← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 98

Sashe 79

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Najwa tace to amma a zuciyarta tana mamakin rashin karan da Malam ya nuna mata ƙarara, haka suka bar falon Saleema jikinta a sanyaye dan taji kunyar maganganun malam ga Najwa, suna fita Saleema ta kira Yaya domin ta sanar dashi malam ya yarda da zaman Najwa sai dai harya ringing bai ɗauka ba, da suka isa sashinsu ne ta kuma kira shine ya ɗauka take sanar dashi komai yace ba damuwa kana ya sanar da ita an kwaso kayan Najwa ɗazun.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

49.

Su Saleema suna fita daga falon malam, sai É—aya daga cikin mutanen dake falon yace cikin sosa kai.

Malam in ba damuwa ina da magana akan wancen yarinyar da suka fita yanzu, amma Allah yasa ba matar aure bace.

Malam sai da yayi 'yar dariya kafin yace.

Ina jinka Atiku faÉ—i maganarka kai tsaye.

Yauwa dama ina kamun iri ne idan ba matar wani bace, zan ƙara ta biyu da ita.

Atiku manya daga ganinta sai kaji kana son ƙara aure anya kuwa?.

Dama ina son na ƙara to har yanzu ban samu bane shiyasa, to yanzu ne na ga wacce ta dace dani dan sosai ta kwanta mini a zuciyata.

To madallah kuma kayi rasa akan gaɓa domin kuwa ba tada aure sakin wawane ko nace auren rana guda ne da yini aka sauta, saboda mijin baida lafiya ya ɓoye musu gaskiya, ko idda bai ɗaura mata ba.

Alhamdulillah gaskiya nayi farin ciki, ni dama nasan zuwa na nan alkhairi ne, ga cigaba na kasuwanci da nake samu bisa tallafin addu'o'inka gashi kuma zan samu mata. Allah yasa na samu karɓuwa a gunta.

In dai wannan ne zata soka dan bata isa in kawo miji ta ce bata so ba, tuni zan yi maganinta, in dai da gaske kake to ka bar mini komai a hannuna.

Nan Atiku ya shiga jero masa godiya kamar zai kwansa masa, malam ya gama aikin da zai yi musu ya sallame su akan zasu yi magana a waya. Suna fita malam ya yi duba akan Atiku da Najwa, nan ya hango aure zai tabbata kuma shima hanyar samunsa a jikin Atiku zai ƙara buɗewa dan ba ƙaramin morarsa yake yi ba, duk abinda ya gindaya masa na kuɗi baya taɓa kaucewa sai ya bayar, hakan yasa yaji dole ma Najwa ta aureshi dan ba zai yarda ya rasa wannan gwaggwaɓar samun ba.

****

Bayan kwana.

A Kaduna.

Sameeha mijinta ya kirata akan ta shirya zasu koma Abuja a ranar saboda akwai wani taro da za ayi ranar Alhamis wato gobe In Allah ya kaimu, kuma tarone na manyan mutane da matansu, to yana so Sameeha ta kasance tare da shi a wannan guri dan yasan ita É—in matar fita taro ce, hakan yasa dole ta shirya dan dama taso ta yi sati guda ne sai ta koma, tumi Ikram ta koma gida sai dai suyi waya, hakan yasa Sameeha ta kira Aminu kan batun yara, koda ya daga wayar suka gaisa sai ta É—aura da ce masa.

Abban Amrah dama na kira ka ne kan batun su Abi, Umma tace a gunta zasu zauna, shine nace bari na sanar da kai ko za a yi musu transfer ɗin makarantarsu zuwa nan Kaduna, tunda turkish school ne kuma nan ma akwai, ko yaya Zaidu zai riƙa kaisu makarantar.

Masha Allah naji daɗin umma da zata riƙe su, nasan sai ta fiki kulawa da su tunda ke kina fama da mijinki ga harkar siyasa da kuke yi, sannan batun kaisu makaranta akwai driver da zai dawo nan da motarsu in yaso zai cigaba da kaisu ina biyansa, dama ɗan nan Kaduna ne kinga ya riƙa barin mota a nan gidan da safe ya riƙa zuwa, sannan duk inda Umma zata da Anwar sai ya kaisu kinga ya zama drivern gidan gabaɗaya. In Sha Allah cikin kwanakin nan zanyi komai na makarantar nazo na kaisu nan turkish ɗin, sannan zan haɗo kayansu gaba ɗaya ma, tare da sauran abubuwan da suka dace.

Yayi maganar cikin fara'a fuska sake, murmushi Sameeha tayi jin zolayar da yayi mata a maganarsa ta farko, tace masa shikenan duk abinda ya yanke yayi dama ita yau zata koma Abuja, yayi mata fatan alkhairi sai suka yi sallama. Ba jimawa ya kira umma a wayarta bayan sun gaisa yake ce mata zai riƙa kiranta a waya suna gaisawa da kuma duk abinda ya shafi yaran ta riƙa faɗa masa yanzu ba yida mahaifiyar data fita, umma taji daɗin haka ta saka masa albarka tare da yi masa fatan gamawa lafiya, nan ta bawa su Abi wayar suka fita suna waya da babansu, Umma ta kalli Sameeha tana cewa.

Wlh Aminu mutum ne, banda ƙaddara ta rabaku da zanso ya cigaba da zama sirikina, yana da kirki dan tausayi ma yake bani yanzu,Allah dai ya bashi lafiya ya warke ya samu mata tagari ya aura.

Ameen umma ni ma kaina fatan lafiya nake yi masa kenan, domin a yanzu ina yi masa kallo tamkar É—an uwana na jini.

Allah ya rabamu da mummunar ƙaddara, da ace Najwa ta kirki ce da in ya samu lafiya sai ya mayar da aurensu.

Haba umma wlh bana masa fatan Najwa, dan a yanzu haka ina masa kwaɗayin auren ƙanwar Shamsu wanda suke uba ɗaya, in har Aminu ya samu lafiya kuma bata yi aure ba wlh ita zan nima masa ya aura, yarinyar ga hankali ilimin addini da sanin ya kamata, ta kammala jami'a yanzu tana koyarwa a nan Nuhu Bamalli poly dake zaria, itama ƙaddara ya rabata da mijinta sanadin auren da ya ƙara yaranta biyu.

Allah sarki kinji kowa dai da irin ƙaddararsa, zan so hakan ya faru kuwa, amma karki faɗawa kowa tukuna sai mun tabbatar da ya samu lafiyar ni da kaina zan shiga gaba wajen nima masa aurenta nasan Aminu zai yi mini biyayya.

Murmushi Sameeha tayi tana gasgata maganar umma dan sosai taji daɗin yadda ta amsa maganar, haka suka cigaba da hira har zuwa lokacin da Ibrahim yazo ɗaukarta ya shigo har gida ya gaisa da umma kana ya bar musu maƙudan kuɗi kamar yadda ya saba, shima yaso umma ta bar musu yaran dan sunyi maganar da Sameeha amma tunda umma ta hana dole ya bar maganar, haka suka tafi su Abi suna yi musu bye bye.

*

Abuja.

Bayan sun isa Sameeha ta É—aura musu girki, Ibrahim yazo ya tsaya a bayanta yana cewa.

Gaskiya yau matata ba zata girka komai ba, shiryawa za kiyi muje muci abincin waje, saboda akwai aiki na musamman da za kiyi anjima kinga in kin gajiyar da kanki yanzu aikin anjima bazai samu yadda naje so ba.

Sameeha ta juyo tana fuskantarsa É—auke da murmushi.

Mahboob É—ina yau da kanka zaka ci abincin waje, ni dai ka barni na samu lada biyu na yanzu da kuma anjima.

Naƙi wayon muje ki shirya mu fita dan gaskiya ina son more soyayya ne yau, nayi kewarki kwana biyu so badly.

Ya ƙare maganar yana jan dogon hancinta ita kuma matsowa tayi tayi masa kiss a kuncinsa kana tayi masa a wuyansa, wanda ya saka shi sakin wani ƙara sai ta zame ta ruga a guje yabi bayanta yana cewa.

Ai tunda kika fara kunna ni tun yanzu zan bankaÉ—a asirin soyayyarmu.

Haka suka dinga zagaye falon suna dariya da junansu, saida Sameeha ta gaji kana ta zube a cushing tana mayar da numfashi, shima ya dawo gefenta ya zauna tare da cewa.

Wa na kama.

Ni, amma dan Allah karka mini komai muje muyi wanka mu fita nima ina muradin shaƙar iskar waje tare da gaurayyen numfashin mijina a kusa dani.

Ta ƙare tana kanne masa ido, murmushi yayi wanda ya bayya kyawun fuskarsa.

Allah yayi miki albarka Haskena ina alfahari da samunki, ban taɓa zaton aure yanada farin ciki da natsuwa ba a duniyarmu ta Hausawa ba sai dana sameki nasan haka, Sameeha na tabbatar samun irinki a duniyar nan sai an tona, duk da ina busy ina harkar siyasata amma wlh inna tuna dake sai naji babu gajiya ina samun kwarin guiwar gunadar da komai cikin salama.

Wannan shine fatana a kullun ka kasance cikin farin ciki, ni baiwarka ce, masoyiyarka ce, sai yadda kayi dani domin zuciyata da gangan jikina mallakinka ne, ina sonka Ibrahim.
Chapter 79 · 0% Book details