← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 98

Sashe 39

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da suka koma Abuja yake fama da rashin lafiya a tsastsaye, yayi ta zarya asibiti aka ce ya kamu da hawan jini ga kuma ulcer wanda dalilin damuwa da rashin cin abinci ya ja masa wannan ciwo, haka ya rame duk wannan ƙibar babu hatta tumbin da yake dashi ya tafi, ya dawo asalin bafulatanin Meyere sai karan hanci ake gani da kwala kwalan ido, saboda jinya har hutu ya ɗauka a gun aiki, ga rigimar su Abi da suka matsa masa akan dole sai ya mayar da su gun mamansu, musamman Amrah da ta fi Abi kawazucin uwa, lallashinsu yake yi da basu baki sai sun samu hutu zai kai su, dan tuni ya sama musu makaranta suka fara zuwa, sannan ya sama musu mai dafa abinci namiji dan shi ya buƙaci haka, wani abokinsa ya samo shi shima ɗin sai da aka yi masa gwaje gwajen ciwo aka tabbatar free yake ba cutar da ke damunsa kafin ya fara yi musu girki kuma ba laifi ya iya. Sannan drivernsu dake nan Kaduna shine ya je can ya cigaba da kai su makaranta, damuwarsa ɗaya ne yana buƙatar mace da zata riƙa zama dasu a gida in baya nan musamman in sun dawo daga makaranta. Hakan yasa ya kira wata gaggonsu ƙanwar Abba dake Meyere ita Allah bai bata haihuwa ba kuma mijinta na farko rasuwa yayi na biyun fara aura rabuwa suka yi saboda zaman nata yaki daɗi da kishiyarta, shiyasa ta aje auren tunda girma ya fara kamara ta cigaba da sana'ar cikin gida, lokaci zuwa lokaci tana zuwa Kaduna gurin su Alhasan, ita kawai Aminu yaji ya kira ta dawo gunsa da zama dan tana buƙatar taimako tunda ita ba ɗa gareta ba, koda ya sanar sa ita buƙatarsa tace ba damuwa zata zo, lokacin bikin Salma da bata ga yazo ba tana ta magana, sannan taji labarin ya saki matarsa abin bai yi mata daɗi ba, taso kiransa amma Allah bai nufa ba, yace ai bakomai jarabawarsa kenan, idan ta tashi zuwa zai aiko da driver ya ɗauketa, tace ya bata kwana biyu zata kira shi in ta sallami bashin da ake binta itama ta karɓi nata da ta ke bi, a haka suka yi sallama.

Sati guda a tsakani Baba Saude ta zo Abuja Su Amrah sun ji daɗin ganinta wanda hakan yasa suka rage damun Aminu maganar mamansu, ko shi Aminu yaji daɗin zuwan Baba Saude domin ta rage masa damuwa sosai da yawan tunani, dan sai su raba dare suna hira tana bashi labarin garinsu da mutanen daya sani, da yake ta iya bada labari kuma shima yana son irin labaran, hakan yasa ɗan nutsuwarsa ta fara dawowa ya koma walwalarsa sai dai ba kamar na da ba. Ko lokacin da Sameeha take ta kiransa yasan tana so ya haɗa ta da yaranta ne, amma yayi biris yaƙi ɗagawa dan baya so tayi magana dasu su zo su riƙa damunsa akan ya kaisu gunta, shiyasa ma daga baya yayi blocking layinta ya cigaba da lallaɓa rayuwarsa da yake ji tamkar ma mutuwa zai yi. Haka aka shafe wata uku da kwanaki wanda yayi daidai da lissafinta Sameeha ta fita idda, duk da saki uku yayi mata amma kafin tayi wani aure dole sai tayi jini uku, kuma a lokacin yaran sun samu hutun makaranta, suka dame shi akan ya kai su kaduna tunda yayi musu alƙawari, amma yace suyi hakuri zasu je Ilori wani samina zai je kuma tare dasu zai je su raka shi. A lokacin ne Hauwa ta kirashi akan batun zuwansa Kaduna daya ce sai yara sunyi hutu, yace mata wani aiki ya taso masa zasu je Ilori sai dai in sun kuma samun wani hutu na gaba, cikin faɗa Hauwa tace.

Kenan ni ka mayar dani mutumiyar banza, na dage akan maganar aurenka har na saka wa É—iyar mutane rai amma kana son bani kunya sai wasa kake mini da hankali.

Haba taya zan miki wasa da hankali, ai ni nace na amince.

To yanzu ya kake so nayi? Kuma nace a wannan watan zaka zo ayi maganar aure amma abu yaci tura, ko yaranyar ma baka sani ba balle kuyi waya ku fahimci juna.

To yanzu ya kike so ayi? ni dai bazan fasa tafiyata ba tunda abu ne daya shafi aiki na.

Idan ka amince zan je na samu su yaya suje gidan su yarinyar su nima maka aurenta, sannan zan tura maka number É—inta ka kirata ku fara zance.

Murmushin gefen baki yayi yana mamakin ƙarfin halin Hauwa.

To shikenan ki same su kuyi magana zan tura musu da kuÉ—in sadaki ayi komai ba sai ina nan ba, amma ko sunan Yarinyar ma ban sani ba yaya.

Najwa sunanta, kuma wlh kyakkyawa da ita har tafi Sameeha kyau ga kuruciya.

Hauwa ta faɗa cike da farin ciki a fuskarta dan rabon data yi farinciki haka tun lokacin da ya saki Sameeha, bata ɗauka zai yarda da maganar a yanzu ba, Hmmm yace ya kashe wayar yana maimaita sunan Najwa a zuciyarsa, tamkar ya taɓa sanin wata mai irin sunan amma ya manta ssboda sabgogi sunyi masa yawa, kuma rabuwarsa da Sameeha ya goge masa memory ɗinsa da yawa. Baba Saude ce ta fito daga ɗaki tana cewa.

Sai naji kamar waya kayi da Hauwa.

Yace mata eh kana ya kwashe yadda suka yi ya faÉ—a mata Baba tayi murmushi tana cewa.

Hauwa rigima, ai gwara daka amince ayi ɗin, tunda zama haka ba mata da sauran ƙuruciyarka bai dace ba, itama Sameeha ba zama zata yi ba aurenta zata yi, gwara duk ku karɓi ƙaddararku hannu biyu.

Aminu murmushi yayi shi kaÉ—ai yasan yadda yake ji a zuciyarsa, kamar zai faÉ—a mata lalurar da yake fama da ita sai yayi tunanin in taji zata hana auren da Hauwa ta haÉ—o masa, shi kuma yana so yayi auren dan yayi maganinta. Yace.

Baaba ina so ku shirya gobe In Allah ya kaimu da safe wajen goma zamu tafi Ilori, za muyi kusan mako biyu a can.

Ilori wannan yaro, ashe zamu sha zaman mota.

A'a jirgin sama zamu hau dan har nayi mana buking ticket.

Ikon Allah Saude a jirgi taf! Allah yasa zan iya, dan naji ance akwai É—aga hankali tashin jirki sama, har 'yan hanjin mutum sai ya kaÉ—a.

Baaba da nake yi miki shirin Hajji bana dake za ayi, kice ba zaki iya zuwa ba.

Zuwa kai É—an nan, garin Manzo s.a.w fa, ai ko kasaye hanjin cikina zanyi wlh sai na je.

Aminu ya kwashe da dariya su Abi suna tayashi, itama dariyar tayi tana cewa.

Yo makka fa! wanda ban taɓa zata ba ko a mafarki, wlh ko da jan giuwa ne sai na je.

Haka suka cigaba da hira gwanin sha'awa, haƙiƙa zaman baba Saude a gidan Aminu ya sauya rayuwarsa daga damuwa sosai, ya samar masa da farin ciki shida yaransa.

*****

Hauwa da Najwa.

Da yamma Hauwa ta garzaya babban gida tayi sa'a Alhasan ya dawo, nan ta zauna ta rattafa masa yadda suka yi da Aminu, yace shi bai yarda ba sai da ya kira shi ya tabbatar kafin yace zasu suje nima masa auren Najwa, sannan ta sanar da iyayen yarinyar su faɗi ran da zasu je, nan take Hauwa ta kira Najwa a waya, Najwa da take haɗa gawayin girki taji wayarta tana kara a ɗaki, tayi sauri ta miƙe zata je ta ɗauki wayar, sai inna ta dakatar da ita.

Wlh koma ki haÉ—a wutar nan dan in kika É—auki wayar nan yau bamu ba cin abinci dare da wuri, dan kin zama aljanar waya hatta haddar naki ya zama shiriri kin daina zuwa makaranta saboda kin sakawa kanki shirme.

To inna wlh Haddar ce ya daina shiya, sai in dage inyi karatu sai naje badawa na kasa, shiyasa na hakura.

Hmmm to kin sakawa kanki jarabar son aure kuma saurayin da kike ta faÉ—a zai turo shuru muke ji É—an sanda yaci shirwa.

Zai zo ne In Sha Allah, ba zama yake ba sai a waya muka hira shiyasa.

Allah yasa ba irin mayaudaran nan bane, ya jirgaki a banza kina zaman jiransa.

Ni dai ki bari na duba wanda ya kirani, kinga har sau biyu ana kira, wata ƙila ma shine ya kira.

Inna bata ce komai ba ta cigaba da gyara kayan miya da zata jajjaga na dafadukan shinkafa da za suyi na manja, ganin bata ce komai ba yasa ta wuce ɗaki ta zauna gefen gado tana dubawa taga Hauwa ce, cikin zaƙuwa ta danna mata kira ringing ɗaya Hauwa ta ɗauka bayan sun gaisa Najwa ta bata hakuri akan bata kusa da wayar ne.

Diyar Albarka babu damuwa dama maganar aurenku ne ya taso, ina so ki tambayi iyayenki yaushe za a zo nimawa Aminu aurenki.

Wani irin miƙewa Najwa tayi cike da tsananin farin ciki dan ta daɗe tana jiran zuwan wannan ranar, tace zata sanar da inna in sun yanke ranar zata faɗa mata, haka suka yi sallama ta kashe wayar, Najwa ta daka wani uban tsalle tana ihun wayyo Allah daɗi.

Da sauri inna tabar abinda take yi, ta leƙo ɗakin ta duba me ya sameta, dan har ga Allah tayi zaton ko wani abin tashin hankali ne aka faɗa mata a wayar.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

26.

Najwa ganin Inna ta leƙo ta isa garena tana dariya.

Inna albishirinki?

Wani kallo Inna tayi mata mai É—auke da harara sai Najwa taja da baya tana cewa.

KuÉ—in aurena fa za a kawo nake so na faÉ—a miki, yanzun nan aka sanar dani na faÉ—a muku ku saka ranar da iyayen Muhammad zasu zo.

Kina da hankali kuwa Najwa? Yaron da bamu sanshi ba shi ne zai turo.
Chapter 39 · 0% Book details