← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 98

Sashe 22

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Binafa tana 'yar dariya, suma dariyar suke yi cike da jin daɗin samuwar mafitarsu. Sai gabda magrib Nafeesa da Najwa suka bar gidansu Binafa dama aikota ummansu tayi ta samu guri ta rashe, da yake baban Binafa shine yayan maman Nafeesa. Binafa irin sagartattun yaran nan ne da uwa ba kwaɓa kaka ba tsanani, ita ce kaɗai mace a gidan shiyasa kowa ya ke bata kulawa daga iyayenta har yayyinta, wannan kulawar ya jawo ta faɗa mummunar rayuwar lesbian, hakan ya faro ne tun daga makarantar secondary ita da ƙawarta Hanan da sauren kawayensu, har suka shiga jami'a suna tare bawai dan maza basa kulasu ba sai dan su sun keɓe kansu da mu'amala da su a cewar su namiji bai kai ya wulaƙanta su ba, kuma yadda suka riƙa a harkar basa jin sha'awar namiji kwata kwata shiyasa taƙi aure duk da iyayen suna so tayi, sai cewa tayi a ƙara mata lokaci, Hanan dai tayi aure bai daɗe ba ya mutu ta cigaba da harkanta da matan data saba, shiyasa sun gagari iyayensu sai abinda suke so suke yi sai dai har gobe babu wanda yasan ga abinda suke aikatawa, sai Nafeesa da itama nuna mata suka yi ta haɗe dasu tace ba zata yi ba tana tsoron Allah hakan yasa ta shiga musu wa'azi sai dai bai yi tasiri ba, Binafa ta roki Nafeesa data rufa mata asiri zata bari da zarar tayi aure, ta sakar mata kuɗi mai yawa wanda yasa Nafeeaa taja bakinta tayi shuru shiyasa bata cika zuwa gidan ba sai an aikota suke haɗuwa, sai gashi yau Binafan zata yi mata rana tunda zata kawo musu ƙarshen matsalar Najwa. Sai da mai napep ya fara sauke Nafeesa kafin ya juya ya sauke Najwa a gida wanda a lokacin ana gabda kiran sallar isha'i. Tana isa ta samu yayanta Junaid yana zaune a tsakar gidan suna zancenta da Inna, koda ta ganshi gabanta sai da ya faɗi ta ƙarasa ciki jikinta a sanyaye, da harara ya bita yana cewa.

Wai gidan uban waye kike zuwa ne yanzu, kin fara sabon yawo har kikai dare a waje. Ko kin mance da dokar gidan nan ne akan kar ki riƙa bari magriba tana yi miki a waje.

Yaya bikin ƙawata za ayi to munata shirye shirye ne fa.

Ni baki faÉ—a mini biki za kuyi ba Najwa, cewa kika yi zaki je gidan su Nafisa ki dawo akwai maganar da zaku yi na gasar karatu da aka shirya a makarantarku. Ina mamakin yadda halinki ya sauya lokaci guda Najwa ki zauna kina shinfiÉ—awa mutane karya.

Allah inna biki muke yi ban dai faɗa miki bane kuma dagaske za muyi musabaƙar Al-Qur'ani a makaranta. Kuyi hakuri ba zan sake ba.

Ai kin saba kiyi laifi ki bada haƙuri, to wlh daga yau in na ƙara ganin haka sai na kusa karyaki.

Cewar Junaid a fusace, Najwa ta buro baki ta wuce É—aki tana cewa a zuciyata.

Na kusa dai hutawa da wannan masifar naka, zan yi aurena na bar muku gidan gabaÉ—aya sai wanda naga dama yaje mini gidana.

Ta zauna a gefen gado tana cire safar ƙafarta dan bata yawo ba safa, tunawa da tayi da plan ɗinsu da suka shirya yasa ta saki murmushi ta ciro wayarta a jaka ta dubo number ɗin Jamila ta kirata, kiran ya kusa tsinkewa ta ɗauka tana sallama, Najwa ta amsa tana sakin murmushi.

Hajiya Jamila kwana da yawa ko É—an flashing zamani ba kya yiwa mutane.

Anty kin san ni ba wani kuÉ—i nake sawa a wayar ba sai in an kirani dan ba fita nake sosai ba, ya kwana biyu? Kin dai na zuwa gidanmu bama ganinki.

Makaranta ya ɓoye ni yanzu ma wani dalili yasa na kiraki ina so gobe mu haɗu, amma a layin dake bayanku, wani aiki zaki mini na dubu ashirin, idan kinyi aiki da kyau zan caske miki kuɗinki.

Wlh zanyi aikin dan babu abin da ba zan iya yi ba akan wannan kuÉ—in, ace lokaci guda na samu dubu ashirin kamar mafarki, nan fa da dubu goma ake biyana duk wata aiko nagode sosai.

Yauwa zan fito ƙarfe goma na safe kuma zan kiraki kafin na ƙaraso sai ki fito mu haɗu.

To Jamila tace mata cike da tsantsan murnan kuɗin data ambata, ɗan sosai ta kwaɗaitu da su, Najwa ta koma ta kwanta tana tunanin yanzun wa zata daki hancinsa ta samu dubu ashirin, sai ta tuna da Zaidu da suna tare ta san wlh zai bata, taja guntun tsaki tace bari ta latsa wani saurayinta Shamsu, shima ba laifi yana da sakin hannu kawai bai yi mata bane saboda baƙine sosai kamar shuni, gashi yana mugun sonta, nan take ta tura masa da sakon tana buƙatar kuɗi dubu goma kuma cikin sauri, dan wani abu muhimmi ne ya taso mata, ta tura tare da account number ɗinta. Shamsu daya ga sakonta ya saki murmushi yana cewa.

Uwar son kuÉ—i zanyi maganinki.

Yana gama faÉ—ar haka ya tura mata dubu ashirin tare da sakon.

_Sauran kuÉ—in kisa kati a waya, amma ki tabbatar da in na zo hira maganar aure za muyi dan wlh na gaji da jan ran da kike yi mini._

Ya tura mata, Najwa tana ganin alert ta saki ihu cike da murna, data karanta sakonsa ta saki wani uban murmushi ta mele baki.

Aiko zaka ji a salansa wlh, dan blocking layinka da komai zanyi yanzu, ka gama yi mini amfani.

Ta ƙare maganar tana ɗage gira ta zauna da kyau ta shiga blocking ɗinsa.

_Zaku iya fara biyan kuɗinku domin muna gab da gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. Bononza na kwana Huɗu akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, dan Allah ku mara mini baya._

Pay N300 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO*

Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 16.

Najwa wani tunani ta sake yi bayan ta zauna tayi shuru da mintuna, a daren ta ƙara kiran Jamila tace mata ta bata kwana biyu zata sake kiranta su haɗu saboda wani uzuri ya taso mata, Jamila tace mata to sai ta kashe wayar tana gyara kwanciya. Najwa sai da ta ɗauki kwana biyu bata fita ba saboda kar Inna ta saka mata ido, ta natsu sosai tana nazarin yadda zata ɓillowa Jamila ta amince da bukatarta, duk da ta san zata iya yin komai akan kuɗi amma dole in ta ciza ta huta dan kar kwaɓarta tayi ruwa, hakan yasa ta samu damar haɗa wata dabara da kuma wani makirci dan ta gogawa Hauwa nata kashin kajin, hakan yasa ta kuma shafe kwana biyar tana lissafi. A ranar da ta cika kwana bakwai cif da haɗa plan ɗinsu dasu Binafa wato ya kama yau juma'a to daren ranar Najwa ta ɗauki kwalin maganin da Binafa ta bata, ta tsaya tana wani nazari sai da ta kai mintuna tana yi kafin ta sauke numfashi tana sakin murmushi, gabaɗaya magani guda takwas ta ɓallesu ta tashi ta ɗauko wata santana leda dake cikin ɗakinta wanda inna ta adana na saka tuwo, ta kulle ta fita tsakar gida ta samu ba kowa sai ta shiga kitchen ta ɗauki taɓarya ta daddaka maganin ya koma gari ta dawo ɗaki ta sauya masa leda saboda wannan ya faffashe, ta mayar ta saka a jakar islamiyyanta, ta duba agogon wayanta taga ƙarfe tara da minti uku, lokacin ne ta ƙara kira Jamila tace mata ta fito da ƙarfe goma na safe su haɗu, tace mata to sai ta kashe wayar ta gyara kwanciyarta.

******

Sameeha.

Tana zaune a falo tana lissafin biki saura kwana 21 wato saura sati uku, kayan da zata yi fitan biki dasu ta tuna bata amso daga É—inki ba, dan haka yasa tace zata je gurin telanta ta duba ko ya gama dan so take kan lokacin komai ya kasance a hannunta, shiyasa gari yana wayewa ta shirya yara da kayansu zata kaisu gidansu suyi hutu saboda sun samu hutun makaranta wanda tace sai biki ya rage saura kwana É—aya zata É—auko su saboda ta samu damar yin zirga zirga, sai ta soma ninke kayan Amrah tana sakawa a trolly wanda zasu tafi dashi gidan umma, sai kuma ta buÉ—e murya ta kwalawa Jamila kira sai gata ta fito ta tsaya tana cewa gata.

Yauwa jeki ki kwaso mini takalmar Abi ki zo da tsumma ki goge min su.

To tace mata sai ta wuce taje ta dawo ta soma aikin gogesu, wayar Sameeha tayi ƙara ta ɗauka ganin Aminu ne, bayan sun gaisa take ce masa.

Maganar kuÉ—in da kace zaka turo na kama hol É—in taron sisters eve da zamu yi, in kuma ka yarda sai muyi a gidan nan tunda wlh komai ya wuce ba wata matsala.

Sameeha maganin kada a kuma to kar a fara, zan turo da kuÉ—in kawai dan bana son damuwa, ya batun su Abi sun kammala exam ko?

Eh gasu nan ina haÉ—a musu kaya zasu gidan umma sai biki saura kwana É—aya kan su dawo saboda na samu lokaci sosai na huta da kuma zirga zirgan bikin.

Hakan yayi ki gaida umman, ina ganin nan da sati biyu zan dawo.

Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya.

Ya naji kamar ba kya missing É—ina, har kin fara sabawa kenan da rashin ganina.

Haba my Man, missing ai ya zama jinin jikina kawai dai juriya ce yasa kaji na dake kamar ba komai.

Murmushi yayi yace sai zuwa anjima, haka suka yi sallama ta aje wayar, ta cigaba da haÉ—a kayan, a lokacin Jamila take cewa.

Anty na gama, kuma ina so in faÉ—a miki zan fita anjima zan je duba wata yayata da take mando ta kirani bata da lafiya.

Amma baki taba faÉ—a miki kina da 'yan uwa anan ba.

To da ya yake ba muyi hirar ba kuma nima bason fita nake ba shiyasa baki sani ba.
Chapter 22 · 0% Book details