← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 98

Sashe 65

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ba saboda shi nake kuka ba domin koda na ganshi babu abinda naji a raina saboda ka gama maye gurbin zuciyata, ni 'ya'yana ne suka bani tausayi saboda ya rabani da su, ƙiri ƙiri tun da muka rabu ban sake saka su a ido ba sai yau, haka suma yaƙi bari suzo inda nake, Amrah ce ta saka ni kuma da zasu wuce take maganar in zo in ɗauke su.

Sauke ajiyar zuciya yayi yana cireta daga jikinsa ya juyo da kyau suna kallon juna yana cewa.

Nafahimta amma me zaisa shi yin haka bayan ba rabuwar tashin hankali kuka yi ba, ai ba a raba uwa da 'ya'yanta dan sai mutum yaji kunya, idan kinsan inda suke gobe In Allah ya kaimu sai driver ya kaiki ki gansu, in ya baki yaran sai su zo su zauna damu ni ba ni da damuwar haka.

Nagode nagode Mahboob É—ina kuma ni ba zan je ba domin in ya kula ina son ganin yaran zai nima muzguna mini, idan sun dame shi da kanshi zai kawo su.

Hakane, yanzu ina gani ki zauna bari na saka security su ƙarasa siyayyan'r dan bazan so ki fito haka ba.

Ina ganin ma a haɗa kayan da muka siya in yaso sai a aiko a ƙarasa siyayyar zuwa gobe in Allah ya kaimu.

Cewar Sameeha, nan take Ibrahim ya kira ɗaya daga cikin security ɗinsa ya bashi umarnin ya amso kayan da suka ɗiba ya haɗa masa da ATM ɗinsa, ba jimawa ya dawo suka saka kayan a bayan boot kana ya saka wani security ya jasu shi kuma yana maƙale da Sameeha a baya ya rungumeta suna duba wani abu a yawarsa, suna yi suna hira ƙasa ƙasa tare ɗan murmushi kan fuskarsu a haka suka isa gida. Sameeha sam ganin Aminu bai wani dameta ba saboda tana da Ibrahim daya maye mata gurbinsa, sannan ma a wasu abubuwa na rayuwar aure Ibrahim yafi Aminu gogewa da wayewa sosai, shiyasa komai in yana yi mata take ganinsa a sabo dan bata saba da hakan ba, yanzu ne dai take kokarin sabarwa kanta, yaranta sune damuwarta kuma sune burin da ya rage mata ta gansu kusa da ita amma ta kula Aminu ya ɗauki lamarin da zafi, amma dole zata zuba masa ido taga iya gudun ruwansa dan dole wata rana zai nimeta akan yaran.

****

Aminu.

Koda suka isa gida rigimar da Amrah ta saka masa yayi matuƙar bashi haushi har sai da ya kai hannu ya bige ta abinda bai taɓa yi ba, wanda in za a bincika zuciyarsa cike yake da haushin ganin Sameeha da wani ya haifar da fushinsa, ganin yadda ya daki Amrah yasa Abi ya natsu suf-suf ya shige falo ya barsu a farfajiya, ya samu baaba a ɗakinta ya sanar da ita komai, sai ta fito falon ta samu Aminu a zaune ga Amrah can gefe tana kuka, wajenta ta isa ta fara rarrashinta kafin ta ce su wuce ɗakinsu su rage kayan jikin su tana zuwa, sai da ta tabbatar sun wuce kafin ta duba Aminu rai ɓace tana cewa.

Kasan kana son mamansu ka saketa, ai da sai ka zauna da ita duk laifin da tayi maka, taya zata kuhunta yara da laifin da basu aikata ba, Aminu kada da son zuciya ya rufe maka ido ka riƙa aikata ba daidai ba, taya zata raba yara da uwarsu alhalin tana raye, duk da kun rabu wlh baku rabu ba domin yaran nan sun riga sun haɗa ku, idan kai ba zai yuwu kayi zumunci da ita ba to su bai dace ka shiga tsakaninsu ba, naga ma ƙoƙarin Sameeha data zuba maka ido har tsawon wannan lokacin bata buƙaci ka dawo mata da yara ba, in wata ce wlh kotu zata kaika tunda in Abi Musulunci ya baka ka riƙe shi ai Amrah musulunci ya bawa Sameeha damar ta riƙe ta har sai ta kai munzalin balaga, kayi tunani da kyau idan ƙanwarka aka yiwa haka ko ɗiyarka zaka ji daɗi ne, yau ko baram baram kuka rabu bai dace ka rabasu da uwarsu ba dan ba a sauyawa tuwo suna, uwa uwa ce ba a shiga tsakanin ɗa da uwa.

To Baaba In Sha Allah zan gyara.

Ya dai fi maka tunda kaga aurenka yana ƙaratowa sai ka kaisu can wajen mahaifiyarsu, mu mu tafi Kaduna ayi biki damu na yi zumunci da 'yan uwa, in yaso kaima sai ka samu damar ganawa da Amaryarka ba tare da takuran yaran ba, ni in an kammala biki zan komon nan Abujan na samesu, in ka dawo shikenan.

To baaba za a yi yadda kika ce, Allah ya kaimu lokacin.

Ta amsa da Amin kana ta miƙe tabi bayan yaran, shi kuma Aminu ya shiga mazarin maganarta, kuma tabbas yasan gaskiya ta faɗa amma a zuciyarsa bai so yaran su zauna hannun Sameeha ba, amma tunda Baba ta saka baki zaiyi haka ya huta tunda zai zamu damar yin bikinsa kuma shima zai zo Sameeha tasan aure zaiyi, hakan zai bashi damar ta gane ya samu lafiya taji haushi, wanda kuma lafiyar har yanzu bai samu ba yanata lallaɓawa ne da shan magunguna da aka ɗaura shi, wanda dai har yanzu ba wani sauyi.

A ranar da dare ya kira yaran yayi musu alƙawarin zai tura su gurin mamansu su zauna a gurinta saboda zai yi tafiya shi da baaba, a can zasu cigaba da zuwa makaranta, amma sai nan da karshen wata, sunji dadi sosai duk da ba a daɗe da shiga sabon wata ba dole suyi hakuri har lokacin tunda yayi musu alƙawarin haka.

****

Najwa.

Shirye shirye take yi sosai dan ta mayar da hankali kan bikinta, gashi an bugo kati tana ta yawon rabo ita da Nafeesa, wanda a cikin hakane suka koma gurin malamin nan ta bashi kuɗi akan yayi mata aikin da ko Aminu ya ga itace matarsa bazai yi mata wulaƙanci ba balle ya rabu da ita, malam ya tabbatar da aiki kamar yankan wuka haka zai yi mata, daga bisani suka wuce Nafeesa tana ƙara mata ƙarfin guiwa, wanda ita kuma a bayan fage tana ta tusa kanta ga Aminu, a yanzu har ta fara jan ra'ayinsa yana charting da ita duk da ba wani hira suke yi ba amma sukan ɗan taɓa hirar duniya, sannan ma yayi mata alƙawarin duk in ya shigo Kaduna zai zo su gaisa, kuma ya sanar da ita aurensa tayi masa fatan alkhairi da addu'a, ganin bata nuna masa komai ba kan batun aurensa yasa shi ƙara sakin jiki da ita, dan a tunaninsa ƙila sonsa take yi da take yawan matsa masa da waya ko text sai kuma yaga saɓanin haka.

Biki saura kwana biyu.

Aka kawo akwatin Najwa guda Huɗu da kit yaji kaya ba laifi su Hauwa sunyi kokari sosai sun gwangwaje Najwa, maza suka kawo akwatin hakan yasa babu wanda ya gane daga dangin Aminu ne aka kawo dan sai da suka kawo a daren jiya inna ta kira 'yan uwa yau suka zo ganin kaya ciki har da Umma, ta kira Ikram yazo tace ba zata samu zuwa ba saboda ta tafi gidan Khairy kuma ƙarya ne ba inda taje zuwan ne ba zata yi ba dan tace sai ranar ɗaurin aure zaje ita da Sameeha. A ɓangaren Najwa sam kaya baiyi mata ba yadda take so, amma ya zata yi tasan dai bata isa ta haɗa kanta dasu Sameeha ba, tunda ko ƙaramin zinari basu saka ba sannan babu key mota a ciki, kadaran kadahan ta nuna farin cikinta. A lokacin da Nafeesa ta zo ta gani sai da Najwa tayi mata ƙorafin akwati bai mata ba Nafeesa tayi dariya tace cewa.

Niko banga aibun akwatinki ba Najwa domin sunyi ƙoƙarin saka miki kaya masu tsada, ni da zan samu irin haka zan so wlh, Allah ya saka ni a damshin ki.

Haba haba wlh kiyi fatan naki yafi nawa, ai ni Hauwa ta bani mamaki duk cika bakinta bata saka kaya na gani na faÉ—a ba, yanzu haka Aminu ya bata kuÉ—i masu yawa ta coge wasu dan nasan halinta da mugun son banza.

Hmmm yau keda Hauwa za a ji kanku kenan, aiko sunyi ƙoƙari Najwa ki godewa Allah a haka.

Hmmm kina zaton yadda suka yiwa Sameeha haka zan zuba ido suyi mini, ai wlh mace tayi katdan duk ubansu zanci ki dai zuba ido kiyi kallo duk zan yi maganinsu, ba dai buƙatata ta biya ba to an gama magana.

Ohhh Najwa Duniya, wato kice shigo shigo ba zurfi kika yi musu dan ki cimma muradinki.

Hahaha Nice fa ake faÉ—a miki, kina zaton Hauwa ta yarda da aurena ne hakanan, hmmm to itama taga zata juyani ne yadda take so ne shiyasa ta dage da ayi auren domin cikar muradinta, saboda Sameeha ma turje musu data yi yasa suka tsaneta.

Lallai kice kowannenku yana da manufa a auren nan, to Allah ya baki sapa a kansu, dan wlh in kika yi musu bore ba ƙaramin rikici da tashin hankali zaki jawowa kanki ba. Ki dai bari ki kama Aminu a hannu yadda zaki ji daɗin yi musu abinda kika yi niyya.

Murmushi Najwa tayi dan ita kaÉ—ai tasan yadda zata yi maganin su Hauwa, sai sun ce Sameeha nafila ce dan ba zata É—auki iskamcin da suka yi mata ba.

*****

Abuja.

Sameeha ta gama shiri a ranar juma'a zata tafi Kaduna domin bikin Najwa, wanda Jirgin kasa zata bi tare da securety saboda shi Ibashim ba zai samu zuwa ba dalilin aiki, ranar Alhamis tana zaune a falon ƙasa tana magana da Ikram a chart sai ga kiran Aminu ya shigo wayarta, bata yi mamaki ba dan tasan dole watarana zai nimeta dan tasan yaran zasu matsa masa akan ya kawo su gurinta, ya kusa katsewa kafin ta ɗauka suka gaisa kana ya sanar da ita zai kawo mata yara saboda aurensa ya matso, tayi mamaki sosai wanda yasa ta kasa haƙuri tace.

Ashe ka samu lafiya kenan? Wacece zaka aura? Allah yasa wacce zata kula mini da tarbiyyan yarana ne.

Inna samu lafiya inma ban samu ba wannan bai shafeki ba, ki tura mini adireshin gidanki driver zai kawo su yanzu.
Chapter 65 · 0% Book details