Sashe 13
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai dama ke badan Allah zaki so su zauna anan ba sai dan kwaÉ—ayi da kika sabarwa kanki, wlh Najwa in baki wasa ba bakinki sai ya ci abinda zai kashe ki.
Ikram bana son sakarci ko kin mance matsayin Najwa a gunmu da zaki riƙa faɗa mata duk abinda yazo bakinki, ki na sane da jininmu ce ita kuma itace matar Yaya Zaidu da zai aura ko da kin girmeta dole ki bata wannan girman, kuma abinda ta faɗa gaskiya ne babu abinda zai sa na bar kaduna wallahi.
Cewar Sameeha tana gargaɗin Ikram, Ikram bata ƙara magana ba Najwa kuwa ta sakar mata murmushi tana yi mata gwalo, Ikram harara ta balla mata tana ƙofa sai ta miƙe ta wice ɗakin Sameeha dan ta yi wanka saboda su Adama sun camama mata jiki duk ciwo yake mata. Tana shiga ɗakin ta kira umma ta zayyana mata komai, umma a wannan karan itama ranta ya ɓaci ta aje kara ta dinga faɗa tana cewa yanzun nan Zaidu zai kawota, abin nasu yayi yawa itama Sameeha 'yar dangi ce kuma tanada gata ba zai yuwu su riƙa yi mata cin kashi ba dan ita ba shara bace da za a zubar da ita a duk inda aka ga dama, dan in bata nuna ɓacin ranta ba to gama ba sakewa zasu yi, Ikram taji daɗin bayanin Umma wanda ta ce sai sun zo ta kashe wayarta.
Bayan kusan minti talatin sai ga Yaya Alhasan da yaya Kamalu zun so gidan, su Hauwa suna ganin shigowarsu suka sha jinin jikinsu ko wanne ya shiga hankinsa, suka ƙaraso gabansu suka tsaya suna kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin Alhasan yace.
Kun kyauta abinda kuka yi, kuma wlh duk sai naci mutuncinku, marasa lissafi da tunani, daga zuwa cin arziki sai abu ya zama rashin hankali da hauka, dole dai sai kun saka kanku a cikin irin dangin mijin nan da basu da kirki ake faɗarsu a duniya, to ina dai dai da iskancinku kuma daga yau duk shegiyar data kuma tako ƙafa tazo gidan nan naji labari abinda zanyi mata Allah kaɗai ya sanshi, dan har gida zanbi mace naci ubanta kuma..
Bai ƙarasa maganarsa ba su Umma suka shigo ita da Zaidu, suka jira har suka ƙaraso gurin da suke Alhasan da Kamalu suka gaisheta kana Zaidu shima ya gaishesu, a lokacin su Sameeha suka fito daga ɗaki suka ƙaraso dan Zaidu ya kira Sameeha yace mata suna gate tace su buga mai gadi zai buɗe musu, Umma ta ce cikin damuwa.
Dan Allah Hauwa ina so ku faɗa mini meye Sameeha tayi muku da kuka saka mata wannan karan tsanan haka, tunda ta Aure Aminu kuke yi mata abubuwa tana kawo min magana amma ban taɓa bin bayanta ba, dalilin zuwana yanzu so nake naji me take yi muku sai na sakata ta baku haƙuri komai ya wuce, dan gaskiya lamarin bai mini daɗi ba tunda har ya kai ga fara duka, ina son Sameeha dan haifarta nayi ba daga sama ta faɗo ba, ba zai yuwu daga dawowarsu a hana mata kwanciyar hankali a gidanta ba.
To ai itace ta kawo rikicin ta fara marina saboda ta zagi mamana na saka baki.
Cewar Adama data tari numfashin Umma, Kamalu cikin daka tsawa yace.
Zo nan dan ubanki, uban waye yace ki saka baki?
Adama ta matso nesa da shi ta tsaya tana turo baki, aiko daya yi wani tsalle ya kifa mata mari mai kyau ya rankwatseta akai yana zaginta, Hauwa ta ce cikin faÉ—a.
Haba taya za a dakeni a hanani kuka, ya zaka huce haushinka akanta, dan me daga mayar da magana sai duka.
Idan baki mini shuru ba Hauwa wlh zan ci kaza kazan ubanki 'yar banza kawai mara mutunci ba duk kece kika kawo wannan hargitsin ba. Dan Allah Hajiya kuyi haƙuri In Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba kuma zan ɗauki tsattsauran mataki akan haka.
Cewar yaya Alhasan kamar zai rufe Hauwa da duka, nan suka cigaba da yi musu masifa suka ce su tattara su bar gidan kuma idan suka ƙara zuwa gidan Sameeha ta faɗa musu zasu ɗauki mataki, kana fa su Hauwa suka wuce soƙai soƙai ko wacce cike da ɓacin rai, Laure dai ta kasa magana dan tasan halin mijinta da ɗaukar zafi idan bata yi wasa ba sai aurenta ya samu gargada, shiyasa ta sakawa bakinta kwaɗo da linzami tabi sahun sauran matan ba tare da yin ko tari ba, haka itama Sa'a bata iya cewa komai ba dan tasan halin Kamalu bai da wasa, sai da suka bar gidan umma ta sake jajjada musu su ɗauki mataki dan ba zata yarda da zancen duka ba, suka tabbatar mata da hakan bazai sake faruwa ba kana suka bata haƙuri, Sameeha tayi musu godiya ta ɗaura da cewa.
Aminu yace wai zan bar kaduna mu koma Abuja dan Allah kuyi masa magana ya barni a nan na zauna cikin 'yan uwa ni banga abinda zaisa ya yanke wannan hukuncin ba dan su Hauwa sun saba yi mini bita da ƙulli duk in da naje ma ba fasawa zasu yi sai dai in Allah yasa su gane gaskiya.
Dama wannan ba dalili bane da zai sa ku sake barin Kaduna, In Sha Allah za muyi masa magana ba in da zaku koma.
Cewar Kamalu, nan ta sake yi musu godiya suka yi mata sallama suka wuce, su Umma suka wuce zuwa falo, sai da suka zauna kafin Umma tace.
Sameeha da za kiji ta tawa da kin bi mijinki kin huta da fitinarsu.
Tsoransu taje ji kenan? aiko wlh ni banga dalilin da zai sa ta bar kaduna ba muna jin dadin ta dawo kusa damu.
Cewar Zaidu, nan dai suka dinga tattaunawa, Najwa ta buÉ—e kunne tana ta É—aukar magana, sai daga baya ta ce ita zata tafi, Sameeha taje kitchen ta É—ibar mata sauran abinci a babbar kula da naman ragon da kaji tace ta kaiwa inna, ta bata dubu uku Najwa ta amsa tana godiya, Zaidu ne ya É—auketa a mashin É—insa yace in ya sauketa zai dawo ya mayar da umma gida.
A hanya da suke tafiya Zaidu ke cewa Najwa.
'Yan matana wai laifin me nayi ne kwanakin nan kike ta shareni? Tunda na siya miki waya ya kamata ace kin sauko daga fushinki ko.
Hmmm ni ba wani abu kawai dai karatu ne ke hanani yin magana da kai.
Amma ina ganinki a online ina miki magana sai dai baki kulani, ko shima karatu kike a gurin..
Hira nake da ƙawayena bana ganin maganarka sai in na fita daga group. Kuma lokacin sai naga ka sauka.
Najwa ko dai kin samu wani ne kina son kiyi mini halinku na mata.
Ai kasan dama ni a kasuwa nake mai rabo ka É—auka, duk yadda ka É—auka to hakan ne dan na kula ka fiye zargi da mita, idan dan wayan da ka siya mini ne sai na mayar maka da abinka, nasan ina da wanda sai kawo mini sabuwar waya wacce tafi wanda ka bani.
Haka ma zaki ce?
Eh!
Ta faɗa cike da tsiwa tana murguɗa masa baki kamar yana kallonta, girgiza kai yayi yana Allah ya kyauta ya cigaba da tuki bai sake magana ba har ya sauketa ta shiga gida ba tare da ko godiya ba sai cin magani take tana ɓata fuska, Zaidu ya sauke ajiyar zuciya yaja mashin ɗinsa ya wuce, tunaninsa ya gama bashi Najwa tayi sabon saurayi kuma da alama mai kuɗi ne tunda yasan halinta tana da son abin duniya, sai dai bai taɓa kawowa lokaci guda zata sauya masa ba, ashe ba sonsa take ba yaudararsa kawai take yi, idan hakan zai kawo saɓani da zumuncinsu zai haƙura da ita kawai ya nima wata, amma zai cigaba da binta a haka ya ga iya gudun ruwanta.
Zaidu bayan ya koma gidan Sameeha yadda suka ganshi ba annuri yasa Umma ta tambaye shi ko lafiya, ya zauna ya zayyano musu duk abinda Najwa take masa dama abinda tayi masa yanzu da ya kaita gida, Sameeha tace masa.
Ko dai dama bata sonka tuntuni kawaicin zumunci yasa take saurarenka, to gwara tun wuri kasan matsayin data ajeka dan kar azo a samu matsala, idan ba zai yuwu ba ka nima wata dan bana son zumuncinsu ya samu matsala.
Gaya masa dai tun farko daya zo mini da maganar sai da na jinjina amma daya dage nabi sa da addu'a, dan haka kasan me kake ciki da ita, idan bata yinka ka kama kanka cikin salama. Tashi ka mayar dani gida, Ikram sai yaushe zan ganki?
Cewar umma, Ikram tace.
Tsakanin Alhamis ko juma'a bayan mun seta gidan In Sha Allah zan dawo.
Ta faɗa tana miƙewa tare da ɗaukar musu kular da suka zuba musu abinci da ledar da suka saka musu kayan lemu da ruwa, dama mazubin da suka saka musu nama. Har gate suka rakasu suka hau mashin tare da aje musu kayan a gaban mashin ɗin, Zaidu ya jasu suna daga musu hannu, sai suka dawo cikin gida Sameeha ta sanar da mai gadi ya samo masu aiki su gyara mata farfajiyar gidan, sannan in masu ɗibar kanofi da kujeru sun zo ya buɗe musu su shigo su kwashe dan ta sallamesu, sai ta wuce cikin gida. Ta samu Ikram tana waya ta zauna tana kwalawa jamila kira ta fito da sauri daga ɗakinta dan dama tun ɗazun da su Hauwa suka tafi ta shigo ciki ta shige ɗakinta, sai da ta tsuguna a gaban Sameeha kana ta ce gani.
Yauwa gobe In Allah ya kaimu da sassafe nake so ki gyara mana gida bana so na tashi naga baki yi komai ba. Zaki iya tafiya.
Cewar Sameeha, sai Jamila ta ce mata to kana ta miƙe ta wuce tana ƙunƙuni da zancen zuci.
Dama É—azun sunyi miki dukan tsiya sun kumbura miki baki muga ta yadda zaki yi magana, shegiyar mata ko tausayi na bata ji, ko da yake kuÉ—i zata biyani dole ta bautar dani.
Ta ƙare zancen tana turo baki ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shige.
***
Najwa.