← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 98

Sashe 80

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama faɗar haka ta miƙe ta wuce tana rausaya cike ta jan hankalinsa, nan take ƙaunata da yake yi mata yaji ya nunku har wani hucin numfashi yake fitarwa, banda ya ɗaukarwa kansa alƙawari babu saki a rayuwar aurensa da Nabila amma da ya saketa ya kasance da Sameeha ita kaɗai, dan sai yayi ma da gaske zai iya yin adalci a tsakaninsu, to zuciya tana son mai kyautata mata haka kuma tana ƙaunar mai ƙaunarta domin Allah, ji yake kamar shi kaɗai ne namijin daya yi sa'an samun matar kwarai, Sameeha ta zame masa bangon jingina farin cikin rayuwarsa a nan duniya da kuma a aljanna da yake fata, haka ya miƙe yabi bayanta wanda koda ya shiga ya sameta cikin wani irin rigar barci da bai santa da shi b,a dan kuwa alƙawari ta yiwa kanta na faranta masa a duk lokacin data gane yana muradinta, Ibrahim bai tsaya ɓata lokaci ba ya bi lafiyar gado tare da ƙanƙameta yana shakar kamshin dake fita daga wuyanta, daga nan sai suka lula duniyar masoya sai da suka samarwa kansu natauwa kafin suka yi wanka tare suka shirya cikin ƙananun kaya, Ibrahim t-shirt blue ya sanya ya saka jins baƙi ya feshe jiki da turare, Sameeha kuwa top ta sanya pink da rashin blue a jiki, sai ta saka siket fari mai buɗewa kana ta ɗauki after dressing mai shara shara blue ta ɗaura akan kayanta ta yane kanta da gyalensa, yadda tayi masifar kyau sai da Ibrahim ya ɓata lokaci wajen yi mata hotuna sannan shima suka ɗauka tare itama tayi masa kafin ya saƙala hannunsa a nata suka fice daga gidan cike da tsantsar soyayya, shine da kansa yaja motar security kuma suna binsu a baya, a haka suka fita tare da buɗe saman mota iskar gari yana kaɗasu gidauniyar soyayya tana fizgarsu.

(Ko wani aure akwai farin ciki a cikinsa muddun akwai kyakkyawar fahimta da kauna).

****

Aminu.

A cikin sati guda yaje Abuja ya koma Kaduna ya kai su Abi makarantar daya amso transfer ɗinsu, tare da driver suka zo ya gabatar dashi ga su Umma, sannan yaje kasuwa yayi wa yaran siyayya mai yawa da kayan abinci daya siyawasu Umma da yawa, kana ya turawa Zaidu kuɗi masu yawa akan cefanen gida mai ɗin mota da sauransu, ya yiwa su Umma sallama ya wuce babban gida nan ma ya sallami 'yan uwansa. A washe gari ya koma Abuja wanda bayan mako guda jirginsu ya ɗaga ya bar ƙasar zuwa London.

*****

Nafeesa.

Tunda aka amshe wayarta ta zama kamar mararniya saboda ta yi mugun sabo da waya, ba ƙaramin hukuntata akayi da shi ba dan ji tayi gwara kullum a bigeta akan a rabata da wayar, tana son yin magana da Najwa sannan ta amsa number Sameeha amma ina ba a barinta ta fita balle ta samu damar yin magana da su. Kuma a satin Taju ya samu Sadi yayi masa zancen Nafeesa sai dai ya sanar da shi Fyaɗe aka yi mata idan zai aureta to, yace ya amince domin kuwa ya yarda da ƙaddara tunda ba yin kanta bane Fyaɗe aka yi mata, sannan ma babu namiji kamarsa da za a bashi auren Nafeesa yace baya so domin daidai gargwado tana da kyau ga hasken fata kuma akwai diri, abu ne da bai taɓa zato ba ko ya kawowa kansa samun matar aure irinta dan haka ya amince. A satin iyayensu suka zo nima masa aurenta da sadaki dubu Hamsin wanda SaDi ya basu, Alhaji ya ce ya basu sannan da zasu tafi ya basu key ɗin gidan daya mallakawa Sadi, yace ya yafe masa akwati nan gaba in ya samu hali sai ya ɗinka mata suturar daya dace, ba ƙaramin daɗi suka ji ba tare da yin godiya.

A ranar Juma'a aka ɗaura aurensu a Masallacin jikin gidan, ba wani taro aka yi ba sai dai 'yan uwa na kusa sun zo kuma kowa yayi mamakin wannan aure na gaggawa, sun dai bayar ƙila Nafeesan taƙi fito da mijine Alhajinsu ya yanke mata wannan hukuncin, ita dai a ɗaki ta yini dan ko fita ta kasa yi nan duk 'yan uwanta suka sameta suna bata haƙuri. Zuwa bayan magrib tayi wanka ta saka wani leshi da abbansu ya siya aka ɗinka mata, kana 'yan biko suka zo aka kaita gidan mijinta. Kowa yayi mamakin gidan da aka kai Nafisa dan gidane filat mai kyau da ɗakuna a katon falo guda huɗu ko wanne da bayi kuma an zuba kayan zamani masu kyau da tsada, hatta kitchen ɗin ya tsaru, sannan ɗakin da aka kai Nafeesa sun tadda setin akwatuna guda biyu da me set huɗu da kuma me set uku, koda suka buɗe sun same ahi cike da kaya masu tsada da kyau, Nafeesa ganin wannan ba zata ya sa ta samu ɗan natauwa a zuciyarta har take jin zata zauna da Sadi tunda bata muzanta ba ta samu gida mai kyau da kayan lefe, 'yan uwa sai sam barka domin malam Sadi ya basu mamaki kuma yayi bajinta, kuma dagasken shine ya yi mata wannan kayan dan ya jima yana tara kaya a gurin yarsa akan koda ya tashi aure bazai sha wuyan haɗa akwati ba, to ganin karamcin dasu Abba suka yi masa yasa shima yace zai gwangwaje Nafeesa da kayan lefe domin ya saka alkhairin da suka yi masa. Bayan kowa ya watse abokansa suka rakoshi yazo ya kirata ta fito cikin babban mayafi ta zauna a cushing nan suka rattafo musu nasiha akan zamantakewar aure dama koyi da sunnar Ma'aiki s.a.w da kuma matansa, wanda yasa jikin Nafeesa ya kuma yin sanyi ta ƙara saduda da karɓan ƙaddararta, bayan abokansa sun gama suka yi musu sallama suka tafi. A wannan dare Sadi ya angonce wanda ko kaɗan Nafeesa bata yi masa musu ba ta bada kai bori ya hau, da Safe bayan sun natsa ya bata sabuwar waya iPhone 13 a cikin kwalinta kyauta wanda yaya Taju ne ya bashi yace ya bata domin dai ta ƙara sakin jiki dashi tayi zaman auren, Nafeesa sai da tayi kukan murna dan sosai taji daɗin wayar sai dai ya sauta mata layi, nan ta yi masa godiya Sadi ya katseta da cewa.

Nine ya dace na gode miki da kika amince da ni a matsayin mijinki baki yi mini jayayya ba ganin ni ba kowa nace almajirin gidanku.

Haba kafi ƙarfin haka a guna domin bazan taɓa gujewa zaɓin iyayena ba, kuma yanzu na tabbata ba suyi mini zaɓin banza ba. Sai dai zan nima alfarma a gunka ka bani tsohon layina dan na cire numbobin daya dace.

Layinki baya hannuna Nafeee, amma bada gmail kike saving ba.?

Wasu suna cikin wayar amma akwai wasu a gmail.

To kiyi amfani da gmail É—inki In Sha Allah zaki samu duk number din da kike so a ciki.

To tace masa kana ya miƙe yayi mata sallama ya fita, Nafeesa ta miƙe cike da farin ciki ta shiga zaga gidanta sai taga komai yayi mata yadda take so babu abinda ta rasa, nan ta shiga jero godiyarta ga Allah dan sosai ta yaba da Sadi saboda' jiya ya shayar da ita wani ruwa mai mugun zaƙi.

Ashe Ustazai sun iya soyayya haka?

Ta faɗa a zuciyarta. A hankali ƙin auren ya riƙa barin zuciyarta har ta fara samar masa gurbi a ciki. Nan ta koma ɗakinta ta kunna wayar dan dama ya sanar da ita anyi chargynta, ta duba ko akwai kuɗi a ciki taga kusan dubu biyar ga kuma data kusan 2gb ta saki murmushin farin ciki sai ta kunna data ta fara setting komai na wayar ta ɗaura gmail ɗinta, duk contact ɗinta suka dawo, nan take ta kira Najwa domin ita ce wacce take son fara kira ta sanar da ita damuwarta dama komai daya faru.

Najwa tana kwance a É—akin yara wanda yanzu ya zama nata, game take yi a wayar Siyama É—iyar Saleema wanda a yanzu ya zama nata dan ta saka sim É—inta a ciki, kiran daya shigo wayarta yasa ta duba taga number ne bata san me layin ba, kamar ba zata É—aga ba sai kuma ta yanke É—auka ta kara a kunne, muryar Nafeesa data ji yasa ta tashi ta zauna tana faÉ—in sunanta. Nafeesa ta amsa tana cewa.

Ƙawata abubuwa da yawa sun faru dani ina son yin magana dake ban samu hali ba, sai yau da aka bani waya a hannuna.

Ina jinki amma kafin nan da fatan kin bar mini Aminu ko, dan kin san har yau ban huce ba.

Dalla waketa Aminu yanzu, ni da aka É—aura aurena jiya da Sadi malamin yaran gidanmu.

Kai dan Allah, garin ya haka ta faru.?

Najwa ta faɗa tana dafe ƙirji da zaro ido waje dan taji lamarin yazo mata a bazata, Nafeesa ta nisa ta soma bata labari tun sadda Taju yaje gida ya sanar da saƙp da aka tura masa wanda Hamisu ne ya tura, tiryan tiryan take bata labari babu abinda ta ɓoye mata, har zuwa auren da aka mata gidan da aka kawota da kuma akwatina ga kuma kyautar waya da Sadi ya bata yau, nan take Najwa taji wani abu ya ɗarsu a zuciyarta wanda sam bata so ƙarshen Nafeesa yazo a haka ba, taso ace ta fita wulaƙanta sai gashi tona mata asirin da tayi yaja mata wani nasara har ta fita mutunci yanzu, Nafeesa jin Najwa tayi shuru bata ce komai ba yasa tace.

Ƙawata kinyi shuru baki ce komai, wlh ke ce na fara kira domin mu shirya kiji kuma abinda ya sameni ki taya ni jaje da murna, sannan kinga yanzu bani ba Aminu sai mu cigaba da ƙawancen mu, ki bani labarin ya kika ƙare da Aminu daya ga ke ce Amaryarsa.

Najwa wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya a kuncita ji take yi komai daya faru ya dawo mata sabo, ga baƙin cikin Nafeesa ta yi nasara akanta ita kam kamar tsiya akanta ya ƙare, cikin sanyin murya tace.
Chapter 80 · 0% Book details