Sashe 69
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna kuwa bayan mutuwar tsaye da ta yi numfashinta ne ya soma barazanar barin jikinta wanda nan take ta nima yanke jiki ta faÉ—i amma mutane suka tarota, suka kaita zuwa É—akinta suka kwantar a gado tana mayar da numfashi da Æ™arfi tare da zufa daya rufeta, sai sannu 'yan uwa suke jera mata idonta a rufe. Æangaren Najwa kuwa Nafeesa ce ta taimaka mata ta tashi tare da wata Æ™awarsu, sai suka shiga kakkaÉ“e mata jiki kuka kawai take yi tana alwashin sai ta rama abinda Ikram tayi mata, ko kaÉ—an bata yi dana sanin dan sun san Aminu ta aura ba, ita taso ma ba a lokacin suka sani ba sai in an kaita suga gidan Sameeha ne ya zama mallakinta, duk da tana jin mutanen cikin gidan suna surutunta amma bai dame ta ba dan tasan watan maganar ne ya tsaya, da É—ingishi ta shiga É—akinta ta zauna bakin gado tana shafa gashinta daya yi kura, dan tuni É—ankwalin da aka É—aura mata yayi nashi wajen, a lokacin ne ta buÆ™aci wayarta domin ta kira 'yan daban da suka taÉ“a yiwa Jamila duka ta sakasu su je su rama mata abinda Ikram tayi mata, sai ta kalli Nafeesa tana cewa.
Ina wayata.?
Kin manta wayar tana hannunki da kuka soma kokawa, tuni kuka bi ta kanta taci screen, ko haske bata yi duk ta fashe tayi baƙi.
Wlh Ikram taci bashi yadda ta dukeni sai jikinta ya gaya mata, kuma wlh sai na saka tayi asara kamar yadda nima nayi asarar wayata.
Ta faÉ—a tana girgiza kai, Nafeesa ta isa gefenta ta zauna ta dafa kafaÉ—arta.
Najwa an riga an ɗaura aurenki ya kamata ki gane yanzu rigima ba naki bane, ki barta da Allah ki fuskanci ƙalubalen dake gabanki tunda su inna sun san mijin Sameeha kika aure, sai ki tanadi maganar da zaki kare kanki.
Nafeesa dan sun sani sai me, an dai riga an É—aura ni banda damuwa da su domin dai nayi nasara da aurensa, ni yanzu in har ban rama abinda Ikram tayi mini ba ban cika sunana ba wlh.
To shikenan Nafeesa tace ta koma gefe tana zuba abinci dan dama zasu ci ne suka fita waje yin hoto in sun gama su dawo su ci, Najwa sai kumbure kumbure take tana girgiza kai, ta cire sim ɗinta ta ce Nafeesa ta saka mata a wayarta saboda kar a kirata aji ba'a samu tunda akwai ƙawayenta da basu san gidansu ba, ba musu ta cire ɗayan layinta da bata cika amfani dashi ba ta saka ajaka kana ta sakawa Najwa nata sim ɗin.
Baba ne da yayyin Najwa su uku suka shigo gidan, basu zame ko ina ba sai ɗakin inna, sun samu ta dawo hayyacinta tana zaune gefen gado sai dai har lokacin gumi take yi da alama in aka gwada jininta a lokacin to ya hau, ganin sun shigo yasa mutanen ɗakin suka fita baba ya samu gefe ya tsaya yana dubanta yaran kuma duk zama suka yi a ƙasa, baba yace cikin kulawa.
Sannu Zulai ya jikin?
Da sauki Alhamdulillahi, kaina ne ke sara mini kamar zai rabe.
Allah ya sauke ya baki lafiya. Wai abinda naji da gaske ne akan Najwa mijin Sameeha ta aura, yanzu Junaid ya sameni da maganar wai har aljanun Ikram sun tashi sun yi faÉ—a da Najwa.
Wlh malam nima a bakin Zaidu muka ji maganar tunda kasan shi yasan mijin 'yar uwarsa, sannan da shi aka daura aure, abinda ya bani mamaki da tsoro taya duk aka amsa musu bamu gane komai dan gane da haka ba, Najwa dai nasan ta san komai da haÉ—in bakinta da shi mijin Sameeha suka shirya komai, kuma 'yan uwansa sun san ita ce shiyasa suka ki bari aje kai kaya ashe da walakin goro a miya, hatta kayan lefe maza suka kawo dan kar mata su kawo a gane 'yan uwansa ne dan duk mun sansu.
Amma wannan yarinya ta haÉ—a gurmi, da wani ido zamu kalli Halima, ai ana barin halal dan kunya, banji daÉ—in wannan lamari ba, dama ba a É—aura ba sai a fasa amma aikin gama ya riga da ya gama.
Cewar baba cike da ɓacin rai, Yaya Junaid ya miƙe a fusace ya fita zuwa ɗakin Najwa, yadda ta ganshi a fusace tasan dalili sai ta miƙe tana kallonsa yace cikin tsawa.
Muje É—akin inna za muyi magana.
Yana faɗar haka ya juya, itama tabi bayansa tana ware ɗankwali ta ɗaura akai ta fice. Suna shiga ta samu gefe ta zauna nesa da 'yan uwanta, baba ya kalleta rai ɓace.
Ya aka yi kika haÉ—u da Aminu har kuka yanke shawarar auren juna, domin an saka bikinki lokacin bai daÉ—e sosai da sakin Sameeha ba.
Ni fa yayarsa Hauwa ta roƙeni Allah da Annabi in yarda da auren ɗan uwansu saboda ta yaba da hankalina, har aka ɗaura bamu haɗu da Aminu ba dan bai san nice matar da Hauwa ta zaɓar masa ba, saboda ita ce ta buƙaci kar ya sani, amma muna waya da juna sai dai bai ɗauki muryata ba.
Yanzu dama Najwa duk wannan shirin Hauwa ce munafuka, duk yadda suke da Sameeha basa ƙaunarta amma suka jawoki a jiki domin su ƙara muzguna mata duk da ya rabu da ita, idan ita ta saka son rai a ciki ke meyasa ba zaki duba alaƙarki da Sameeha ba ki ƙi yarda da buƙatar ta, yanzu kin kyauta mana kenan? kina son ki zama silar lalawar zumuncinmu da iyalen yaya Amadu.
Cewar inna cike da tsantsar damuwa, yaya Junaid ya ce cikin faÉ—a.
Ni wlh ban yarda da maganar yarinyar nan ba karya take yi, ita tasan yadda ta tusa kanta garesu har suka yarda ya aureta, na tabbatar mugun son duniyarta yasa ta zaɓi auren mijin Sameeha.
Zan yarda da bayaninka domin lokacin da su Sameeha suka bar lagos suka dawo nan Kaduna, yarinyar nan da ta je gidan ta haɗu da mijin Sameeha, ta dawo gida tana yi nuni surutu akan mijin Sameeha shine daidai irin mijin da take so ta aure, a lokacin na kwaɓeta tace mijin ta bar maganar, ashe abin yana ranta saida ta san yadda tayi ta samu ta aureshi, Allah ya wadaran halinki Najwa, basan a ina kika samo irin wannan son zuciyar ba, idan kin shuka alkhairi zaki gani haka ma in sharrin kika shuka In Sha Allah za ki gani.
Inna kiyi haƙuri kar ki yi mata mugun baki, tunda an riga an ɗaura mu bita da fatan alkhairi Allah kuma ya shiryeki.
Inji Sadiq da yake shi ustaz ne, nan dai suka cigaba da yi mata faɗa, suka yi mata kaca kaca Najwa dai sunne kai tayi tana ta ƙunƙune sam babu abinda ya shiga jikinta na faɗar da suke yi mata, cewa ma take a zuciya.
Na kusa bar muku gidan gabaÉ—aya na huta, kuma wlh sai kun nimeni zan zo ma gidan.
Tana faɗe tana kwafa, su kuma suna cigaba da yi mata faɗa, daga bisani suka yi mata nasiha sai suka sallameta ta fito su kuma suka cigaba da tattaunawa. Najwa tana shiga ɗakinta ta samu Nafeesa ta fita taro wasu 'yan ajinsu na islamiya sun zo basu gane gidan ba, sai ta bar waya a chargy ita kuma Najwa ta ɗauki wayar akan tayi waya da Aminu tace masa ya turo mota da wuri na ɗaukar amarya, ta zauna a bakin gado ta duba contact ɗinta bai hau kan wayar Nafeesa ba saboda a email take saving, Allah yasa ta haddace number ɗin Aminu akanta, sai tayi dialing number, abinda ya ɗaure mata kai ganin sunan Amina ya fito daga number, wato akwai number ɗin a wayar anyi saving, da sauri ta cire Number ɗin ta duba wajen kira, tana kuwa dubawa taga ko jiya sunyi waya, nan take ta shiga WhatsApp ɗinta ta duba number ɗin taga chart ɗin su suna magana a online, jikin Najwa ya soma rawa sai dai bata yarda ta bayyana hakan a fili ba saboda kar sauran ƙawayenta su gane, ta shiga chart ɗinsu taga hira sosai suka yi sai dai kafin ta karanta taji muryar Nafeesa sun shigo gidan sai kawai tayi saurin fita ta goge duk abinda ta san ta duba ta miƙe da sauri ta isa ta mayar da wayar a chargy, ta juyo kenan sai gasu sun shigo da fara'a ta isa ta rungume 'yan matan da suka zo su biyu, sai gumi take yi kamar wacce ta haɗiye ƙarfe dan ta kaɗu sosai dacin dunduniyar da Nafeesa take yi mata, hakan yana nufin ta fara hulɗa da Aminu ne domin ya aureta ne ko kuma ta tona mata asiri itama ta rasa mijinta kamar yadda ta rasa saurayinta, ta kaɗu sosai dan tasan babu sirrinta wanda Nafeesa bata sani ba, haka dai take ta saƙa a zuciya tana yiwa mutane yake suna hira dan ta kasa saka musu baki, bata sake marmarin ɗaukar wayar ba sai in an kirata ne Nafeesa ta ɗaga ta yiwa mutane kwatance dan ba zata yarsa wayar ta shiga hannun Najwa ba saboda tsaro, sai a lokacin ne taji dama bata saka mata sim ba dan kar ta gane suna magana da Aminu. Haka suka yi yinin bikinsu cike da armashi duk da bakin amarya a fashe yake, kuma ta cigaba da sauya kaya ana gyara mata kwalliya, a ranar salla dai tace haɗawa zata yi in an kaita gidanta sai ta rama dan bata son abinda zai ɓata kwalliyarta, sai dai abinda Nafeesa tayi mata ya tsaya mata a rai, tana saƙa da warwara akan irin hukuncin da zata ɗauka a kanta.