← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 98

Sashe 82

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya ƙare maganar yana duban 'yan uwansa, Taju da duk jikinsa yayi sanyi saboda tausayinta yace.

Wlh ta bani taussayi sosai ƙila da gaske ta tuba ko za muyi wani abu ne akai Hassan.

Wani irin harara Hassan yayi masa yana cewa.

Babu abinda za muyi mata wannan shine kaɗai gatan da zamu nuna mata gwara ta ɗanɗana zaman gidan kaso taga yadda mutane ke cikin wahalar rayuwa, jin daɗi da gata da sangarci yasa take ganin zata aikara komai, ciki kuwa harda saɓon Allah mafi muni, ita ta haka ne zata nuna godiyarta a gareshi, to kaga gwara taga ikon Allah ya nuna mata da gatanta da komai amma ta rasa wa zai taimaketa, wataƙila hakan zai sa tasan ya rayuwa take ba munzo duniya dan mu shagalta da jin daɗi ba ne mu sabawa Allah son ranmu, Allah ya haliccemu ne domin mu bauta masa mu kaɗaitashi sannan mu yi koyi da halayyar Manzon Allah s.a.w domin mu gina lahirarmu da ayyuka na kwarai don mu samu Aljanna. Bawai dan banji tausayinta bane, ba kuma dan bana sonta bane, ina so ta gyara rayuwarta ne domin gatan da ya rage muyi mata ganen mu nusar da ita yadda rayuwa take da kuma yadda zata bi da lafiyarta da jin daɗinta gurin bautawa Allah.

Maganganunsa sunyi matuƙar tasiri a zuƙansu wanda yasa suka ƙarfafa masa guiwa akan hukuncin da aka yanke musu shine dai dai, sannan ma ba zuba ido zasu yi ba su barta sakaka a can dole zasu na kai mata ziyara dan ganin wace rayuwar take gudanarwa a can fatan su dai Allah yasa hakan ya zama silar shiryuwarta.

Da suka isa gida ne Hassan ya zayyano wa iyayensu duk abinda ke faru tare da bayanin Taju, Dady cike da tsantsar mamaki ya dubi momynsu yace.

Me yasa tsawon kwanakin nan kika ɓoye mini Binafa bata nan, kullun na tambayeki sai ki ce kin aiketa ko tana gidan su Taju taje hutu.

Wlh Alhaji text ta tura mini da wayarta akan tayi tafiya zuwa kano to bana son na sanar da kai kayi faɗa shiyasa naketa ɓoye maganar.

Cewar mony cike da damuwa, Hassan yace.

Ai nine na tura miki saƙon lokacin dana amso wayar a gurin 'yan sanda, nasan ba zaki so a san tayi tafiya ba shiyasa na tura miki dan ke zaki kareta tunda dama haka kika saba yi mata, wlh kuna da saka hannu a lalacewar Binafa dan haka yanzu gatan da zaku nuna mata ɗaya ne shine ku bari doka tayi aikinta yadda zata gyara ruyuwarta ta gane abinda take aikatawa a matsayin wayewa karyace, rayuwar da za abi dokokin Allah da bin sunnar Manzon Allah shine gaskiya.

Babana shekara biyu fa a gidan yari baka ganin shekaru yayi yawa ina laifin wata shida, ko dai mu ɗaukaka ƙara ne a sake nima musu sassauci.

Cewar Dady, momy ma nan ta goyi bayansa, Hassan yace.

Bazan hana ku ɗaukaka ƙara ba, amma duk abinda yaje ya dawo babu ruwana ni kuma wlh idan Binafa ta cigaba da aiwatar da abinda take yi to da kaina zan kaita kotun musulunci su hukuntata.

Jin maganar daya faɗa yasa Dady yace to ba damuwa a bar maganar a haka, sai dai zasu riƙa kai mata ziyara shi gani yake har da kuruciya ke damunta, amma yana ganin tana dawowa gida aure zai yi mata ya huta, haka dai sukaita tattaunawa daga bisani taron ya watse.

Binafa an saukesu a babban gidan yari dake nan jihar Kaduna ɓangaren mata, ji take kamar ba ita ba tamkar wata aka sauya dan ko a mafarki bata taɓa kawowa kanta yin rayuwa a irin wannan ƙasƙantaccen gurin ba, Hanan kam kuka tun tana na zahiri har ta koma na zucci idanu sun koɗe kamar tsohon zani, nan aka gabatar dasu ga hukumomin gidan aka basu kayan da zasu saka na gidan yari riga da wando da kuma hijab, aka shigar dasu wani ɗaki suka sauya kayansu kana wanda suka cire aka adana musu,vnan aka shigar da sunayensu a lis aka tisa ƙeyarsu zuwa cikin gidan, faɗar tashin hankalin da suke ciki ɓata lokaci ne dan sosai suka karaya suka kuma tsunduma cikin gogin dana sani.

*******

Najwa.

Bayan sati biyu wanda ya kama wata guda kenan da zuwan Binafa gidan. Da dare lokacin sallar Isha'i ta idar da sallah kenan sai ga Siyama ta shigo tana ce mata mamansu tana kiran ta, Najwa ta miƙe ta cire hijab ta naɗe sallayar sai ta fito falo ta sameta a cushing sai ta zauna tana cewa.

Anty gani.

Yauwa dama baƙo ne Malam ya turoshi gurinki, sai ki fita ku gaisa, ina fatan ku daidaita kinga In Sha Allah ba zaki ɗauki lokaci ba zaki yi aurenki, kuma mutumin yana da abin hannu dan babban ɗan kasuwa ne matansa biyu.

Haba Anty mata biyu fa kika ce, ina zan kai shi? tafÉ—i! wlh ba zan iya auren me mata ba saurayi ma sai na darje.

Haba Najwa karki saka naji kumya mana malam da kamshi fa ya turo shi, kiyi mini kara ki bani haÉ—in kai na tabbatar in kika ce gidanki ke kaÉ—ai kike so Alhaji Atiku zai gina miki dan yana da kuÉ—i sosai.

Hmmm bari dai naje naga kalarsa tukuna kan nasan abin da ya dace nayi.

Ta faɗa tana miƙewa tare da komawa ɗaki ta ɗauko hijab ta saka kana ta fita zuwa fargfajiyar gidan da bai wuce fitanta sau uku ba tun zuwanta gidan, daga can nesa ta hango shi tsaye jikin wata farar mota, hakan yasa ta nufi can ɗin dan tasan shine ma tunda ba wani da ta gani a farfajiyar gidan, sai mai gadi dake can wajen gate yana sauraren radio. Najwa tunda ta tunkaroshi yake washe mata baki kamar wanda ya ga wawan zama, takaici da baƙin ciki ya turniƙe Najwa domin mutumin baƙinƙirin yake hasken haƙoransa kawai take gani da farin idanu, yadda ta rainawa Shamsu wannan ma ya dama shi a baƙi ya tsanye, ga wani tumbi daya aje sai kace mai ciki, da ɗaure fuska ta ƙarasa ta tsaya tana gaishe shi a daƙile, Atiku ya washe baki yana amsa mata ya ɗaura da tambayar ta ya gida tace lafiya, sai suka ɗan yi shuru daga bisani ya cigaba da cewa.

To Najwa mai daÉ—in Suna, ni sunana Alh. Atiku, tun ganin farko dana yi miki ranar kin shigo falo tare da matar malam a nan naji na kamu da sonki, kuma ni ba da wasa nazo ba aurenki yake son yi wanda kafin na zo sai da malamvya bani damar haka wato na nima izini a gunsa, dan haka ina so ki bani dama mu fahimci juna kafin daga bisani manya sai su shiga maganar dan bana so a É—auki lokaci kan azumin nan ayi bikin a gama saboda a shirye nake.

Malam dakata mini dan Allah, wani irin ganɗoki ne haka daga ganin ɗan fawa sai miya tayi zaƙi, to baka yi mini ba kaje can ka nima wata amma ba Najwan Inna ba, ko baka kalleni da kyau bane, nayi maka kala da matar da zaka aura? To nace a kai kasuwa.

Ta ƙare maganar a cikin tsiwa tana murguɗa masa baki ta juya fuuu ta wuce ranta a mugum ɓace, Atiku kuwa tsayawa yayi kamar gunki yana kallonta shi yadda ma take yi masa tsiwan burgeshi tayi dan sai yaji ya ƙara sonta da son mallakanta dan ya nuna mata shiɗin ya isa ya aureta, yayi guntun dariya yana cewa.

Yarinya kenan, hmmm da Atiku kike magana.

Ya ƙare maganar yana girgiza kai sai ya wuce sashin malam dan so yake a yi ta ta ƙare, dole malam yayi wani abu dan ba zai taɓa yarda Najwa ta kuɓuce masa ba. Najwa kuwa tana zuwa falo ta fashe da kuka tana cewa.

Haba Anty kinga mutumin ne kuwa? Baƙinƙirin da shi sai hasken ido da haƙora da yake washe mini su na gani, ga tumbi kamar mai cikin wata biyar wlh ko a ƙafa aka ɗaura mini shi bazan ja ba wannan ba irin kala ta bane balle ajina, wlh bai min ba bana sonsa haka kawai ban gama da wani baƙin cikin ba zaku zo ku kawo mini wani damuwar, dana auri wannan gwara na mutu ba miji Allah.

Ta ƙare maganar tana jan tsaki tare da share hawayenta, sororo Anty Saleema ta yi tana kallonta har sai da takai aya, tayi murmushin takaici tana cewa.

Allah yasa baki masa wulaƙanci ba dan wlh baki isa ki watsa mini ƙasa a ido ba, kuma malam bazai taɓa yarda da haka ba domin ba a yi masa musu a gidan nan, duk abinda ya yanke wa yaro bai isa ya ce a'a ba, hatta muma haka ne.

Faɗa mata da kyau Saleema tasan waye Malam Umar, har ke wacece da zan kawo miki miji kice baki so, to wlh baki isa kina zaune a gidana ba kice ba zaki bi dokata ba ƙarya kike yi yarinya, dole ki aje duk wata tashen balaga kibi zaɓina in ba haka ba hukuncin da zan ɗauka a kanki ba zai taɓa yi miki daɗi ba, aure da ke da Atiku babu fashi kamar anyi angama.
Chapter 82 · 0% Book details