← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 98

Sashe 41

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sameeha ta saki murmushi.

Naji daɗi Inna yau zamu faba dare muna hira. Gogganmu ina Najwa? ta kwana biyu bata leƙomu ba.

Ta ƙare maganarta ga inna Zulai, sai tace mata.

Ai Najwa an kusa girma dan an saka ranar bikinta nan da wata shida in Allah ga kaimu shiyasa nazo na sanar daku.

Wani mai rabo ne zai yi wuf da ita haka, to Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu.

Ameen ya rabbi, sunan yaron Muhammad yana aiki a Abuja.

Lallai Najwa ta samo mana mai zafi ashe Abuja zamu kaita. Masha Allah nayi murna kwarai.

To bamu san inda zata zauna ba tukuna tunda ance É—an nan ne kowa nasa yana nan.

Allah sarki to Allah ya sa albarka. Ni bari nayi sallar Azahar.

Cewar Sameeha sai ta miƙe ta fito tsakar gida su kuma suka cigaba da hira dan duk sunyi nasu sallan. Sai wajen ƙarfe uku Inna tabar gidan a lokacin ne inna Rakiya ta samu damar faɗawa umma zacen dake cinta a zuciyata.

Nifa yaya maganar Sameeha ya kawo ni, Idrisa ƙanin mijina dake aiki a Kano tunda yaji labarin mutuwar aurenta ya dage akan yanq ciki in ta fita idda zai zo ayi magana. Shine fa tunda yaji nace zan zo ya matsa mini numba, shiyasa nace zan sanar daku inna zo.

Umma tayi shuru can ta kalli Sameeha da take gyara wake tana cewa.

Ga ki ga Sameehan ai tana jinki, dan yanzu magana nata ne ba a yiwa Bazawara zaɓen miji sai wanda ta kawo.

Ai nasan É—iyata ba zata bani kunya ba, Sameeha ina so ki bawa Idrisa dama ku daidaita yaron yana da mutunci ga sanin ya kamata, yana aiki a kano a wani company amma matarsa tana nan cikin zaria kusa damu, yaransa biyu duk maza.

Inna banƙi ta taki ba amma gaskiya a yanzu babu tsarin yin aure a zuciyata ko in ce nan kusa, ban sani ba ko nan gaba in abubuwa sun daidaita a zuciyata, dan in har na amince kamar na takurawa kaina ne.

Haba Sameeha ƙanin mijina ne fa kuma nasan halinshi ba wata matsala wlh ko matarsa ba tada damuwa dan tasan yana sonki.

Inna a bani lokaci.

Sameeha ta faɗa tana miƙewa ta fita tsakar gida da ido suka rakata, Inna tana cewa.

Ni wlh banda ya takura bazan yi maganar ba tunda yaushe ma ta fita idda, sannan ma ai da ciwo har yanzu a zuciyarta na abubuwan daya faru, zan sanar da shi ya hakura kawai dan ba zan so takurata ba Allah.

A'a kar kiyi saurin yanke hukunci Rukayya, ki bari tunda tace a bata lokaci kuma nima zanyi magana da ita dan aure shine cikar mutuncinta ai.

Haka suka dinga tattaunawa Sameeha tana jinsu duk zuciyarta a dagule, sarai ta gane wanda suke magana sam bai yi mata ba balle ta kawo wa zuciyarta sha'awar aurensa, haka ta ƙarasa yininta sukuku dan har gobe son Aminu yana manne a zuciyarta, dangana ne kawai tayi a ba yadda zata yi.

*****

Khairy.

Tana isa gida ta shiga kitchen dan dafawa kanta abinci saboda gabaɗaya yaran sun je gidansu suyi hutu saboda anyi hutun makaranta, ita kaɗai ce a gidan sai 'yar aikinta Naja sannan mijinta baya nan kuma ma ba itace da girki ba yana gidan amaryansa, wayarta data ji tana ƙara a falo yasa ta fito ta isa center table ta ɗauka, ganin anty Amina ce babbar yayarsu da take aure a Abuja yasa ta ɗaga da sauri.

Ina yini Anty.

Amina ta amsa suka shiga gaisawa da hirarsu ta zumunci, can sai Khairy tace mata.

Anty yau na haÉ—u da mai kama da marigayiya Mubeena hatta wushiryarsu da dimple É—insu iri daya, sai dai ita wannan tanada manyan idanu.

Nan ta kwashe yadda suka haÉ—u da Sameeha da komai da faÉ—a mata.

Khairy sannu da ƙarfin hali, kawai sai ki shigewa mata baku ssn juna ba, kika sani ko tanada wani aure a kanta in kin yi zargin ma bata tare da uban yaranta.

Anty Amina wannan ba tada aure dan a gidan iyayenta na sauketa.

Alhamdulillah da alama Ibrahim ya samu mata, dan na tabbata in ya ganta tayi kama da Mubeena zai sota, sai dai kafin nan ki shiga jikinta sosai kisan abubuwa game da ita da bugan ruwan cikinta akan me ya rabata da mijinta. Idan kin samu bayani mai kyau ki riƙa sanar dani.

Anty ai wannan dai ina ganin sakin ganganci mijin yayi mata dan wlh full option ce matar fita anguwa, yaya Khalil ya samu matar shiga taro tunda Labeeba tana ja masa aji.

Aiko ajinta yana gab da tsinkewa dan gani take kamar ba zai iya ƙara aure ba tunda yaƙi karɓan tayi a cikin dangi da aketa yi masa na 'yan mata, Allah dai ya zaɓa abinda ya yake Alkhairi, karki faɗawa kowa wannan maganar har sai mun tabbatar da ta cancanta.

To khairy ta faɗa tana murmushi kana suka shiga hirar walimar haddar da Ƙaninsu zai yi nan da wata guda, taro suke shiryawa na gani na faɗa dan shine autansu kuma mahaifinsu Allah yayi masa rasuwa sai Hajiyarsu ce data rage musu. Dan haka dole sune zasu tsaya su tsara komai yadda zasu fita kunyar mutanan da suka tara. Wani kira daya shigo wayarta yasa tayi sallama da anty Amina ta ɗauka tana cewa.

Babban wa uba kuma mai share hawayen Khairy.

Zaki fara ko? gani na shigo gari ki haɗa mini abinci na mutum biyar haka zuwa shida, meeting zanyi dasu da dare a guest house ɗina, kin san bana son abincin waje saboda tsaro, sannan Nabeela bata gari bana so naje gida nasa Ma'u girka Hajiya ta yi faɗa, kin san bata ƙaunar rashin zaman da Nabila bata yi a gari.

Karka damu Honorable, kamar me zan dafa yanzu na fara shiri.

Fried rice da tuwon shinkafa miyar agushi da kuma sauran abinda kika ga ya dace ki ƙara, karki damu da drink abincin kawai zaki girka na fita kunya.

To In Sha Allah zuwa magrib komai ya kammala sai ka aiko a amsar maka.

Ok ya faɗa kana ya kashe wayar ba jimawa taji alert ya shigo wayarta na dubu ɗari biyar, wani murmushi ta saki ta miƙe tana cewa a fili.

Yaya kenan baya gajiya da kyauta, É—an girkin nan shine ya bani wannan kuÉ—in haka.

Ta ƙare maganar cike da tsantsar farin ciki da nishaɗi.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

27.

Khairy sai gabda magrib ta kammala musu abincin wanda ta haɗa da farfesun naman rago da kuma soyayyar kaza haɗi da sakwara da ta tuƙa musu garinsa su ci da miyar aghushi, a cikin wasu jigaggun food wormers ta zuba abincin ta shiryasu akan dinning idan driver yazo ya kwashe, ta koma ɗaki ta bar Naja tana gyara kitchen ɗin, sai ta shiga wanka lokacin da ta fito ana kiran salla, dama da alwalarta ta fito ta saka hijab da zanin data ware na sallah ta gabatar da farilla, data idar ta miƙe ta shafa mai ta ɗauko wasu ƙananun kaya riga baka mai guntun hannu ta kamata sai legis baƙi shima ta ɗaure gashinta ta filo falo ta zauna a cushing tana mayar da numfashi, sosai ta gaji da girkin da tayi duk da ta saba da girki dan bata yarda mai aiki tana saka mata hannu a fannin abinci, shiyasa ta ciri tutu a gun mijinta dan yana matuƙar son abincinta saboda ta iya girki kala kala, musamman take da group a WhatsApp na girki tana faɗawa mata irin nata salon basirar kyauta. Sai kuma naƙasunta bata iya gyaran gida tana da shauni da son jiki bata son wahala hatta ɗakinta mai aiki take gyarawa ɗakin mijin ne take ƙoƙarin gyara masa dan bata yarda tana wasa da hidimarsa, sannan bata son raino shiyasa ta ce ita ta gama haihuwa hudun nan sun isheta. Wayarta ce ta katse mata kallon tv da take yi tana ringing, ko da ta duba Yaya Ibrahim ne ta ɗauka da sauri.

Khairy abincin ya kammala kuwa?

Tun É—azu na gama driver zai iya zuwa ya É—auka.

A'a ki kira mijinki ki faɗa masa zaki kawo mini abinci, nafi so ki kawo da kanki dan bana yarda da kowa sama daku 'yan uwana sai matata a fannin abinda zan ci saboda tsaro, idan ba zaki iya tuƙi ba zan aiko driver ya zo ya ɗauke ki ya dawo dake.

Zan iya ma bari na fito, amma guest house É—in zan kawo maka dake NDC.

A'a gidana dake unguwar sarki zaki kai mini.

To tace masa ta kashe wayar tana miƙewa tare da komawa ɗaki ta ɗauki dogon hijab har ƙasa ta saka, sai ta ɗauki key motarta ta fito ta kwalawa Naja kira ta fito daga ɗakinta, sai ta yi mata umarni ta kwashe kulolin abincin zuwa mota.
Chapter 41 · 0% Book details