya aikata shi saboda ni ba a gidan nan nake zama ba, kuma ita ta saka nayi ne ganin Sameeha yar uwata ce nafi kusa da ita, amma kuma dawowata gidan nan zai mini wahala saboda ina zuwa makaranta can malali, to ganin tace biyana zata yi nace mata zanyi mata aikin, amma sai daga baya na yanke shawarar bari na baki aikin kema ki samu naki rabon, sai dai ina so ya zama sirri a tsakaninmu domin maganar nan daga ni sai yaya Hauwa muka yita, sai ke yanzu da zan faÉ—a miki kar ki sake ki bari tasan ke na bawa aikin, dan Wlh zaki jawa aikinki nima ki ja mini.
Anty Najwa wannan wani irin aikine haka?
Ba mai wuya bane amma ana buƙatar kiyi takatsantsan kuma ki riƙe sirri. Wannan magani ne da Anty Hauwa ta karɓo gurin wani malaminta akan a riƙa zubawa Sameeha a abinci domin ya fara aiki a jikinta kafin Aminu ya dawo dan ayi farraku a tsakaninsu. Saboda babban burinta ta bar gidan ni in maye gurbin Sameeha, kinga kema inna samu damar auren mai gidan aikinki ya tabbata a gidan nan kuma albashinki dubu ashirin duk wata.
Tana kaiwa nan taja fasali, Jamila ta saki wani murmushin jin daɗi taji batun kuɗi, tace cikin zaƙuwa.
Wlh da ba ƙaramin murna zanyi ba in kika zamo matar gidan nan, kuma gwara a setawa Anty hanya dan ba tada kirki ko kaɗan, hakuri kawai nake yi da ita, ashe kema Hajiya Hauwa ta sanar dake yadda take son raba aurensu, nima dalilin daya saka kenan ta ɗaukeni aiki, sai dai kuma bana samun labaran da zan faɗa mata wlh, saboda anty bata yin komai a gabana.
Ta ƙare maganar tana taɓe baki, Najwa tayi murmushi.
Yaushe munafukar zata bari kiji bayan tana zarginki akan zaki kwashe ki faɗa musu tunda su suka kawo ki aiki, yanzu dai ga maganin nan ki ɓoye ki riƙa saka mata a cikin juice zaifi aiki da kyau. Kuma wlh in kika bari na kamaki karki ambaci sunana ko Hauwa dan wlh saurayina soja yana nan, kina kuskure zan aiko a kamaki ya kashe ki a banza.
Jamila ta zaro ido waje cike da tsoro.
Haba Wlh bazan taɓa bari ta kamani ba, ai tana yawan sakani na miƙa mata kankana ko abarba su tafi so, kinga zan riƙa saka mata in ban samu dama ba, to ko a cikin abinci na barbaɗa.
Yauwa haka za kiyi, ga dubu goma idan kin gama aiki da kyau zan cikasa miki dubu gomanki.
Jiki yana rawa Jamila ta amsa kuɗin ta shiga ƙirgawa ta samu ya cika cif.
Nagode Anty Allah ya ƙara arziki yasa ki auri Alhaji.
Ameen. Yanzu zan riƙa kiranki a waya kina faɗa mini abinda ke faruwa da kuma faɗa mini tabbacin ranar da Alhajin zai dawo.
Eh É—azun naji suna waya yace nan da sati biyu zai dawo.
Yauwa ki riƙa saka kunne musan yaushe ne ranar da zai dawo, amma da yaushe yafi dawowa?
Da safe yafi shigowa.
To shikenan zan tafi sai munyi waya.
Najwa tace tana miƙewa, Jamila ma ta miƙe tana koro mata godiya dan ba ƙaramin daɗin kuɗin taji ba saboda tana hada so ta fara kuɗin ne in ta tashi aure ta siya kayan 'yan birni masu kyau, Najwa ta tafi Jamila ta juyo ta koma ɗakinta tana hango yadda zata fara saka mata maganin, dan kuwa tana ɗan sakata aikin kitchen ɓangaren abinci haka, da farko ne taki yarda da ita amma daga baya ta saki komai, ko dan taga bata kamata da wani a bun munafurci bane shiyasa ta saki, kuma gashi ta koma tana shiri da su Hauwa.
Najwa tana cikin napep ta kira Binafa ta faɗa mata yadda tayi da Jamila, da yake sunyi musayar numbern waya, Binafa tace ba damuwa ta saka kunne sosai susan ranar dawowar Aminu, sannan ta tura mata addreshin gidan zasu fara kai ziyara amma sai in Sameeha bata nan, ta yadda mai gadi zai shaida fuskarsu itama Jamila yar aiki ta gane suna zuwan gidan a wannan lokacin akai akai, amma sai in tana binciko musu Sameehar bata nan kafin suje, yin hakan duk taku ne da kwantan ɓauna. Najwa ta yi dariya tana ƙara yi mata godiya a haka suka rabu, nan take ta tura mata adireshin gidan da bayanin komai yadda zasu gane.
Sameeha bata dawo ba sai bayan sallar magrib, ta zauna a cushing tana kiran jamila, data fito tayi mata sannu da zuwa tace ciki gajiya.
Jeki markaɗa mini sauran gwandan nan ki zuba madara ki niƙa karki saka min ruwa, sai ki kawomin shi da kauri shi nake jin sha, sannan ki kawo plate guda biyu zan zuba miki abinci na tawo dashi daga gidanmu.
To tace mata sai ta wuce zuwa kitchen, dama a kitchen ɗin ta adana maganin inda tasan babu wanda ya isa ya gani, ta ɗauko shi ta maƙale a cikin rigarta ta soma aikin data sakata, a cikin nikan ta barbaɗa maganin ta mayar da shi ma'ajiyarsa tazo ta haɗa komai, data gama ta kawo mata tare da plate data ce ta kawo, Sameeha ta saka mata tuwon shinkafa miyar zogale da nama ta bata ta wuce tana godiya, itama ta saka nata amma sai da ta shanye smoothy ɗin kafin ta fara cin abinci, data gama ta shiga ɗaki ta yi wanka tayi shirin barci ta kwanta dan tana fashin sallah kuma akwai gajiya a tare da ita saboda aiki sosai ta yiwa Umma dan tayi mata kwalemar dakinta.
Da safe data tashi jin kanta tayi cikin wani irin yanayi na feeling, abin har mamaki yake bata dan rabon da ta ji haka ta manta tunda ta dena shan maganin mata saboda miji baya kusa saboda ta samawa kanta lafiya, rabon ma data sha wani magani ta mance lokacin dan an jima, kayan fruit kawai take sha suma badan su ƙara mata komai ba sai dan jikinta ya yi kyau, kuma sosai suke nunawa a jikinta dan tayi fresh sosai gwanin burgewa, sai ta bayar ƙila smoothy ɗin gwanda data Sha jiya shine ya taso mata da sha'awa tunda akwai madara a ciki, wankan tsarki tayi dan ranar ne ta gama al'ada sai ta shirya tayi salla kana ta fito ta haɗa masu abin kayi, tana gama karyawa ta fice saboda sunyi da telanta zata je da wuri ta amso kayanta, daga can kuma zata je babban gida kan batun cincin ɗin amarya da za ayi, saboda Hauwa ta kirata akan tazo ayi shawarar yadda zata kasance.
***
Binafa.
A safiyar Binafa ta kira Najwa akan zasu je gidan Sameeha amma ta kira ta tambaya ko tana nan, suna gama waya nan take ta kira Jamila ta tambayeta sai take faɗa mata bata nan sai ta kashe waya, Najwa ta sake kiran Binafa ta faɗa mata, tace yanzu zasu je gidan da ƙawarta Hanan dan su fara aikinsu. Binafa a motarta ta fita ta biya gidansu Hanan ta ɗauke ta suka wuce, basu sha wuyar gane gidan ba, suka yi parking mota daga nesa da gidan suka tako da ƙafa har kofar gate sai suka buga, mai gadi ya buɗe yana ganin baƙin fuska ya tsaya tana tambayarsu.
Wa kuke nima?.
Baƙin Sameeha ne.
To ai bata nan yanzu ta fita.
Zamu jirata.
Binafa ta faɗa a takaice, sai da mai gadi ya ƙare musu kallo yaga ba wani mummunar abu a tare dasu dan hijab suka sha har ƙasa, sai ya buɗe musu suka shiga zuwa falo da yake Kofar a buɗe yake sallama suka yi suka samawa kansu gurin zama, Jamila ta fito daga kitchen da take yin wanke wanke ta ƙaraso tana yi musu sannu da zuwa.
Sameeha fa?
Cewar Hanan.
Bata nan bata daÉ—e da fita ba amma ko a kirata?
A'a bari kawai, amma kawo mana ruwa mu sha.
Tace to ta koma kitchen ta kawo musu ruwan gora da kofi biyu, suka amsa suka sha kana suka ce mata zasu tafi.
Su waye zance mata?
Karki damu zamu dawo anjima ko gobe.
Cewar Binafa, to tace musu kafin suka fita ta rufe kofar falon ta koma ta cigaba da aikinta. Su Binafa suna fita suka shiga mota Hanan tana cewa.
Dole yarinyar nan ta rikice akan mai gidan, kinga hoton masu gidan kuwa mijin ya haÉ—u kam.