← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 98

Sashe 72

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmmm ga sani ga shagali ko, kuma Hadisi ne sahihi sannan ingantacce, amma ai ke baki yi aiki da Hadisin ba domin ke kika fara tona mana asirin da muka jima da birneshi ni da sameeha, yanzu dalilinki kowa sai ya san bani da lafiya. Dan haka dole ki je ki amsa laifinki ki kuma warware musu yadda kika haÉ—a makircinki.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un dan Allah Aminu ka yafe mini kayi mini rai bazan iya dubansu da wannan maganar ba, wlh duk abinda kake so zanyi maka amma banda wannan.

Hmmmm kina ɓata bakinki ne, kamar yadda baki yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba kika aikata abinda kike so, dan haka banga abinda zai sa na fasa abinda nayi niyya ba nima.

Najwa ta fashe da matsanancin kuka dan sosai ta shiga tashin hankalin daya fi na jiya muni, Aminu so yake ya kaita ƙasa ya wulaƙantata ya tozarta ta a idon maƙiyanta, dan ta tabbatar suma sun ƙullaceta zasu so suga ta wulaƙanta, ita kuma ba zata yi fatan hakan ya faru ba dan kar suyi mata dariya, wanda tasan Ikram sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan farin ciki, da yayi mata wannan hukuncin gwara yace ya saketa ta tafi gidansu, ganin sun kusa isa gidan yasa ta kama wajen buɗewa ta danna dan gwara ace ta mutu da ta muzanta a idonsu Sameeha, tasan idan yaga ta mutu bazai ma ɓata lokacin tona mata asiri ba, in ma ya tona bata duniyar balle taga sunyi mata dariya, sai ta soma kokawa da ƙofar motar amma taƙi buɗewa, ganin fa saura ƙiris su isa yasa ta faɗawa Aminu ta kama sitiyarin mota akan duk su mutu, Aminu ya saka ƙarfi dan ya tureta amma ina itama ta saka nata ƙarfin, gashi a daidai lokacin wata motar tifa data ɗauko yashi ta doso su, salati kawai Aminu yake yi yana cewa.

Shikenan Najwa zaki kashe mu, innalillahi wa inna ilaihir raji'un.

Mu tara a pegi na gaba...
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

45.

Aminu ganin da gaske fa Najwa kashesu zata yi, sai ya tattaro ƙarfinsa ya bisgeta daga gabansa ya wasar da ita a gefe ya kifa mata mari mai kyau, sai ya kama sitiyarin motar yayi gefe da motarsa da mugun sauri dan saura ƙiris suyi karo da wannan tifar har saida jikin motarsa ya gogi jikin tifar, mutane sai ihu suke suna salati dan sosai kowa ya sadakar da wannan mummunar hatsari daya kusa aukuwa, Ganin sun tsira yasa kowa yana musu sambarka Aminu ya isa gefen titi yayi parking yana mai sauke numfashi ga wani zufa da yake karyo masa saboda tsananin tashin hankali daya gani mararan, Najwa kuwa kuka kawai take dan itama ganin tifar tayo kansu ba ƙaramin firgita tayi ba, saida taga sun kauce masa yasa ta dawo hayyacinta tana sauke ajiyar zuciya, ashe dai tana tsoron mutuwa ganinta ne kawai da bata yi ba take lissafin gwara ta mutu amma data ga da gaske ne sun kusa mutuwar ta shiga hankalinta, mutane suka dinga tsallakowa suna yiwa Aminu barka shikam hannu yake ɗaga masu yana ya gode, saida ya daidaita natsuwarsa kafin ya kuma tada motar suka wuce. Ɓangaren su Inna kuwa har sun insa gidan, ita ta fara shiga kafin ta sanar da su umma tare take dasu ba kana ta fito tayi musu iso shi da Junaid, a nan tsakar gida suka zauna kan babbar tabarma da aka shimfida musu, Umma ta sako hijab ta fito suka gaisa kana su baba suka bata haƙuri akan abinda ya faru jiya da kuma nuna mata suma basu san da lamarin ba sai a jiyan, umma tace ba komai haka Allah ya ƙaddara, sai suka yi ɗan jim kafin Junaid ya isar mata da saƙon da Aminu ya sanar musu wanda yasa suka zo, umma tayi shuru tana mamaki tare da tunanin mai zai kawo Aminu gidansu bayan tun da ya saki Sameeha bai sake waiwayarsu ba, sai ta nisa tace Allah ya kawo shi kana ta miƙe ta shiga cikin ɗaki, ba jimawa su Sameeha suma suka fito suka gaishe su harda Zaidu dan duk suna a tare ne a ɗakin Umma sun gama karyawa, nan umma ta saka Zaidu ya bawa inna haƙuri akan abinda yayi mata jiya tace ba komai ai ya wuce, sai ya matsa kusa da Junaid suka shiga yin hira su Umma ma suna nasu.

Aminu suna isa ƙofar gidansu Sameeha yayi parking ya kashe motar ya fito, Najwa ma fitowa tayi ya rufe motar ya tasa ƙeyarta suka shiga gidan, Najwa sai sunne kai take yi jiki a mace domin ruwa ya karewa ɗan kada, sun tadda har su inna sun iso suna zaune a tsakar gida bisa babban tabarma da alama zuwansa ake jira, ganin yana tare da Najwa yasa suka fahimci maganar ta shafesu duka ƙila kan batun aurensa. Su Abi suna jin muryan baban da yayi sallama suka fito daga ɗakin umma suka rungume shi ya kama su yana cewa.

Yaushe kuka zo kaduna.?

Shekaran jiya tare da mamanmu.

Abi ya bashi amsa, Aminu yayi guntun murmushi.

To yayi kyau ku koma É—aki in mun gama magana sai na kiraku mu yi magana kan na wuce.

To suka ce masa sai suka koma cikin ɗaki, shi kuma ya samu guri ya zauna kusa da inda Najwa take zaune, ta rufe fuskarta da mayafi bata buɗe ba balle tasan su waye zaune a tabarmar, zuciyarta ta gama tsinkewa sai bubawa take yi kamar zata faɗo ƙasa, Aminu daya zauna suka gaisa da su uma gabaɗaya sai a lokacin ne Najwa ta gane dasu innarta a gurin, take taji fitsari ya kamata jikinta ya ɗauki rawa, jin Baba ya soma magana yasa ta natsu tama rasa me zata yi.

Yauwa Aminu gamu mun zo sai ka faÉ—a mana dalilin taruwarmu a nan.

To baba maganace Nazo da shi akan abinda ya shafeni da kuma Sameeha sai kuma Najwa data shigo ciki, in ba damuwa a kira Sameeha tazo ayi maganar da ita.

Nan take Umma ta kwalawa Sameeha kira sai gata ta fito sanye da hijab ta ƙaraso ta zauna daga gefen tabarma, sai ga Ikram ma ta fito ta zauna daga bakin ƙofa dan so take taji meya kawo su. Aminu ya cigaba da magana ya fara basu labarin dalilin sakin Sameeha da yayi dama yadda ya kamata da waɗannan 'yan matan, su inna da basu san zancen ba suka shiga mamaki sosai, Sameeha kuwa kuka ta fara mara sauti dan ya tuno mata da mugun giɓi da kuma ƙoƙarin tona maganar da yayi gaban su inna, Aminu ya cigaba da cewa.

Sameeha kiyi haƙuri ba na dawo da maganar nan bane domin na tona miki asiri kona tozartaki ba, saboda ina so na ɗaura maganar akan yadda kowa zai fahimta. Ina son Sameeha amma haka na haƙura da ita badan na kamata da waɗannan 'yan matan ba sai dan na kuɓutar da ita daga faɗawa halaka, akan ta samu damar auren mai lafiya wanda zata tsira da mutuncinta dana yaranmu, wanda daga ni sai ita sai kuma in ta faɗawa su umma sune suka san da wannan maganar, dan ko 'yan uwana babu wanda yasan da maganar dan ban faɗa musu dalilin rabuwarmu ba sannan basu san bani da lafiya ba. A bayan rabuwarmu ne Hauwa ta matsa mini da zancen sai nayi aure, hakan yasa nace ta samo mini mata domin na samu hanyar da zan ƙuntata mata na rama duk wani abu da suka yiwa Sameeha nima suka yi mini, ita kuma bata san da wannan kuɗurin na amsa mata da auren ba, sai tace ta samo mini mata Najwa, wallahi Tallahi ban san wannan Najwan bace dan ban taɓa kawota a raina ba domin ban ma wayeta sosai ba dan haɗuwarmu da ita baifi sau biyu ba a gidanmu lokacin Samewha tana nan, haka ta haɗamu a waya muka cigaba da magana bamu taɓa haɗuwa ba sai jiya da aka ɗaura aurenmu har nasan wacece Hauwa ta aura mini, sai a lokacin ne na tuna irin kallon da Zaidu kayi mini ashe na tuhuma ce wanda ni ban fahimci haka ba. Najwa da Hauwa bansan a ina suka haɗu ba har suka haɗa kai wajen ganin sun cutar da Sameeha sun ƙuntata mata, ko da yake wannan ba shine abin mamakin ba dan nasan halin Hauwa zata iya aikata komai wajen ganin ta jawo Najwa a jikinta, sai dai kuma ita Hauwa tana nata Najwa ma tana nata haɗa tuggun.

Kamar ya fa? ka warware mana maganar nan kai tsaye yadda zamu fahimta.

Cewar Zaidu da duk ya ƙosa yaji ƙarshen maganar, Aminu ya yi guntun murmushin takaici ya girgiza kai yana cewa.

Sameeha wannan lesbian dana kamaki da 'yan mata, ashe ba kowa ya haɗa wannan makircin ba sai Najwa da ƙawarta Nafeesa.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un

Duk suka haɗa baki wajen faɗa, Sameeha kuwa har da dafe ƙirji tana kallon Najwa dake rufe da gyale jikinta yana mugun rawa, Ikram tace da ƙarfi.

Anzo wajen, yau dai Allah ya bayyana gaskiya kowa yasan wacece ke Najwa, Allah ya tsine miki albarka ya wadaranki.

Karna sake jin maganarki Ikram.

Cewar Umma data waigo tana gargaɗinta da nuna mata yatsa, Baba kuwa cire hular kansa yayi yana jin wani zafi yana hura shi, inna ma sosai ta soma gumi dan gashi nan akan fuskarta tayi matuƙar girgiza da wannan labari, Junaid ko girgiza kai kawai yake cike da ta'ajibi, Yaya Zaidu kam murmushin takaici yake saki yana cije gefen leɓensa zuciyarsa tana harbawa da sauri. Aminu ya cigaba da basu labarin bayan kawo Najwa da aka yi jiya da kuma hirarsu daya ji na faɗa ita da Nafeesa, babu abinda ya ɓoye duk wanda bai manta ba ya faɗa, ya ɗaura da cewa.
Chapter 72 · 0% Book details