Sashe 52
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin farin ciki suke zaune a tsakar gida suna mayar da zancen abinda ya faru ɗazu na kuɗin aurensu da aka kawo, ko wanne fuskarsa cike da annashuwa,wanda Zaidu yake faɗar zai je MGfurnitures domin yin magana da shugaban company kan kayan katako da zai yi musu oder, Ikram tace cikin zaƙuwa.
Aiko kayansu nake so, dan wlh sun iya aiki kayansu tamkar daga ƙasar waje kuma suke haɗawa da kansu a nan Kaduna, naji ance ba inda ma basa tura kaya a faɗin Nigeria har Niger ana fitar da kayansu. Yaya Zaidu nifa komai nasu na funitures nake so.
To azagwaigwai kazar birni, Ikram ba kunya, ashe dai kina son Shamsu har haka yadda naga kina murna.
Cewar Sameeha tana 'yar dariya umma tace.
Rabu da sakarya ai da ta yiwa kanta illa ta rasa nagartaccen miji, ga Aliyun data damu dashi har yanzu ba labarinsa ma.
Zaidu zai yi magana wayar Sameeha ta katse shi wacce take kusa dashi, Sameeha ta dauko wayar data aza a cinya ganin sunan Aminu data yi saving ta sauya masa da sunan da da ta aje numbernsa, yasa taji gabanta ya faÉ—i dan tasan yaranta yanzu suna da wayarsu daya siya musu, kuma dashi suke magana, har kiran ya kusa tsinkewa Umma tace.
Ki É—auka mana, waye ma ya kira naga kin yi sororo ne.
Wai Aminu ke kirana wataƙila yaran nan ne suka ɗauka dan su kira ni.
Ta bata amsa lokacin wayar ma ta tshinke har wani ya sake shigowa, sai ta ɗaga ta ƙara a kunne tana sallama. Jin anyi mata shuru sai saukar hucin numfashi da ta ji yasa ta gane Aminu ne, cikin karfin hali ta ce.
Ina yini ya aiki?
Sameeha!
Ya faɗa cikin ɗaga murya ya ƙare da sauke numfashi, gabanta ne ya faɗi tama kasa amsa masa ta tsaya tana saurarensa, ya cigaba da cewa.
Ance mini aure zaki yi dagaske ne?
Sameeha sai da ta cire wayar a kunnenta ta ƙara duba number ɗinsa dan ta tabbatar da shi ne, kafin ta mayar ta ki cewa komai dan bama san amsar da zata bashi ba.
Kinyi shuru ko amsar ki kenan? ya tabbata kenan aure za kiyi, hakan ya nuna dama tuntuni kina son rabuwa dani kije kiyi aure, sai kika ƙi nuna mini sai da abin nan ya faru kafin kika samu damar saki, ina ganin dama kin shiryawa hakan ne domin ki samu damar rabuwa dani, na jima ina mamakin ganin wannan 'yan matan a gidanmu bayan kinsan nace miki washe gari zan dawo da sassafe mu tafi kano, dama kinyi haka dan na gansu ne na sake ki tunda na tabbatar in sun kwana a gidan dole zan haɗu dasu, sai dai in kin ɓoye su a wani wajen.
Haba Aminu ya zaka ce haka, ka sani yanzu ba igiyar aurenka a kaina dan zanyi aure ba haramci a ciki, kuma batun 'yan mata, to nace na aikata É—in, hukunci kuma ka gama yanke mini tunda ka sakeni, babu sauran mayar da hannu agogo baya.
Hmmm dole ki naÉ—e tabarman kunya da hauka Sameeha, domin yanzu ne na tabbatar da wacece ke tunda daga fita idda sai aure, kamar kina jira na sake ki, kin bani mamaki ban zaci haka daga gareki ba, nagode wa Allah daya bayyana mini ke wacece kuma In Sha Allah ki zuba ido zan nima lafiya duk inda yake koda nan da birnin sin ne zanje domin nima na yi aure, dama dakon sonki ne yasa nake ganin zan iya komawa ga Allah a yadda nake, amma yanzu kin shayar dani gubar mamaki daya zaburar dani akan na nima lafiyata, kin nuna mini ke É—in 'yar Adam ce Sameeha wato butulu.
Me nayi maka dana zama butulu Aminu? kawai dan zan yi aure kake faɗa min baƙaƙen magana saboda son zuciya, kar ka manta ƙaddara ita ta haɗamu kuma itace ta rabamu.
Kaddara ko kuma cin amanata da kika yi Sameeha, ai da ban kamaki da yaran nan ba da yanzu muna zaman aurenmu.
Zaidu ne ya fizge wayar daga hannun Sameeha ya kara a kunnensa, da yake duk suna jin maganar Aminu saboda sunyi shuru kuma volume ɗinta ana ji sosai koda bata saka handsfree ba, Zaidu yace cikin ɓacin rai.
Dan Allah karka sake kiranta ka nima ɗaga mata hankali tana cikin farin ciki, tunda kai ka saketa kace baka yi da ita duk halaccin data yi maka ta zauna da kai tsawon shekara shida ba ka da lafiya amma ka saketa akan abinda ba kada tabbas, dan haka ta samu wanda yake sonta kuma yake ganin mutuncinta gidan mutunci ba irin 'yan uwanka ba marasa mutunci, yara kuma kar Allah yasa ka kawo su ka riƙe su In Sha Allah zata haifa mana wasu a sabon gidanta.
Bai jira ya yi magana ya kashe wayar yana huci, Umma ta riƙe haɓa.
Ashe shima baida mutunci ina yi masa kallon salihi, koda yake ai nono guba Hauwa ta sha ta sake masa, ina ganin abin nasu ya samo asali.
Nifa ina ganin kishi ne yasa shi fusata haka, ko uban waye yace ya sake ta oho.
Cewar Zaidu, Umma tace.
To kishi sai ya saka idonsa ya rufe ya rika faÉ—in magana sai kace wanda cutar É—an kanoma ya kama, haba abin ya yi yawa, ni nayi mamakin ma yadda ya samu labarin auren abinda akayi magana yau yau amma har magana ta isa gareshi shi da yake Abuja.
Ai kiwon mutum ake yi Umma, da alama ƙila ya saka masu yi masa bincike akanta ne suna faɗa masa halin da take ci, in ba haka ba taya daga magana yau har ya samu labari.
Cewar Ikram cikin faɗa, nan dai suka dinga juya maganar Sameeha dai ta kasa cewa komai sai maganganun Aminu ne suke yi mata yawo a zuciya, dan sosai lamarin ya taɓa ta ba yi zaton jin waɗannan kalamai a bakinsa ba, kira daya ƙara shigowa wayarta yasa ta duba taga number ce da tun ɗazu da take magana da Aminu ake kiranta, har ya katse bata ɗaga ba sai ma miƙewa tayi ta wuce ta ɗauki buta ta wuce bayi dan tayi fitsari, tana shiga ta saki kukun da take dannewa, sai dai bata bari tayi mai sauti ba dan kar su ji ta, gabaɗaya duk farin cikin da take ciki ya yaye sai baƙin cikin abinda Aminu ya yi mata yanzu daya maye gurbin zuciyarta, ko a mafarki bata taɓa tunanin zai yi mata haka ba, babban baƙin cikinta yadda ya gasgata ta aikata masha'a da 'yan matan nan, har gobe ba zata iya yafe musu ba dan duk sallah tana kai kukanta gurin Allah akan ya saka mata tare da jera musu Allah ya isa, babban farin cikinta yadda su Hauwa basu san dalilin mutuwar aurenta ba, da sun sani ta tabbatar ba zasu taɓa barinta ba dan sun riƙa zuwa kenan suna niman rikici da ita, haka tasha kukanta ta gama ta wanke fuska ta fito ta wuce ɗaki suf-suf bata bi ta kansu Ikram ba, su dai kallo suka bita dashi dan sun san in tana cikin damuwa to shuru take yi bata magana da kowa, sai ta kaɗaita kanta ita kaɗai tana sharɓan kuka, Ikram data bi bayanta da kallo har ta shige sai ta juyo tana cewa.
Umma kuka fa tayi a bayi, baku ga yanayinta ya sauya ba.
Na gani tunda nasan halinta, ku rabu da ita da kanta zata saki ranta, kuka da damuwa dole tayi domin duk inna tuna da wannan sharri da 'yan matan nan suka yi mata sai na tsine musu tare da addu'ar Allah ya tona musu asiri.
Ameen nima wlh ina yin addu'ar Allah ya hana musu kwanciyar hankali.
Cewar Zaidu, haka suka cigaba da hira wanda duk rabi akan zancen Sameeha ne.
Aminu kam wayar yabi da kallo lokacin da Zaidu ya kashe kiran, ya tsugun kan guiwarsa yana jin wani ɗaci a makoshinsa, jikonsa har wani kalkarwa yake tsabar damuwar daya samu kansa, dana sanin sakin Sameeha ya rufe shi sai yaji dama saki ɗaya yayi mata ko biyu yadda zai samu damar gyara aurensu ta dawo masa, tabbas yadda yake ji a zuciyarsa hakan yana nuna shine ya zalunci Sameeha, domin kuwa dama a tsakanin ma'aurata duk wanda yayi zalunci to tabbas yana gamuwa da dana sani a gaba kuma wanda aka zalunta yana riga yin aure, bai san hawaye yake yi ba sai da ya taɓa kuncinsa ya shafa kafin ya gane haka, shima yasan duk maganganun daya faɗa mata ɓacin rai ne dan har gobe zai shaidi kyawawan halayyarta, sai ya miƙe cikin sanyin jiki yana ambaton sunan Allah dan hakan ne kaɗai zaisa ya samu sassaucin halin da yake ciki.
*Barkanmu da Sallah fatan munyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana yasa muna cikin yantattun bayi. Ameen.*
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
35.
Aminu bai taɓa zaton Abin da ciwo ka saki mata wani ya aura ba sai yanzu, bai kawo zai damu ba in yaji Sameeha zata yi aure ba, sai gashi abu yana niman zama masa ƙaya a maƙoshi, zazzaɓi mai zafi yaji ya kamashi kuma a haka ya kwana, wanda da kyar barci ya ɗauke shi. Washegari da wuri ya shirya ta tafi asibiti, dan ya ɗauki alwashin nimawa kansa lafiya ko nawa zai kashe, sannan ma dole ne ya amsa auren da Hauwa ta samo masa domin ya huce takaicin Sameeha, zai yi fatan ya samu lafiya kafin bikinsa duk da ba yi da tabbacin zai samu lafiyar, amma ya ɗaura niyya sai inda ƙarfinsa ya ƙare.
*
Ibrahim.