Sashe 48
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta faɗa tana gyara zama, nan Ikram ta zuba mata ta soma ci tana yi tana yagan nama tare da kurɓan zoɓo dan bata yarda ma ta ɗauki kunun aya ba dan tasan yana tayar mata da sha'awa, tana cikin ci ta cika cokali tana kai loma kamar ance ta kalli ƙofar da Ibrahim ya shiga sai taga ya kafeta da ido da sauri ta aje cokali tana tari dan ta kware, shi kuma murmushi ya saki ya koma ciki, dama bai rufe ƙofar ba tura ta yayi ɗazu shiyasa bata ji ƙarar buɗe ƙofar ba, shi kuma hakanan yaji ya leƙo ta yaga zata cigaba da cin abincin data daina ci ɗazun data ganshi, sai da ta sha rufa kafin tarin ya lafa Ikram da bata ga abinda ya faru ba ta shiga jera mata sannu.
Garin ya kika kware.
Ni ina ganin na haƙura da cin abincin nan tashi mu fita mu...
Bata rufe baki ba Khairy ta dawo É—akin tana cewa.
Da fatan kun cinye abincin nan tas.
Idan muka cinye aiko sai kin ce ba mu da lafiya, ni yanzu ma na kware naji na kwoshi ma.
Cewar Sameeha tana zama a cushing dan ta miƙe daga gun abincin, Ikram da ke haɗa kayan ta na cewa.
Anty Khairy ashe yayanku shine Sanator É—inmu, É—azun ya fito daga wancen É—akin yace na zuba masa abinci sai ya koma ciki.
Laaa ashe yaya nan yazo ya ɓoye kansa ba wanda yasan inda yake ana ra nimansa. Ina zuwa.
Ta faɗa tana wucewa ɗakin ta tura ƙofa ta shiga ta same shi yana shirin yin wanka.
Yaya dama nan kazo ka boye kanka bamu sani ba anata nimanka.
Khairy ina buƙatar hutu kuma wannan damar kaɗai nake da shi shiyasa na ɓoye a nan, nasan ba wanda zai san ina nan. Wasu baƙi ne a falo? Ba na gargaɗeku kar wanda ya shigo nan ba.
Yaya wannan special baƙi ne, ƙawata ce babbar, ƙaramar kuma ƙanwarta ce. Yauwa baka ga suna yanayi da Mubeenarka ba.
Wacce daga ciki?
Sameeha babbar.
Haba banga wata kama ba, Mubeena baƙa ce wannan kuma fara ce.
Haba yaya baka dai ƙare mata kallo bane amma hatta wushiryar su iri guda da dimple.
Khairy kenan sai kawai na ƙurawa matar aure ido ina kallonta danna tantance kamarta da Mubeena, ko ance miki banda abin yi ne.
Laaa ai ba tada aure, aurenta ya mutu watanni baya daya wuce yaranta biyu Wlh abin tausayi ya hanata yaran ma, ai mijinta yayi asarar mace ta gari.
To ni da kika tasa ni a gaba da zancen na tambayeki ne? ki kwashe plate É—in nan ki fita dashi ina so nayi wanka na shirya zan fito yanzu.
Yauwa ka fito muyi hotuna.
Saboda ni tsararki ne ko?
Au na manta da Sanator mai tsada nake magana.
Harararta yayi sai ya shiga toilet abinsa, ta bishi da dariya ta É—auki plate da gorunan ta fito falon ta zauna kusa da Sameeha.
Ku tashi mu je ayi mana hotuna.
Sai ta miƙe ta matsar da abincin gefe suma suka miƙe suka fito tare zuwa farfajiyar gidan, suka tsaya ana ta hotuna kala kala banda me hoto yana ɗaukar nashi suma masu waya sai ɗauka suke, a haka har lokaci ya kure a fara kiraye kirayen sallar magrib. Kiran daya shigo wayar Ikram yasa ta matsa gefe ta ɗaga dan umma ce ta a kira.
Ikram na jiku shuru baku dawo ba to Wlh ko mun dare ku zaku zo ku É—aura abincin dare dan ban dafa komai ba.
In Sha Allah yanzu zamu dawo shagalin ne yayi daÉ—i umma, zaki sha labari da yawa dan mun ga karamci iya mutunci.
To Masha Allah haka ake so ki faÉ—awa Sameeha ku dawo yanzu fa, nayi ta kiran wayarta bata É—aga ba.
Ina zata ji kowa sai son É—aukar hoto yake da ita abu dai kamar a film Sameehan umma ta sama tauraruwa, da alama addu'arki ya fara tasiri umma.
To suda mai bakin magana faÉ—i ba a tambayeki ba.
Umma ta faɗa tana murmushi, Ikram dariya ta saka sai ta kashe wayar dan wlh ta ƙosa su koma gida ta fesa musu labari jikinta har tsuma yake dan ta guntso labari mai daɗi. Sai ta koma inda au Sameeha suke ta faɗa mata saƙon umma nan tace dama sallah kawai zasu yi su wuce.
Ibrahm yana gama shiryawa cikin wani tsadadden shadda sky blue riga da wando ɗinkin jamfa ya ɗaura hula da takalmi baƙi, ya fito a asalin Honorable ɗinsa, sai ya fita ta ƙofar baya dan dama ta nan ya shiga baibi ta falo ba, yana isa farfajiyar main house ɗin inda maza suke nan fa suka miƙe aka shiga taro shi maroƙa suka fara nasu aikin ana yi ana masa busa sai kace wani sarki, nan fa aka rufeshi kowa yana kawo gaisuwa yana amsawa fuska cike da amnuri, haka ya soma rabon kuɗi dan buɗe motarsa yayi ya dauko wata jaka ya bawa wani abokinsa yace a rabawa mutane sai ya wuce can ginin dake ɓangaren hagu wanda a da mahaifinsu ne ke ganawa da baƙinsa a gidan, ya zauna a baranda dan akwai kujerun hutu ga kuma sauran abokai da 'yan uwa da suka raka shi nan aka soma chapter, da aka kira sallamar magrib ne sai suka tafi Masallacin dake ƙofar gidansu wanda yake musamman na gidan ne Abbansu ya gina. Har Tafsirin Al-Qur'ani yana yi da watan azumi Usman yana ja masa baƙi lokacin da yake a raye. Kusan duk mazan nan a masallaci suka gabatar da Sallah liman ya jasu, bayan sun idar suka dawo cikin gida cikin tamfol suka zauna ana cigaba da hira.
Sameeha sun fito bayan tayi sallama da mutanen gidan, hajiya tana ta saka musu albarka har suka fito, rakiya har da 'yan uwansu Khairy sannan ta haɗosu da wannan sauran abinci a kuloli tace wlh dasu zasu tafi sannan ta ƙara haɗa musu drinks da snack ga soveniers ko wanne saida ta bashi nashi har da na umma da yaya Zaidu da Anwar, har farfajiyar gidan suka rakosu inda maza suke sai Khairy ta kwalawa Shamsu kira ya taso da sauri ya zo ya risina yana cewa.
Da girman kujerar Anty K, gani.
Kaga bana son shiririta ga ƙawata ka kaisu gida a motarka. Sameeha nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci wlh yau kin shayar dani farin ciki sosai. Shamsu fito sa motar ka kawo shi nan su shiga.
To Anty Shamsu yace sai Sameeha tayi saurin katse shi.
Barshi kawai malam Shamsu muna da abin hawa.
Kamar ya fa? a daren nan? To bazan bari ku shiga napep ba.
Cewar Khairy, Ikram ta fara dariya tana cewa.
Anty Khairy da motar anty Sameeha muka zo, motar da Yaya Zaidu ke hawa nata ne fa, bata hawa shiyasa baki sani ba.
Wani kallo Khairy ta yi mata na mamaki.
Ikon Allah kawata abin duniya be dameki ba, ai ban taɓa sanin kina da mota ba shine ko ki faɗa mini.
Labarin hakan ne bai zo ba kuma bana fita da ita ne shiyasa.
Cewar Sameeha tana murmushi, nan ta faɗa musu inda tayi parking sai suka wuce har gurin, Shamsu yana tafiya tare da Ikram tana tambayarta sunanta da unguwarsu, Ikram taƙi yin magana saboda tasan tana da wanda zata aura, amma ganin ya na niman damunta yasa ta bashi number ɗinta akan za suyi magana, Shamsu bai yarda Number dai dai ta bashi ba dan haka ya juya da sauri ya dauko motarsa ya shiga ya jira har Sameeha ta tuko nasu Su khairy suna ɗaga mata hannu har ta bar gidan shima shamsu ya rufe musu baya, sai yanzu yake tunanin kamar ya san Ikram a wani guri wanda a hankali ya tuna Najwa dan suna ɗan kama da Ikram sai dai fari ne tafi Ikram ɗin. In har hakane to wataƙila 'yan uwane kuma yadda Najwa ta yi masa wulaƙanci tayi blocking ɗinsa to ko sai yayi yadda zai yi ya samu Ikram domin ya nuna mata shi ɗin ba matsiyaci bane kamar yadda tayi zato. Ba zai mance rabuwarsu da ita ba tun lokacin data tambaye shi kuɗi dubu goma sai ya tura mata dubu Ashirin, to tun ranar ya daina samunta a layi daga baya ma ya je gidansu hira tace ace bata nan, ya ƙara aikawa ta fito cikin masifa ta yi masa wulaƙanci son ranta akan yayi haƙuri ita ba zata iya aurensa ba bisa dalilin matsiyaci ne shi bai da kuɗin da zai iya kulawa da ita, sannan ma ko motar hawa bai da shi, kuma ba zata auri miji baƙi ba sai fari ɗan kwaliza dan ta kula ko wanka bai iya ba kullum cikin manyan kaya. haka ya tafi guiwa sake da alƙawarin ko ita ce autar mata ya haƙura. Dama tuntuni yaga take takenta shiyasa ya ɓoye mata asalinsa domin ya gwadata yaga ko zata so shi domin Allah sai kuma ta faɗi.
Shamsuddeen.