← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 98

Sashe 59

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama faɗar haka ya fito daga ɗakin ya zauna a falo tare da dafe kansa da duk hannunsa biyu, damuwa sosai ya shiga kan yadda ranarsu ta farko a gidan aurensu ya kasance, yadda yasan Ikram tana sonsa ya tabbatar ba ƙaramin abu bane yasa ta yi masa haka, kuma yasan tana da tarbiyya musu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, haka ya zauna zaman jiran isowar su Ibrahim. Itama Ikram zama tayi a bakin gado tana matsar kwalla dan ta rasa yadda zata danne halin da take ciki ta ɓoyewa Shamsu, shiyasa ta kasa controlling kanta kamar yadda Sameeha tace karta nuna masa komai ta bar komai a hannunta, haka kowannensu ya zauna cikin damuwa har zuwa sadda suka ji hon ɗin motar Ibrahim a gate, hakan yasa Shamsu yayi saurin fita lokacin mai gadi ya buɗe musu sun shigo, Ibrahim yayi parking suka fito Shamsu ya ƙaraso yana yi musu sannu da zuwa cikin ladabi, suka amsa kana suka shiga cikin falo suka samu wajen zama Sameeha da Ibrahim a kujera mai zaman mutum uku suka zauna, sai Ikram da fitowar ta kenan ta samawa kanta guri a kujera mai zaman mutum ɗaya, Shamsu shi kuma ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu, nan Ibrahim ya soma magana yana cewa.

Shamsu ba ɓata lokaci za muyi ba saboda dare, ina so ka duba wannan saƙon kayi nazari akan waye ko wacece zata yi maka irin haka.

Yayi maganar yana miƙa masa wayar Ikram daya amsa a hannun Sameeha, Shamsu ya taso ya amsa ya koma ya zauna ya soma karanta saƙon cike da tsantsar mamaki a fuskarsa, ya ɗago ya kallesu bayan ya gama karantawa ya ɗaura da cewa.

Yaya ni ba ni da wani maƙiyi dana sani a zahiri da zai yi mini irin haka, ashe shine dalilin da ya sa Ikram ta rikice mini, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.

Ya ambata yana mai dafe kansa da hannu bibbiyu domin saƙon ya kaɗa shi sosai kuma bai ga laifin Ikram ba domin saƙone da yake da tashin hankali a ciki, musamman ita da take a matsayin matarsa da aka ɗaura aure yau yau, Ibrahim yace.

Shamsu kadai zurfafa tunaninka akai ƙila ka taɓa samun sabani da wani ko wata yace bari ya biyo ta wannan hanyar domin ya rama, abokin aiki ko budurwa, duk da ni ban yarda ka aikata ba saboda nasan tarbiyyarmu wlh ba zaka taɓa ɓata sunan ahalinmu ba wannan shirri ne dai.

A zabure Shamsu ya muskuta ya É—ago kai yana cewa.

Tabbas mace ɗaya ce nasan ƙila ta iya aikata haka saboda zafin da taji na auren Ikram da nayi, saboda budurwa ɗaya nayi a nan Kaduna sai Ikram dana aura yanzu, sannan ita wancen da kanta ta koreni tace ba zata iya aurena ba saboda banda kuɗi.

Nan ya kwashe yadda suka rabu da Najwa ya basu labari tas kana ya cigaba da cewa.

A zahiri na ɓoye mata asalina ne domin nasan zata soni saboda Allah sai kuma ta faɗi jarabawar ta nuna kuɗi take so, ta kuma sallameni da kanta akan karna sake zuwa gidansu. Dalilin da zai saka tayi mini wannan sharri saboda Ikram na aura, zata ga kamar nayi hakan ne domin na ƙuntata mata, kuma na soma soyayya da Ikram bansan alaƙarsu ba daga baya ne na fahimci kuna da alaka a Najwa.

Najwa!

Cewar Ikram da ƙarfi, Sameeha ma tace.

Najwa kuma! Najwa Tamu dana sani ko wata daban.

Ita dai cousin ɗinku wacce take a badarawa, na tabbatar bata san nine na Auri Ikram ba sai yau shiyasa ta biyo ta wannan hanyar dan ta ƙuntata mini, ƙila a ganinta na auri Ikram da gangan ne dan na bata haushi, wannan hasashena ne kuma bincike shine zai tabbatar da gaskiya, ita kaɗai nake zargi a yanzu.

Ikram yau tunyaushe ne baki ƙara ganin Najwa a gidanmu ba, saboda na tuna ban ganta ba tun yamma dan bada ita aka kawo mu gidajenmu ba.

Ai ni rabona da ita tun lokacin da aka fito É—aukar hoto dasu Shamsu suka shigo gaisuwar iyaye bayan É—aura aure.

Cewar Ikram tana yawo da idanunta kamar mai tunani, Ibrahim yayi murmushi domin shima zarginsa ya faÉ—a akan Najwa sai yace.

Da alama ita ce dan na tabbatar a wannan lokacin da muka shiga gida ta ga kaine mijin Ikram yasa ta bar gidan, kuma ta yi amfani da wannan damar dan ta lalata tsakaninka da Ikram, dan haka yanzu ta ina zamu tabbatar mu gano da ita É—in ce ta aikata haka.

Murmushi Shamsu yayi yana cewa.

Ku bani number É—inta yanzu na kirata da dayan layina da ba tada shi, yanzu gaskiga zata yi halinta.

Cewar Shamsu, nan take Sameeha ta buɗe wayarta ta karanto masa number ɗin Najwa ya saka a wayarsa ya soma kira, Najwa a cikin barci taji karar waya hakan yasa ta farka ta duba wayar taga number ne har ya katse bata iya ɗauka ba ta mayar da wayar ta aje, sai ga wani kiran ya sake shigowa cikin gajiyawa da ƙarar tayi saurin ɗaukar wayar ta kara a kunne ba tare da tayi magana ba.

Hajiya Najwa halan kina barci na tashe ki, kiyi haƙuri kamawa tayi da fatan kin gane me magana.

Shamsu yace bayan ya saka kiran a handsfree yadda zasu ji komai, Najwa ta tashi zaune dan ta gane Shamsu ne amma saboda tayi masa wasa da hankali tace.

Ban gane me magana ba.

To Shamsu ne mijin Ikram, na kira ki ne na baki haƙuri akan hukuncin da kika shirya ɗauka a kaina, saboda kin turawa Ikram saƙo gashi ta rufe mini ɗaki tana ta cin mutumci na akan haka, a takaice gani zan kwana a mota dan ta fusata sosai ina tsoron kar dare yayi tayi mini wani illa in barci ya ɗauke ni.

Hmmm ni ban fahimci inda ka dosa ba.

Najwa ki nasan fa kin san komai ba sai mun tsaya muna wasa da hankulan juna ba, na tabbatar sai yau ne kika san nine mijin da Ikram ta aura, domin É—azun na ganki a gidansu kuma tsakani da Allah bansan Ikram 'yar uwarku bace sai da aka gama zancen aurenmu da ita, lokacin take faÉ—a mini kema an saka bikinki to a cikin hira take faÉ—a mini inda kike har na gano ke ce, kuma in zaki yi mini adalci kece kika koreni dan haka bai dace ki hukunta ni ba.

Hmmmm amma ka rasa wacce zaka aura sai 'yar uwata saboda kaci mini fuska ko, meyasa daka gano nice Najwa 'yar uwarsu baka fasa auren ba.

Amma kin san an saka ranar aurenki hakan ya ƙara mini ƙarfin guiwan dana cigaba da niman Ikram, Najwa kinsan ina sonki kuma bazan taɓa son wata mace sama da ke ba amma kika koreni, na rasa me ye makusa a jikina kika yi mini haka.

Meyasa zaka ɓoye mini asalinka? Meyasa ka ɓoye mini komai naka ka muna mini kai talaka ne.

Saboda na gwadaki ne na gane zaki so ni domin Allah, sai kuma baki kaiga cin jarabawata ba kika ma koreni, ni dai yanzu ki faÉ—a mini me kike so a gareni domin ki wanke ni a gun Ikram, dan sosai kika haddasa husuma a tsakaninmu.

Yanzu kana mufin Ikram ta kulle maka É—aki a mota zaka kwana?

Allah kuwa, yanzu ina tunanin kona je na kama hotel ne, ni ina so ki faɗa mini me kike buƙata da zai wanke laifina a gunki ki wankeni a gurin Ikram dan Allah.

Ko meye nace ina so zaka yi mini shi?

Najwa ta faɗa cikin jin daɗin hakkarta ta cimma ruwa, Shamsu yace cikin sanyin murya dan ya ƙara karya mata zuciya.

Eh in dai baifi ƙarfina ba.

To ina so nima ka aureni.

What?

Ya faɗa da ƙarfi su Sameeha ma mamaki yasa suka zazzaro ido waje domin tun sadda suka fara magana zuke mamakin Najwa, Najwa ta ce cikin 'yar dariya.

Eh ko ba zaka iya aure na ba ne? to hakan shine zai wanke laifinka a guna kuma shine zai sa na numa ma Ikram cewar bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane.

Taya hakan zai yuwu? Keda ake shirin yin aurenki, sannan me Ikram tayi miki da ta cancanci haka a gunki.

Hmmmm saboda ta aureka shine laifinta, sannan kuma idan ka yarda da aurena ni nasan yadda zan saka a fasa aurena da wancen.

To shikenan zanyi tunani akai amma kinsan dole zancen aurenmu zai É—auki lokaci saboda yanzu ne nayi aure.

In dai ka amince to ko nan da shekara É—aya ne zan jiraka, sannan ka aje batun zaka yi tunani idan ba haka ba wlh sai na cigaba da kunna maka abubuwan da sai kayi dana sanin auren Ikram. Sannan ko kaje ka faÉ—a mata nice nayi mata sako ba zata yarda ba saboda sun yarda dani kuma ina da hanyar wanke kaina.

To hajiya Najwa nagode Allah ya saka da alkhairi da kika warware mana zare da abawa, ga yaya Ibrahim da Anty Sameeha dama Ikram duk suna jinki kuma suna gaisheki da jan aiki.

Shamsu ya ƙare maganar yana 'yar dariya, a zabure Najwa ta tashi ta zauna tana jin wani gumi yana damunta, bata taɓa zaton gadar zare ya saka mata ba, tace cikin ƙara ji.

Me kake nufi da zancenka Shamsu?

Hanyar da kika bi nima shi nabi na gano gaskiyar abinda kika haÉ—a, Ikram ga 'yar uwarki kuyi magana.

Ya kare maganar yana miƙawa Ikram wayar, Ikram tace cikin sanyin murya.

Ni babu abinda zan iya ce mata taje ita da Allah.

Najwa kin kyauta Allah ya shiryeki.
Chapter 59 · 0% Book details