← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 98

Sashe 86

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Lokacin daya aje wayarsa mai gadin da yake zaune kusa dashi yace cikin zolaya.

Wacece wannan ta faÉ—a komar ka dan Alhaji? kuma ga dukkan alama tarko ya kama kurciya.

Hahahah kai dai bari Tijjani, wata me zafi na samu wlh ganin farko nayi mata naji bazan taɓa bari ta kuɓuce mini ba, kasan 'yan matan yanzu sai ana yi musu ƙarya kafin kake samun kansu, wannan ta aure ce bata yaudara ba.

Kace dai Allah yayi aure yazo mu huta da surutu, wataƙila inka aurenta ka rufe ƙofa 'yan mata ma zasu huta da yaudararka.

Gaskiya inna auri wannan zan daina komai na kama aikina dan na auri matar data kere sa'a.

Allah sarki Maman Jamila watan yi mata kishiya ya kama.

To ya zata yi wlh sai na auri Najwa ko zata mutu, ba dan Mamanmu tana kwaɓata akanta ba ai da tuni na saketa na huta saboda shege ƙazantarta, gata bata ita girki ba balle iya rayuwar aure, kai auren mace 'yar sha bakwai zuwa ashirin matsalata ce basu iya komai ba sai shirme.

To Allah ya sa ka dace da wannan É—in mai tsafta ce.

Kai hmmmm wannan fa matar manya ce, nima da karyata zan samo kanta ta aureni dan wlh tafi ƙarfina fa.

Shege driver ɗan Alhaji, ai yau saura ƙiris ka rasa aikinka yadda alhaji yayi fushi da bai ga motarsa ba jiya.

Kai dai bari É—azun nasan ina ruwa kawai Allah ne ya fiddani saboda ina mugun shiri da Hajiya har ta goyi bayana, dalilin yadda nake koÉ—ata, kasan fa bakin nan nawa yasha ceto na.

Ai kai hmmmm, Allah yayi maka zarafin daÉ—in baki duk macen data faÉ—a komar ka sai Allah.

Kamar yadda nake tunanin Najwa ta faÉ—a ciki tsundum In Sha Allah aurenmu ba fashi.

Ya fada yana 'yar dariya, Tijjani ma dariyar yayi suka cigaba da hirar.

Asalin Mujaheed su 'yan jihar Gombe ne...
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

54.

Najwa tana fita ta ganshi a daidai setin gidansu a jikin mota ya tsaya yana kaɗa key, shigar ɗazun ce ta gani a jikinsa amma kuma da rantsastsiyar mota, ta saki wani murmushi dan ga dukkan alamu yanzu ne ta samu miji wanda take ganin yafi Aminu komai, kuɗi kyau da ƙuruciya gwanin birgewa, ta isa gareshi suka gaisa kana yayi mata tayin su shiga mota suyi hira, ba musu suka shiga ta zauna a gefensa, ƙamshin dake tashi a motar ma ba a magana wanda yasa Najwa lumshe ido ta buɗe, da alama wannan ɗan gaye ne tace a ranta, nan suka soma hira yana zabga mata ƙarya ita kuma tana gyaɗa kai tamkar mai haddar maganarsa. A lokacin ne baba ya dawo ya shiga gida yana mamakin ganin mota a ƙofar gidansa, ya zata baƙi suka yi dan motar tinted ce ga kuma duhun dare ba wutan nepa ba za'a gane da mutum a ciki ba, ya shiga yana cewa inna.

Motar waye na gani a ƙofar gida.?

Ɗazun nan Najwa ta fita ƙila kona baƙonta ne.

Amma ban ganta a wajen ba.

Ba mamaki ko suna cikin motar.

Ashsha! subhanallahi yaushe ta fara hira a mota? kinga Saleema ta ɓata tarbiyyar yarinyar nan ko.

Yace cike da faÉ—a ya fice waje, yana isa jikin motar ya kwankwasa sai Mujaheed ya sauke glass Najwa tayi saurin cewa.

Baba na ne.

Ke dan gidanku hira kike yi a mota maza ki fito nan Shashasha.

Najwa jiki na rawa ta fito baba ya nuna mata hanyar gida suf suf ta wuce, Mujaheed ya sunne kai yana bawa baba haƙuri baba yace.

Yaro ban yarda da hirar mota ba, domin in dai kai ɗan mutunci ne ba zaka so a yi hira da ƙanwarka a mota haka ba, dan haka daga yau karna ƙara ganin haka, kuma in da gaske kake yi ka fito bana son ka ɓata mata lokaci.

In Sha Allah baba zan gyara kuma da gaske nake da zarar mun fahimci juna zan yi mata magana na turo manyana.

To hakan yayi sai ka gaida gida.

Baba ya faɗa yana juyawa, Mujaheed har cikin ranta yaji daɗin yadda baba yayi masa, hakan ya bashi tabbacin gidan akwai tarbiyya, sai ya ƙara samun kwarin guiwa tare da ganin ya samu mata sai inda ƙarfinsa ya ƙare, sai ya ja mota cike da tsantsar farin ciki ya nufi gida.

Najwa kuwa tana shiga gida ta shige É—akin inna tana cewa.

Inna kinga Baba ya koro ni dan kawai ina hira a mota.

Yayi mini dai dai wlh ai kema kin san ya hana ki hira a motar saurayi.

To amma ai ba wani abin zanyi ba kuma wlh mutumin kirki ne shi.

Mutumin kirkin gidanku, kaga 'yar banza ana nima miki mutunci kina turewa, to daga yau inna ƙara ganin kin yi hira a mota zan baki mamaki, naga ma iskancinki gaba gaba yake yi, to zan saka ƙafar wando ɗaya dake.

Cewar baba da ya shigo ya tsinkayi maganar Najwa, sai tayi mukus ta ƙi cewa komai dan tasan halin baba ba wasa, inna ma ta ɗaura da nata faɗar baba ya wuce yana cewa.

Gwara dai ki mata faÉ—a taji, in ba haka ba ta saka tsiya na bada ita sadaka. Dan lamarin ta ya fara isata.

Sai ya shige ɗaki Najwa dai ƙunƙuni take yi a dole bata son faɗar, inna ma sai da ta gaji da faɗar dan kanta tayi shuru. Tun daga wannan ranar kusan kullun sai Mujaheed yazo hira amma yafi zuwa da yamma saboda a lokacin ne yake da damar fita da motar gidan da yake driver, Najwa kuwa ganinsa da mabanbanta motoci yasa ta ƙara dulmiyar da zuciyarta akan ƙaunar aurensa.

***

Bayan wata guda da sati biyu da haɗuwarsu Mujaheed ya turo manyansa aka yi maganar aure, wanda aka saka wata biyu mai zuwa. Musamman baba ya saka Junaid akan ya je ya bincika wanene Mujaheed domin kar a kuma yin aure irin na Aminu duk da shi wannan ya bayyana kansa, Junaid ya tambayi Mujaheed ranar daya zo hira sunan unguwarmu, bai musa ba ya faɗi sunan unguwar gidan da yake aiki bai kawo ko bincikensa zasu yi ba, a nan ne Junaid yaje unguwar ya yi bincike har ya gano asalin Mujaheed ɗan abakwa ne, da gidansu da komai sai da ya binciko nan ya gane duk zancen daya ji Najwa tana faɗawa inna cewar mai kuɗi ne ƙarya ne amma sai yayi muƙus bai faɗawa baba asalin bincikensa ba ya ce masa ya bincika mutumin kirki ne kuma yana da sana'a mai kyau, domin yana so Najwa ta aureshi ta hakane zata gane kurenta ta ragewa kanta dogon buri ƙila hakan zai sa ta gyara zuciyarta.
Chapter 86 · 0% Book details