Sashe 42
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummulkairi kenan ɗiyar Alhaji Aliyu Turaki da Hajiya Aisha 'yar Saifullahi Wazirin Zazzau, su asalin 'yan zaria ne kuma Hausa Fulani aurensu haɗin zumunci ne su 'ya'yan abokai, wanda suma ɗin suna son juna dalilin da yasa iyayansu suka haɗasu. Aliyu ya samu karatun zamani sosai sannan yana da ilimin addini dan mahaifinsa malami ne wanda yake limamin gidan sarki, sannan shima Aliyu kafin ya bar zaria ya cigaba da limanci a masallacin bayan rasuwar mahaifinsa. Ya samu sunan Turaki ne kasantuwar ya gaji sunan kakansa, kasuwanci ne ya baro shi zaria ya yada zango a kaduna, a nan ne Allah ya nufa arzikinsa yake, domin ya shahara saboda company fulawa da yake da shi, semo, gishiri taliya dama kuma wani company daban na yin shinkafa. Yaransu biyar, Amina itabce farko tana aure a Abuja mijinta babban ɗan siyasa ne ya riƙe mukamai da dama daga bisani yayi retire ya cigaba da kasuwanci, yaranta bakwai ta aurar da huɗu saura uku, Sai Aisha ita tana aure a Yobe yaranta biyar ta aurar da biyu, sannan Ibrahim khalil shi yayi auren farko da 'yar ƙanwar Hajiyarsu mai suna Mubeena sai dai Allah ya yi mata rasuwa a gurin haihuwarta na farko, sai da ya shekara biyar kafin ya ƙara wani auren shima bisa matsawar da 'yan uwa suka yi masa da kuma takura shi da Nabeela ta yi saboda tana mutuwar sonsa, ita 'yar hanshaƙin mai kuɗi ne dan babanta ya riƙe mukamin Ministan kuɗi a wancen zamanin baya, sannan ya rasu ya bar musu dukiya wanda shine take juyawa take harkan business ba kama hannun yaro, matsalarta tafi martaba kasuwancinta fiye da aurenta duk da tana mugun sonsa amma harkan kuɗi ba tada sauƙi, plaza ɗinta biyu ɗaya a Abuja ɗaya a nan Kaduna. Lokacin Ummulkairi shekarar ta biyar da aure har ta yi haihuwa biyu dan lokaci guda aka yi aurenta da Ibrahim tana gama secondary ita da Mubeena aka yi musu aure sai dai Alkah ya rubuta Mubeena ba zata yi tsawon rai ba, khairy a ƙasar Sudan ta cigaba da karatunta har ta haɗa digree, saboda mijinta Ahmad a can ya yi karatu a matakin ƙarshe aka yi musu aure ya tafi da ita, yana gamawa ya samu aiki sai ya nima mata makaranta ta soma, basu dawo Nigeria ba sai a lokacin bikin Ibrahim da zai auri Nabeela wanda ta ƙare karatunta shine Ahmad ya aje aikinsa suka dawo gaba ɗaya. A lokacin Ibrahim yana ɗan majalisan jiha saboda shi tunda ya girma yake ƙaunar harkan siyasa shiyasa ya kama ƙafa da mijin anty Amina saboda yana da mutane sosai domin shima ya yi harkan, kuma ya samu goyon baya dan da farko Hajiya taso taƙi yarda amma data ga ya dage sai ta bishi da addu'a. Mahaifinsu ya rasu shekara uku daya wuce wanda mutuwarsa ya girgiza su dan ba wani ciwo ya yi ba daga ciwon kai ya kwanta sai dai suka same shi ya cika, sunyi kukan rashin sa daga bisani suka ɗauki dangana. An raba musu gado mai tarin yawa dan ko wannansu sai da ya samu kuɗi da gidaje. Anty Amina ta sayarsa kadarorinta ta gina gidajen mai ta buɗe wanda duk in aka ga AA Turaki petroleum and gas nata ne, Anty Aisha itama sayar da nata kadarorin tayi ta haɗe kuɗinta ta gina plaza, duk wani plaza da yake amsa AATuraki Plaza nata ne dan a plazanta ne Khairy take da shago a kasuwar gari, ita kuma Khairy wannan shagon boutique da kuma makarantar dara buɗe sune nata sai gidan goda da take harkan kiyon dabbobi, Ibrahim kuma company fulawa ne ya zama nashi da gida biyu da kuma kudi, ya mayar da hankalinsa akan company, Autansu kuma company shinkafa ne nashi da kuma kuɗi da gida, Hajiya kuma gidan marayu ta buɗe da kuma islamiyya domin ya zama sakatul jariya ga mijinta, sannan tana da gidan gona da kuma gidan da suke ciki nata neda kuma kudi masu nauyi.
A lokacin da khairy ta ƙara samun yara biyu a sannan shima Ibrahim yaransa biyu duk maza, Haydar da ya 'ci sunan mahsifinsu sai Musa da yaci sunan mahaifin Nabeela suna ce masa Dady. Ibrahim bayan ɗan majalisan jaha ya ƙara tsayawa takarar ɗan majalisan tarayya na kasa sai dai bai samu ba, shiyasa ya haƙura ya cigaba da bunƙasa kasywancinsa dan har motoci yake sayarwa, shekarar data gabata ya tsaya takarar Senator ta Kaduna ta tsakiya wanda cikin hukuncin Alkah ya samu kujerar, watansa bakwai kenan akan kujerar Sanator, da yake shi mutum ne mai kyauta da son mutane wannan ne ya kaishi ga matakin cin nasara. Sai dai ya ƙara zama busy baya Abuja baya Kaduna, ko kuma ya fita waje dan wani aikin, yaso ya zauna a Abuja da iyalinsa amma Nabeela yaƙi saboda harkokin da ta ke gudanarwa a Kaduna, sannan bata fiye zama ba tana yawan fita kasar waje akan harkan kasuwancinta, ita fa muƙaminsa bai wani ɗaɗata da ƙasa ba dan burinta ta zama ta shahara an saka sunanta a cikin jerin matan da suka shahara da kuɗi, sai dai kullun nima take yi kuɗin sun ƙi haɗuwa yadda ya take so, dan ta raina wanda da take samu so take tafi haka dan da zata ganta a matsayin Ibrahim zata so, gashi ko Khairy da take zaune guri guda ta fita arziki da samun kuɗi saboda bata saka wa kanta son duniya ba kuma tana da godiyar Allah, balle a kaiga su Anty Amina da Aisha, wane ita ta kama ƙafarsu. Wannan buri na Nabeela yana damun Ibrahim ga dukiya da mulki duk ta samu amma ita hakan be mata ba a cewarta nashi nashi ne nata tana ne, shiyasa ya rabu da ita baya takurata saboda aure ne suke yinsa bisa tsarin boko da wayewa ba addini ba. Wannan rayuwar da Nabeela ta ɗaukarwa kanta yasa ta surewa 'yan uwan Ibrahim suka soma tsanarta saboda ba tarbiyyan gidansu bane duk da suna da dukiya da sarauta amma bai sa sun yada tarbiyyansu ba, domin sun fito daga tsatson malamai da kuma Hajiyarsu tayi matuƙar ƙoƙari wajen tarbiyyansu. Ko sha'aininsu bata zuwa sai ta ga dama muddun ya ci karo da nata hidimar kasuwancinta, bata zuwa gaishe da Hajiya sai tayi niyya kuma duk da gidansu manne yake dana juna har da ƙofa ma a tsakiya, hakan yasa suka dinga kawo 'yan mata daga cikin dangi akan ya ƙara aure yace shi ba zai ƙara ba, koma zai yi ba zai auri 'yar uwarsa ba yafi ƙaunar bare, sannan harkan siyasarsa ba zai bari ya samu lokacin mata biyu ba duk da akwai abubuwa da yawa daya rasa a gurin Nabeela dan hatta kwanciyar aure sukan ɗauki lokaci basu yi ba, to shi yana Abuja ita tana Kaduna sai abin ya matsoshi ne yake zuwa ya sauke nauyi, Allah yasa ma baya harkan matan banza duk da suna kawo kansu amma bai yarda ya kaune hanyar Allah shiyasa yake yawan yin azumin Litinin da Alhamis hakan har ya bi jikinsa.
Yau ma ya shigo Kaduna ne domin tattaunawar sirri da zai yi da wasu mutane da suka zo daga Lagos, shiyasa yaso sauke su a guest house ɗinsa amma yana shiga gidansa na unguwar sarki mutane suka fara gewaye gidan shiyasa ya yanke yin meeting ɗin a gidan dan baya so ya fita da mota wasu su bishi suga guest house ɗinsa inda yake ɓuya ya huta, mutanen tun biyar na yamma suka zo dama yayi musu oder ɗin kayan ciye ciye, Abinci ne ya bawa Khairy tayi saboda baya cin na waje gudun matsala dan kuwa yana da maƙila fili dana ɓoye, dan yana da matuƙar farin jini saboda kyautatawarsa ga mutane, shiyasa Hajiya take yawan yi masa addu'a sannan tana cewa ya kula da abincinsa kar ya riƙa zuwa restaurant yana ci saboda rayuwar yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, shiyasa yake burin ya ƙara aure ya samu matar da zata kula da shi da kyau. Ko a Abuja gidan Anty Amina yake cin abinci ko ta aika masa yara har gidansa su kai masa, a nan Kaduna kuma ko yaci a gidansu ko kuma ya sa Khairy ta dafa masa duk abinda yake so, idan kuma matarsa tana gari ya saka tayi masa duk da ba son girkin take yi ba, nata ma tafi sakarwa masu aiki amma da yake tana son farin cikinsa ganin baya takura mata yasa take tsayawa ta girka masa.
.
..
Khairy tana kai masa abincin ta juyo gida, bata zauna ba ta gabatar da sallar isha'i, da ta idar ta ci abinci sai ta É—an zauna a falo wajen goma saura ta kashe kayan kallo da wutan falon ta wuce É—akinta ta kwanta, sai da tayi waya da mijinta dake Lagos dan baya gari da suka yi sallama sai ta kunna data ta soma chating, ta yiwa Sameeha sallama sai dai bata online ta cigaba da hira da 'yan uwanta.
****
Sameeha.
Tana kwance a uwar ɗakan umma taƙi zama a waje suyi hira dan sam taƙi samun sukuni tunda Inna Rakiya ta zo da zancen Idrisa, Ikram ta shigo ta zauna gefen gadon.
Haba Anty ki fito ayi hira dake mana kin wani ƙunshe a ɗaki, ko dai dan maganar Idrisa ne yasa kika zama shuru shuru.
Hmmm wlh sam abin bai kwanta bini ba shiyasa duk bana jin daÉ—in komai.
Babu mai miki dole da in kince baki so. Kin san yanzu ma maganar Kuluwa suke yi, wai zasu yi musu haÉ—i ita da yaya Zaidu.
Kai dan Allah.
Sameeha tace tana tashi zaune dan maganar ya yi mata daɗi. Ikram ta mele baki tace a cikin ƙasa da murya dan kar aji.
Anty kamar basu dace ba, yarinyar kwata kwata fa shekara sha takwas, yanzu take gama secondary, ni zan so ya auri babba mai ilimi wacce tafi Najwa.