Sashe 19
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sameeha ta faɗa cikin walwala da farin ciki haka suka shiga falon, sai da suka natsa kafin suka kai Ikram gida suka gaisa da Umma kana suka yi musu sallama umma tasa musu albarka tare da basu shawarwari wanda zai inganta rayuwarsu, da suka tashi tafiya umma sai da ta keɓe da Sameeha ta ƙara yi mata magana musu daɗi da kuma tunatar da ita wasu abubuwa, kafin suka fito Aminu ya aje musu bandir ɗin 'yan dubu ɗai ɗai wanda ya kama dubu ɗari, kafin suka fito suka shiga mota suka dawo gida, a ranar dai sunyi kwanan farin ciki da jin tamkar duk matsalarsu ta yaye an samu kyakkyawar maslaha da fahimta.
***
Hauwa.
Koda suka sauketa a kofar gida tsayawa tayi a zaure bata shiga ciki ba, sai ta riƙa lekensu har suka shigar da motarsu cikin gidansu kafin ta fito ta tari napep ta wuce unguwar kanawa gidan malam mai allon ƙarfe, dan ba zata iya hakurcewa safiya ba yadda zuciyarta ke azalzala mata, tsantsar baƙin cikin barinsu Aminu Kaduna ya kainainaye zuciyarta, har wani ɗaci ɗaci take ji in ta haɗiye miyau. Da suka isa sai ta sallami mai nalep dan har kofar gidan ya kaita tunda malamin ba ɓoyayye bane, ta aika wani yaro data gani ƙofar gidan ya sallamo mata malam, ba jimawa yaron ya fito yace Malam yace ta shiga ɗakinsa na zaure gashinan zuwa, Hauwa ta miƙawa yaron naira goma ta shiga zauren zuwa ɗakin, ta tura ta shiga ba kowa sai tarkacen kayan aikin malinta, ba jimawa sai ga Malam ya shigo da sallama ya isa mazauninsa ya zauna yana ƙare mata kallo da idanunsa daya sha baƙin kwalli, Hauwa ta gaishe shi ya amsa fuska sake dan ya wayi fuskarta tunda ba yanzu ne farkon zuwanta gunsa ba.
In ban mance sunan ba Hauwa ko?
Eh ita ce, ashe ba zaka manta dani ba.
Ina zan manta dake, ko ba kece kika zo amsar mallakar miji ba da kuma 'yarki da ta samu matsala da miji aka yi miki maganinsa.
Kwarai nice.
Hauwa ta fada tana murmushi tare da gyara zamanta dan ta ji daÉ—in koro masa bayani.
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 14.
Malam mai allon ƙarfe ya kalli Hauwa da kyau yana cewa.
Yau ma na san wani dalilin ya kawo ki dan haka ina saurarenki ko zan iya yi miki maganin damuwar ki.
Yauwa Malam wlh wani babban abune ya kawo ni gunka wanda zan iya kashe ko nawa ne domin buƙata ta biya. Matar ƙanina ne ta sakomu a gaba shi ne nake so a datse igiyar aurenta yayi mata saki uku a wulaƙance.
Ya sunanta kuma shima ƙanin naki ya sunanshi?
Sunanta Sameeha shi kuma Aminu.
Bari na kafe sunansu a allon ƙarfe muga amsar da zai bamu, sai dai kinsan ni bana ƙarya, duk abinda sakamako ya bani to shi nake faɗawa mutum ko yayi masa daɗi ko kar tayi.
Nasani malam ban mance komai ba.
Cewar Hauwa tana jinjina kanta, Malam yace yauwa kana ya ɗauki allon karfensa ya soma jawo wasu kalamai tare ɗaura yatsarsa manuniya a kan Allon ya shiga yin rubutu wanda nan take zane ya soma fitowa a jikin allon, sai da ya gama kafin ya ƙurawa Allon ido tamkar yana kallon wani abu a jiki, ya ɗauki minti goma a haka kafin ya yi ajiyar zuciya ya shafe allon da tafin hannunsa ya ajiye shi a gefe, ya dawo da kallonsa gareta ya soma da cewa.
A gaskiya matarsa ta Allah ce kuma akwai kyakkyawar tsari a jikinta saboda bata wasa da ibada, dan haka babu wani asiri da zai kamata, sai dai É—an uwanki zamu iya yin wani abu akansa tunda ba ya tare da tsari, sannan ban hango rabuwa a aurensu ba a yanzu sai dai na hango akwai gargada anan gaba wanda wani duhu ya rufeshi bazan iya sanin ko miye ba.
Innalillahi wa inna ilaihit raji'un. To malam ba yadda za ayi a sashi ya ƙara aure.
Zan iya amma sai in ya rabu da matarsa.
Yanzu babu abinda za a iya yi akai dan a shiga tsakaninsu.
Babu gaskiya a nan.
Amma zasu yi tafiya gobe ina so a dakatar da tafiyar tasu.
Wannan zan iya yi miki aikinsa amma kan É—an uwanki zai faÉ—a, shi ne zai dakatar da tafiyar da kansa.
Dama shi yace zasu tafi dan ita Sameeha ba so ma take ba, to ba damuwa ayi mini wannan aikin ko tanan na samu nasara kuma ba zan fasa haifar da matsalar da sai ya rabu da ita ba.
Dama sai dai in ku zaku yi amfani da wata hanyar da zaku haÉ—asu har hakan yayi tasirin da zaku raba su, kuma duk inda zaki in dai malamin gaskiya ne to wannan sakamakon zai sanar dake sai dai in yana so yaci kuÉ—inki ne zai ce ba haka ba.
Hauwa tayi jimm tana sauraren zuciyarta, can ta nisa tayi masa godiya tace yayi aikin da zai hana tafiyar, ta kirga dubu takwas daga posa É—inta ta ajiye masa a gabansa tana cewa.
Ga dubu takwas in da ciko sai ka sanar dani in ƙara.
Wannan ma yayi tunda ba aiki ne me wuya ba, sai dai zaki ƙara dubu biyu saboda zan yanka kaza na yi hadaya da jininsa.
Tace to kana ta ƙara masa dubu biyar tace sauran ya ƙara cefane, malam ya washe baki yana dariya ta mike tana yi masa godiya ta fito guiwa a sanyaye dan ba haka taso ba, kuma kamar yadda ya faɗa mata koda taje gurin wani sai dai yaci kuɗinta tunda tasan aikinsa kamar yankan wuƙa ne. Haka ta dawo gida ta zuba kunne dan jin ta inda labarin fasa tafiyarsu Aminu zai zo mata.
***
Aminu.
Cikin dare ya farka a barci a gigice yana zufa hankalinsa a matuƙar tashe sai salati yake yi jikinsa yana kakkarwa, cikin barci Sameeha ta ji motsinsa ta farka ta juyo tana dubansa, yadda ta ganshi yasa tayi saurin miƙewa zaune tana dafa kafaɗarsa da cewa.
Lafiya meke faruwa?
Wani irin mugun mafarki nayi wlh wai kidnapers sun sakawa jirginmu bomb, kuma wai da suka samu nasarar tsaida jirgin duk sun tafi damu zuwa cikin daji, inda suka kashe Abi suka yiwa Amrah FyaÉ—e...
Da sauri Sameeha ta rufe masa baki tana salati tare da cewa.
Kayi shuru haka babu kyau faÉ—ar mugun mafarki, hala kayi mantuwa baka yi addu'a ba ka kwanta.
Wlh kuwa ina danna waya barci ya sace ni banyi ba.
To sai ka kori shaiÉ—an ka koma barcinka Allah ya kyauta In Sha Allah ba abinda zai faru sai alkhairi, mugun mafarki daga shaiÉ—an ne kuma ba gaskiya ba ne.
Humm yace mata ya sauya kwanciyarsa zuwa ɓarin dama yayi addu'a ya tofa ya rufe ido, sai dai barci ya ki ɗaukarsa sai tunani da tsoro daya kewaye illahirin zuciyarsa, Sameeha kuwa ta samu barci mai kyau dan sai da aka yi asubahi Aminu ya tasheta akan ta tashi tayi sallah, dan shi kam idonsa biyu aka kira, ya sauka yayi alwala ya wuce masallaci.
Wajen ƙarfe bakwai Sameeha tana ta hada hadan fito musu da kaya dan tasan lokacin tafiyarsu yayi, kafin takwas ya kamata su isa wajen shiga jirgin ƙasa, tun da ta tashi tayi sallah ta soma shiri duk suka yi wanka, ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast kafin ta tasa yaran suka karya ita kuma ta nufi ɗakin Aminu, ta sane shi a kwance yana duban sama ta zauna gefen ƙafarsa tana jan yatsunsa, ya sauke ajiyar zuciya ya mayar da kallonsa gareta Sameeha tace.
Alhaji naga ko shiryawa baka yi ba kuma kasan ƙarfe takwas da kwata jirgin ke wucewa, gashi har bakwai da minti goma.
Madam Meeha tafiyar nan sai nan da wani lokaci gaskiya dan hankalina ya kasa kwanciya da mafarkin da nayi, ni kaÉ—ai zan koma Abuja na soke tafiyar daku sai nan gaba, kuma nima a mota zan koma driver zai jani mu tafi zuwa anjima.
Da wani irin kallo Sameeha ta dubeshi fuska a dagule kamar zata fashe da kuka.
Haba Abban Amrah sai da muka gama saka rai zamu tafi, duk nabi nayi sallama da mutane meyasa zaka yi mini haka. Kuma fa mafarki ba gaskiya bane, sannan duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa.
Na san da haka amma ni dai abinda naga ya dace nayi kenan, kiyi haƙuri nan gaba zan shiryawa zuwanku dama tafiyar ba shiri saboda rikicinku da su Hauwa ne, kuma yanzu naga komai ya daidaita, zan bawa Kamalu kuɗin da zaije ya yiwa su Abi register makaranta In Sha Allah next week nake so su fara zuwa. Yanzu tashi za kiyi ki haɗa mini ruwan wanka me zafi ki zo ki kamani ki kaini bayi kiyi mini wanka na more miki ki samu lada.
Ya kare maganar yana 'yar dariya tare da jan hancinta, murmushi tayi masa tana jin idanunta suna cikowa da hawaye tunawa da wani moment da tayi a rayuwarsu, Aminu da yaga yanayinta sai ya tashi zaune yana cewa.
Ehen Hajiyar kuka me kuma kika tuna dan nasanki da mugun son soyayya, sai kace daga ƙasar indiya aka kyankyaso ki.
Kai fa hala daga turai aka turoka ka faÉ—o Nigeria baban love.
Ta faɗa tana dariya, miƙewa yayi ya yi kamar zai kamota zai ta zille masa suka shiga zagaye falon suna kwasan dariya kamar wasu kananun yara, Aminu yaƙi barin Sameeha har sai da ya kamata ya rungume ta ta baya yana cewa.
Har gaban Abada ina kaunarki Meeha ke ce haskena kuma farin cikin rayuwata, da babu ke a duniyata tabbas da babu ni.
Allah ya barmu tare mijina ya kuma karemu daga dukkan abin ƙi ya tsole idon makiya, amma kasan ina sonka kuma son da babu gargada ko wasa a ciki, akanka nasan so kuma nasan yadda ake gudanar da tubalin kauna, domin na samu damar yi maka gini a zuciyata wanda duk wuya babu abinda zai sa ya rushe.
Na yarda dake matar Aminun Alhaji Ado meyere.