← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 98

Sashe 36

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aminu bayan sun isa gida yace Driver ya zo da wuri zai tafi da kaya Abuja da safe, yace to kana ya tafi da motar dan ya ƙara shan mai da ita. Aminu suka shiga ciki, yace su jirashi a falonsa ya shiga ɗaki ya watsa ruwa ba jimawa ya fito sanye da jallabiya, ya buɗe ɗakin Sameeha yaga wayam sai da yaji ciwo a ransa bai yi zaton zata yi saurin kwashe kaya ba, damuwa ya kewaye illahirin zuciyarsa ya jawo Kofar ya wuce kitshen nan ma ya tadda ba komai falon ba komai dama a falonsa yaran suka zauna. Sai ya ɗibesu a motar da ake kaisu makaranta suka fita suka ci abinci a wanu restaurant, basu suka dawo ba sai bayan ƙarfe goma Amrah ma har tayi barci, ya kaita ɗakinta ta kwanta kana ya soma haɗa musu kaya Abi yana taya shi dan yaƙi barci saboda Aminu yace masa zasu haɗa kayansu gobe In Sha Allah da wuri zasu tafi Abuja dan ba zai barsu a nan kaduna ba. Sune har ƙarfe sha ɗaya suna abu ɗaya, Aminu yace Abi ya kwanta da safe zasu cigaba, haka ya lallaɓa yaron ya kwanta a ɗakinsa kafin ya fito ya cigaba da haɗa musu kaya dan ko barci baya ji duk da akwai gajiya a jikinsa, amma damuwar da yake ciki yasan ba zai barshi yayi barci ba, sosai yake ji dama bai saki Sameeha ba amma kuma in ya tuna a yadda ya gansu sai yaji sakin shine mafi alkhairi, trolley huɗu ya cika na kayansu, sai gana mazgo na littafai da takalma, bashi ya kwanta ba sai gurin ƙarfe biyu shima sai da yasha wani kwayar magani mai saukar da gajiya da kuma saka barci, ba jimawa barci ya ɗauke shi.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

24.

Gari yana waye wa driver yazo ya loda kayansu Aminu a mota dan ba ƙaramin kaya ya ɗibar musu ba, da nufin sun bar Kaduna kenan sai dai su riƙa zuwa suna sada zumunci. Driver ya tafi da kayan dan su jirgin kasa zasu bi, Aminu ya saka suka yi wanka dan har Amrah ta iya sai dai ya tayata shiryawa suka fito gabaɗaya da nufin a hanya zai siya musu abinda zasu karya da shi, Aminu sai da ya sauke wutar sashinsu gaba ɗaya ya kashe komai ya dawo ya rufe ɗakuna kana ya rufe ƙofar falo. driver mai kai su Abi makaranta dama yazo tun ɗazu akan kiran da Aminu yayi masa sai suka shiga mota ya kai su bakin gate, Aminu yace ya tsaya ya fito mai gadi ya risina yana kwasar gaisuwa Aminu ya miƙa masa dubu biyar yana cewa.

Wannan kuÉ—in kaje a buÉ—e maka account da komai, domin ta nan zan dinga tura maka albashinka duk wata, sannan idan kana da iyali zaka iya É—auko su ka saukesu a É—akunan dake can baya ku zauna a nan kafin Allah yasa in dawo. Wannan kuma dubu arba'in ne gasu.

Alhaji kuÉ—in na menene?

Albashinka ne na ƙara maka na wannan watan domin ka ƙara siyan abinci da komai tunda dama a cikin gidan ake baka na rana da na dare.

Nagode Alhaji Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki, In Sha Allah yau zanje in bayar a buɗe mini asusun banki sai na saka a tura maka numbobin.

Aminu yace Masha Allah kana ya wuce ya shiga mota suka wuce, mai gadi sai juya kuÉ—in yake cike da tsantsar murna da tunanin yadda sai fara kashe su, har motarsu ta kusa fita Aminu ya kwala masa kira, sai ya isa da sauri ya risina.

Gani yallaɓai.

Yauwa ina so naja kunnenka ka kula da gidan nan da zarar ciyayi sun fara fitowa ka faɗa mini sai na tura maka kuɗi ka samu masu gyara suyi, karka riƙa barin gidan yana datti. Kuma daga 'yan uwana duk wanda yazo karka barshi ya shiga mini gida, nasan dai su yaya Kamalu ba zasu zo ba, amma su Hauwa ban yarda ka buɗe musu gida ba tunda kasan dai ba kowa a gidan.

In Sha Allah zanyi yadda kace Allah ya saukeku lafiya sai kun dawo.

Sai Aminu ya É—age gilas É—in motar na baya driver ya jasu suka wuce. Mai gadi ya ja gate ya rufe da kwaÉ—o ya koma ya zauna a benci yana lissafin yadda zai je kauyensu ya É—auko matarsa ko kuma ya kirasu su kamo hanya, amma sai ya nima 'yar katifa wacce tafi na É—akinsa ya saya da É—an kayan amfani.

****

Babban Gida

Da safe Alhasan ya fito zai je wajen Kamalu suyi magana, Laure ta fito daga ɗaki fa biyoshi tana ƙara bashi haƙuri akan abinda ya faru jiya, dan ta samu da kyar ya mayar da ita aka Kawu Lawal da ya zo ya saka baki dole ya mai da ta. A fusace ya juya yana cewa.

Wai da banyi haƙuri ba zan mayar dake ne, karki dameni, idan kin so ki cigaba da yi mini iskanci dan Wlh aure ma zan ƙara na huta da damuwar da kike ƙunsa mini.

Aure fa kace Alhasan.?

Laure ta faɗa tana dukan ƙirjinta, Alhasan ya gyara tsayuwa yana cewa.

Kuma budurwa zan nima yadda zan yi kara'i da kyau.

Yana gama faɗar haka ya wuce ta yana 'yar dariya a ransa dan yasan ya kaɗa mata 'yan hanji dole zata shiga hankalinta, tunda mace komin tsufarta bata ƙaunar kishiya, ita kuwa daskarewa tayi a tsaye ta kasa kwakkwaran motsi dan sosai maganar nashi ya kashe mata jiki, daga bisani taja kafa zuwa ɗaki tana jin babu daɗi a ranta, ta san dai tabbas ta kai Alhasan bango tunda tana sane da bata kyautata masa, lokaci yayi da zata gyara tun kafin ya aiwatar da zancen kishiyar da yace zai yi mata. Alhasan kuwa magana suka yi da Kamalu akan ɗauko yaran da Hauwa tayi, yace zasu je gidan Hauwa su kwashi yaran su mayar dasu gidansu Sameeha, dan ya samu labari bata mayar da yaran ba, suna cikin maganar Aminu ya kira Alhasan a waya, ya ɗauka suka gaisa kana Aminu yace.

Dama na kira ne na sanar daku na dawo daga kano jiya to yau kuma na wuce Abuja, sannan na karɓi yara a hannu Hauwa yanzu haka dasu zan tafi.

Amma Aminu bai dace lokaci guda ka raba yaran nan da mahaifiyarsu ba, da ka basu lokaci itama ta samu natsuwa sosai, yanzu haka maganar nake da Kamalu kenan akan zan kwashe yaran a gidan Hauwa na mayar dasu.

Ai yaya zan buƙaci yaran su kasance tare dani, dan har mun kama hanya ma yanzu sai dai zamu riƙa zuwa hutu.

To waye zai kula dasu kai kana fama da aiki, ga kuma makarantarsu da suka fara anan

Yaya zan sauya musu makaranta kuma zan samu mai kula dasu, In Sha Allah ba zasu yi maraicin uwa ba.

Kenan babu zancen yin aure kuma ko? Aminu dan Allah kar ka fara rayuwar da zai lalata rayuwar ka.

In Sha Allah zan kula, kuma ba Hauwa tace ta sama mini mata ba, ita nake saurare naga irin zaɓin nata.

Kai ka yarda da zancen wannan mahaukaciyar ne, aini sam ban saka Hauwa cikin masu hankali, ayi mace sai kace tinkiya uwar tamɓele.

Aminu sai da ya murmusa yace cikin dakiya.

Yaya ina ganin tunda har ta faɗa a bata dama wata ƙila a dace.

To Allah ya kyauta ya tsare hanya.

Aminu yace Amin kana yace ya sanar da Kamalu yadda suka yi, Alhasan yace ba damuwa sai suka yi sallama ya kashe wayar. Nan Alhasan ya faÉ—awa Kamalu yadda suka yi Kamalu yace.

Tunda haka ya zaɓa ai shikenan kiga ma baya nan za ayi bikin Salma, Aminu fa ta sauya sai dai mu bishi da addu'a.

Allah ya kyauta Alhasan yace kana suka cigaba da tattauna bikin Salma da za ayi ranar juma'a.
...

Ranar laraba aka fara shagalin bikin Salma wanda ranar Alhamis zasu yi sister eve, Hauwa tace ya kamata suje gidan Aminu suga yadda gidan yake kafin su aika masu kanofi su jera kujeru, ita da Laure suka je dan tuni ta sake suka cigaba da sabgar biki, ko da Hauwa ta kawo mata zancen Sameeha cewa take ai ba ruwanta tunda sanadin Sameeha aka saketa ko sunanta bata son ji, Hauwa dariya tayi tace ta dai tsorata ne kuma ma tunda bata gidan Aminu yara basa hannunta ai zancenta ya shafe kuma sun rufe babinta. Koda suka isa gidan sun samu a rufe suka buga mai gadi yace waye ba tare daya buÉ—e ba.

Dalla malam buÉ—e mana ko baka gane Hauwa bace yayar mai gidan.

To wlh yallabai yace karna bar kowa ya shiga masa gida, dan haka ku koma inda kuka fito.

Kan kaza kazanka ko baka gane da waye kake magana ba.

Hauwa tayi magana tana ƙunduma zagi, Mai gadi bai kuma magana ba ya koma ya zauna, suka cigaba da buga ƙofa suna zage zage yana jinsu yaƙi tanka musu. Haka suka gaji dan kansu suka tafi, tun a hanya Hauwa take kiran Aminu yana gani amma yayi banza da ita dan yasan dalilin kiran, ba zai taɓa yarda suyi Wani biki ba su ɓata masa gida dan yasan halinsu. Zage zage Hauwa da dinga yi har suka isa gida wanda Salma da ta ji abinda ya faru tace.

Ni Ban ga abin ɗaukar zafi ba tunda nan gidan ma yana da fadin, sai muyi abinmu a nan gida ba karya ba karairayi, kuma yana da gaskiga tunda yasan irin ɓarnata masa gida da akayi lokacin dawowarsu, dan haka banji haushi dan ya hana muyi taro ba.

Ai dama ke baki da zuciya tunda har kin samu damar kare shi, muna nima muki mutunci amma kina iskanci, yanzu baƙin naki a nan zaki sauke su.
Chapter 36 · 0% Book details