Sashe 55
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Meke faruwa ƙawata? Na ganki a hargitse ne kamar kin gamu da abin furgici.
Su Sameeha sun fini komai Nafeesa banda abinda zan yi gogayya dasu domin duk mazajansu sunfi Amunu da komai, akwatinansu abin kallo ne wanda ya gigita lissafina da tunanina nasan ni ban zo duniya a sa'a ba, komai nice ƙarshen baya ina ganin har na mutu bazan taka matsayin da nake buri ba a rayuwata ba.
Nan ta kwashe labarin akwati ta faɗa mata komai da idonta suka gani, tana faɗi tana kuka hawaye shaɓe shaɓe. Sai da takai aya kafin Nafeesa ta ja numfashi ta sauke a hankali tana cewa.
To sai me dan anyi musu kaya haka? Dama dole ki saka a ranki zasu samu haka domin kuÉ—in sadakinsu kawai ya nuna akwatinsu zai zo da kaya irin wannan, bana so kina saka damuwar su fiki kowa fa da arzikinsa, ina ce kema kin samu cikar burinki na auren Aminu, wanda shima ba talaka bane yana da kuÉ—i sosai, na tabbatar hatta motar hawa zaki samu a gidansa, kuma dama babu yadda za ayi kice komai daidai zaki samu dasu Sameeha domin yatsun nannunmu ma ba É—aya bane, dan haka ki cire komai a ranki tunda kema ba talakan zaki aura ba.
Amma Nafeesa duk yadda naso ba haka nake samu ba, bana so ko kaɗan su fini jin daɗi a gidan miji, burina kafin aga wani abu mai kyau da tsada a hannun 'yan danginmu an fara gani a hannuna, a kullun burina na kasance sama da kowa, sai dai burina ba zai cika ba tunda su Sameeha sun zama zakaran gwajin dafi, akomai suke fara tare mini hanya su rigani isa kafin na kai. Ni bikin ma bazan sake zuwa ba suyi kayansu dan kar baƙin ciki ya kashe ni a banza.
.
Aiko baki isa kice ba zaki je ba, in ba haka ba da wuri zasu gano kina musu hassada, gwara ki shiga a dama dake ta yadda zaki yi ƙoƙarin ganin abubuwa kema ki tsara aurenki da yadda zaki zauna a gidanki yafi nasu, idan fa kina so ki fisu to dole sai kin riƙa binsu kina shige musu tare da sanin duk halin da suke ciki, ta hakane zaki gina naki rayuwar yadda kike muradi, dan haka nima zan shiga bikin a dama dani dan na riƙa ƙara miki karfin guiwa, bana so ki sare akan cikar burinki.
Allah ko Nafeesa? kina ganin hakan za mu yi?
Sosai ma kuwa, yanzu ma tashi zaki yi ki wanke fuska na ara miki kayana ki raka ni dinner É—in 'yar uwarmu kiga yadda ake shagalin masu kuÉ—i, shima wani darasin zaki É—auka.
Da sauri Najwa ta miƙe tana murmuahin jin daɗi, nan da nan ta sake ta watsar da damuwar su Ikram ta shiga shirin zuwa dinner dan duk abinda zai sa ta samu ilimi akan harkan kuɗi ba zata yi ƙasa a guiwa ba. Nafeesa tana ganin Najwa tana shiga bayi ta ɗauki wayarta dan ta san code ɗin buɗewa, ta ɗauki Number ɗin Aminu tayi saving a wayarta da suna Amina. Tun sanda Najwa take bata labarin Aminu yana kulata sosai yanzu har waya suke yi suna hira ya sake mata fuska, sai dai haɗuwa ce basu yi ba kuma yana tura mata kuɗi akai akai, Najwan tana nuna mata farin cikinta da samuwar kwanciyar hankalinta, har take cewa ko dan yaji Sameeha zata yi aure be shiyasa ya sake mata yanzu ya haƙura, to ita kuma Nafeesa ta samu matsala da wanda zai aureta gashi ba tada wani tsayayye, sai ta soma jin damuwa akan auren da Najwa zata yi ta rigata, ga kuma yanzu Aminu yana sake mata suna hira a waya ga kuɗi da yake yawan tura mata, shi kuma yayi hakane domin ya saba da ita dan sosai ya ɗauki kudurin gyara alaƙarsu yayi zaman aure da gaskiya da ita, saɓanin da daya ɗauki alwashin kin amsarta domin ya muzgunawa Hauwa, amma dalilin auren Sameeha yasa zai karɓeta domin ya huce takaici. Nafeesa ta yi tunani kala kala domin taga hanyar da zata lalata auren Najwa a fasa kamar yadda ta rasa saurayinta, sai ta fara hangen ko ta tonawa Najwa asiri Aminu yasan wacece, sai kuma daga baya taga ko ta tona ba lallai yayi tasiri ba tunda Hauwa tana bala'in son aurensu kuma ta san Hauwa zata iya komai ganin anyi auren, hakan yasa ta sake tunani akan ta ɗauki Number ɗinsa ta ja ra'ayinsa su fara soyayya, in yaƙi bada ƙofa ta shiga malamai ta samo kansa itama ya aureta, idan Najwa ta samu labari ta nima kawo mata wargi tayi mata barazanar tona mata asiri akan sharrin lesbian da ta ƙullawa Sameeha wanda tasan in Aminu yasan da haka dole ya rabu da ita, dan haka tasan ba zata yarda asirinta ya tonu ba zata yarda su zauna suci arziki tare, tunawa da wannan plan ɗin nata yasa ta saki wani shu'umin murmushi dan kuwa har hotonsa ta tura kwanaki a wayarta, dan itama ta kamu da sonsa na farad ɗaya tunda Aminu yana da kyau ga kuɗi baida makusa, dama namiji mai kyau haka mata suke rububi akansa sai wanda Allah ya tsallake ne baya faɗawa zina. Najwa koda ta fito shiryawa tayi sauri sauri a lokacin ana kiran sallar magrib amma saboda azalzala mata da Nafeesa tayi basu tsaya yin sallar ba suka tafi, a hanyarsu ne Inna ta kirata akan tana ta jira ta dawo daga inda taje su koma gida, nan Najwa take faɗa mata taje bikin wata 'yar ajinsu da ake dinner amma ba jimawa zata dawo, haka inna ta baro gidansu Sameeha tanata faɗan jiranta data tsaya yi ashe tayi gaban kanta, zuwa yanzu ta soma damuwa da sauyawar halayyar Najwa, ada tana jin magana da gudun ɓacin ranta amma yanzu komai yin gaban kanta take yi bata tsayawa niman izininta ko shawararta, sai take ganin ko dan auren da zata yi ne ya fara sauyata da tunanin haka ta isa gida.
Najwa ko da suka isa gurin dinner Nafeesa sai ƙara kwantar mata da hankali take yi akan karta saka damuwar su Sameeha, dalilin daya saka Najwa ta ƙara samun natsuwa na sakin jiki suka sha hidimar dinner, wanda sai sai wajen goma na dare ta dawo gida. Ba ƙaramin fada Inna tayi mata ba, dan ma ta rufa mata asiri tace tana gidansu Sameeha ne, da ƙila Baba sai ya kusa dukanta, a ɗaki ta sameta tayi mata faɗa sosai, Najwa ta ɓata rai tana turo baki.
Haba inna tare nake da Nafeesa fa kuma kin san duk inda zanje bazan taɓa yarda na ci amanarku ba, kuma nasan da maganar auren wani a kaina. Ni dai inna na kula kin gaji da ganina a gidan nan to In Sha Allah nan da wata biyu zan bar miki gidan sai kin dawo kina kewata.
Ni kike faÉ—awa haka ko? kin kyauta Najwa.
Inna ta faɗa rai ɓace sai ta wuce ta fita, Najwa ta bita da cewa.
Nifa gaskiya na faɗa miki, amma kiyi haƙuri naga ranki ya ɓaci.
Inna bata tanka mata ba ta wuce zuciyarta tana yi mata suya, damuwarta yadda lamarin Najwa ke ƙara yin gaba, tsoronta kar taje gidan miji tana yi masa rashin ɗa'a ya gaji ya korota, dan yadda take fitar da magana bata taunata to ba ko wani namiji ne zai ɗauka ba, Addu'ar shiriya tayi mata ta shiga ɗaki ta kwanta.
***
Kamar yadda Nafeesa ta tsara musu hakan ya faru dan washe gari da rana ta zo gidanau Najwa suka je gidansu Sameeha dan a cigaba da shagali tare dasu, koda Najwa ta gabatar musu da Nafeesa sun karɓeta dan dama ba wasu ƙawaye garesu ba har gwara Ikram, Najwa ta saka aka buɗe musu akwati suka gani, ita kanta Nafeesa sai da ta gigice bata ga laifin Najwa ba jiya da ta rikice tana fidda kuka, ashe gani ya kori ji, duk da ta fito gidan kuɗi kuma tana ganin manyan akwati na 'yan uwansu bata taɓa cin karo da wannan ba, ba a zuba kayan rashin hankali ba amma fa an zuba masu tsada sosai, ji tayi inama ace zata samu ɗaya daga cikin angwayen su so ta koda a ta biyu ko ta uku ta shiga, sai dai so ba samu bane, haka aka rufe akwati sunata santi tare da zuzuta shi, Ikram dai ko a jikinta dan ba su kaɗai bane suka yi wannan santin, Ita Sameeha tana ɗaki ana yi mata gyaran jiki da Khairy takawo musu har gida ake yi musu, kayan kuma suna ɗakin yaya Zaidu an rufe su.
A hankali aka cigaba da shiri Najwa tana ƙara shige musu dan ana saura wana biyu biki ta tattaro kayanta ta dawo gidan tana kwana, ita kuma Nafeesa kullun sai tazo sai yamma lis take komawa gida dan ta sawa kanta sai taga ƙarshen wannan hidima, duk yadda Najwa taso ta san su waye zasu aura bata samu dama ba dan Shamsu tunda aka kawo akwati bai sake zuwa hira ba sai waya, ita dama Sameeha sun fi yin waya saboda baya zama, sunayensu kawai ta sani da Ikram ta faɗa mata, har tana cewa ta taɓa saurayi mai suna Shamsu ta koreshi saboda baƙi ne mummuna, Ikram tace ai dama ta santa da ruwan ido Allah yasa wanda zai aureta mai kyau ne, nan ta shiga zuzuta Aminu tana cewa fari yake tas ɗan fillo son kowa ƙin wanda ya rasa, haka dai suka dinga hira wanda itama har gyaran fuska anyi mata tare da wanke kai da kunshin lalle baƙi da ja, ta fito tayi fes itama kamar amarya.
******
Ranar É—aurin aure.