← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 98

Sashe 51

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Afwan yau aiki nasha kunsan ana ta shirin tarban Ramadan Allah yasa muga farko da ƙarshensa lafiya. Yasa mu kasance cikin 'yantattun bayi*
_Mun kusa tafiya hutu sai bayan sallar In Allah ya kaimu zamu cigaba. Naso na gama kafin azumi amma bazai yiwu na guntule labarin ba, dan akwai abubuwan daya kamata a bisu daki daki._
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

34.

Ƙaurin da inna taji na abincin dake wuta yasa tayi saurin fitowa daga ɗaki tana sababi, ta isa da sauri ta sauke ta mayar da tukunyar holoƙo ta saka ruwan wanka kana ta nufo ɗakin Najwa dan tayi mata faɗa akan ƙin sauke abincin da bata yi ba, Najwa tana jin motsin zuwan Inna yasa ta danne kukanta ta bawa ƙofa baya, Inna ta ce cikin faɗa.

Wani irin shirme ne Najwa kike yi, nace ki sauke abinci amma kin samu guri kin kwanta, kin ma yi sallar magriba kuwa?

Kaina ke min ciwo tun ɗazu da rana, da yamman nan kuma zazzaɓi nake ji da kyar ma na ɗaura girki, ɗazun mantawa nayi ban faɗa miki ba.

Assha yanzu haka maleria ce, Allah ya sauke, bari Junaidu ko Sadiq su shigo sai a samo miki magani kisha, amma ki tashi kiyi sallah in baki yi ba.

To Najwa tace mata, inna kuma ta juya zuwa ɗakinta sam bata gane halin da Najwan ke ciki ba, har zuciyarta ta yarda da ba tada lafiya ne tunda gashi ya nuna ma a muryarta da yayi sanyi. Najwa miƙewa tayi ta zauna tana jin wani tuƙuƙin baƙin bakin ciki yana ratsa illahirin zuciyarta da gabbai, sai ta miƙa hannunta gefen gado data aje wayarta ta dubo number ɗinki Hauwa ta danna mata kira, bugu ɗaya ta ɗauka Hauwa tana cewa.

Amarya kinƙi ambato muna zancen ki sai ga shi kin kira, muna nan muna ta hada hadan haɗa akwatinki, kin san ke twmu ce komai muna su muyi shi waja wajaba laranta.

Hauwa ta kai aya a maganarta tana saurare me Najwa zata ce mata, Najwa sai da ta lumshe ido kafin ta ja fasali tace cikin sanyin murya.

Anty Hauwa kin samu labarin auren Sameeha da ƙanwarta Ikram da za ayi, ta samu miji ɗazun nan aka kawo kuɗin aurensu, sadakin Sameeha dubu ɗari biyu Ikram kuma dubu ɗari uku, abu kamar a film.

Kutumelesi au Sameehan har ta samu miji? Ashe duk son da takewa Aminu ƙarya ce tunda gashi ko shekara bata yi da fita ba zata yi aure, to su waye zasu auresu haka? naji kin ambaci kuɗi masu yawa na sadaki.

Ikram dai ɗan wazirin Zazzau zata aura Sameeha ce dai bamu sani ba amma ance mai kuɗi ne kuma ɗan uwan mijin Ikram ne, abu dai wlh kamar almara, nima nayi mamakin wannan daraja da suka yi musamman Ikram da take baƙa ba ta da fasali.

Hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, yanzu haka asiri suka nima har suka samo su, tunda kin san Sameeha ta saba da gidan kuɗi ba zata yarda ta faɗawa talaka ba, kuma ta saba damin malamai kin ga kuwa ba abin mamaki bane in ta samo mai ƙumbar susa, In sha Allah muma za muyi miki kaya na gani na faɗa tunda kema ba talala zaki aura ba, saboda Aminu yanzu ma yake tashen kuɗi, ina saka ran kina shiga gidansa zaki samu motarki ta hawa.

Allah Anty? Ni dai ina fargaba in ya gano nice matarsa, kamar bazai karɓeni ba ina jin fargaba sosai akan haka.

Ke rabu dashi, an gaya miki haka zan barshi, dole zan nima miki taimako yadda zaki samo kansa sosai, ke dai ki cigaba da shiri kawai ki kwantar da hankalinki kamar kinyi bako ya mutu.

Har naji daÉ—i Anty Hauwa dan wlh tunda naji batun bikin su Sameeha naji hankalina ya tashi, naso ma ace an riga É—aura nawa kan nasu, dan su wata biyu aka saka.

Karki damu kanki gaggawa aikin shaidan, ki rabu dasu yanzu haka ba su shuka alkhairi ba shiyasa suka saka da wuri, mu za muyi namu a tsanake kuma In Sha Allah bikinki sai ya fi nasu armashi.

Najwa sai da ta saki murmushi jin maganar Hauwa dan sosai zuciyarta ta yarda da maganarta, duk da ƙasan zuciyarta ta san Sameeha bata bin malamai, sannan ga Ikram da zara auri ɗan gidan sarauta hakan yafi tsaya mata, haka suka ɗan taɓa hira daga bisani suka yi sallama, sai ta aje wayar ta wuce tsakar gida dan tayi alwala, duk da har yanzu bata dawo dai dai ba amma maganganun Hauwa sun ƙara mata kwarin guiwa.

*
Hauwa.

Suna aje wayar take kallon Laure da suke zencen akwatin Najwa da Aminu ya fara turo mata da kuÉ—i, dan musamman taje babban gida dan su tattauna maganar, Hauwa ta labartawa Laure yadda tayi da Najwa duk da ta gane inda hirar ta dosa da suna waya, Hauwa ta kare da mele baki.

Kinji dai tsautsayi ta faɗawa wani zai kwashi Sameeha alaƙaƙai, Allah dai ya sa su kwashe lafiya.

Hmmmm ko kuma auren kashe wuta zata yi ba ta dawowa Aminu, dan kinsan irin son da take masa na tabbatar zata iya aikata haka.

Allah ya kyauta kima daina yi mana wannan fatan domin mun riga da mun yada kwallon mangoro mun huta da ƙuda, Aminu ba zai taɓa sake dawo mana da ita ba wlh, ke duk inda zan shi to zan fita in tabbatar da haka bai faru ba. Ita da shi haihata haihata.

In Sha Allah kuwa, domin bazan taɓa mance sakin data jawo mini ba, annoba ce Sameeha bana fatan ta dawo, suje can su karata sai dai tayi wa wasu fi'ili. Yanzu sai ki kira Aminu ki faɗa masa imma zai saki jiki yayi aurensa da zaifi masa, dan Sameeha ma ta mance da shi.

Kuma fa hakane, bari na kirashi kinga yanzu ya zage yayi aurensa in ma yana tunanin Sameeha ne sai ya daina.

Cewar Hauwa data ɗago wayarta ta shiga wajen kira ta danna number ɗin Aminu. Har ya kusa tsinkewa kafin ya ɗaga ta ƙara a kunne suka gaisa kana Hauwa ta shiga koro masa bayanin auren Sameeha har da karin gishiri a miya, Aminu sosai yaji maganar ta daki zuciyarsa dan bai ɓata zaton Sameeha zata yi aure nan kusa ba, sai sabon sonta ya taso mata tare da kishinta sosai, duk da lamarin ya taɓashi cikin dakiya yace.

Amma yaya Hauwa a ina kika ji wannan labarin? anya ba karyar mutane bane?

Haba Aminu ai da ban tabbatar da maganar ba bazan kira na faɗa maka ba, kuma daga majiya mai ƙarfi na ji, kasan zancen aure baya ɓoyo, ka sani ma ko taji labarin naka auren.

Da taji zata yi mini maganar ko ta tambayi yara tunda suna waya. Amma ke waye ya faÉ—a miki an kawo kuÉ—in aurenta.

Au baka yarda ba kenan? To sai ka kirata ka tambayeta tunda kana da numbern ta nasan ba zata ɓoye maka ba tunda ba igiyar aurenka akanta, waya sani ko auren huce takaici zata yi ko na kashin wuta danta dawo maka.

Sameeha ba zata taɓa yin haka ba, na santa nasan halinta, domin tana da sani na addini ba zata yi auren kisan wuta ba.

Hmmm ashe har yanzu dai da sauran ƙimarta da kake gani, to ai sai ka kirata kaji daga bakinta tunda ni baka yarda da maganata ba, koma dai miye yanzu ba aure a tsakaninku taje taita auren Allah yasa ta zauna.

Hmmmm shikenan na yarda Allah yasa alkhairi, ya batun akwati kun fara siyan kayan ne?

Yaushe ka turo kuÉ—in da zamu fara? Muna dai shirye shirye ne.

To Allah ya taimaka sai anjima.

Cewar Aminu yana kashe wayarsa bai jira amsarta ba, Hauwa ta aje waya a ƙasa tana 'yar dariya.

Kin ga ko bai wani damu da maganar aurenta ba, ina ga dai Aminu ya daina son yarinyar nan asirin da suka yi masa ya rabu dashi maganar ma kayan akwati yayi fa yanzu.

To ba dole yabar jikinsa ba saki uku fa yayi mata, Allah kaɗai yasan tsawon lokacin daya ɗauka yana cin ƙamu ƙamu, dan irinsu Sameeha har tsafi zasu yi dan su mallake namiji, balle Aminu yanavda abin hannunsa da dole ma ta bi malamai dan kar wata ta shigo mata gida.

Mun dai rabu da alaƙaƙai aje cen a yiwa wasu.

Cewar Hauwa, haka suka cigaba da hira wanda rabi zagin Sameeha suka dinga yi suna rage mata zunubi, tare da mugun fata akan Allah yasa auren ma kar yaje ko ina kowa ya gane ba 'yar kirki bace ita.

*

Aminu.

Miƙewa yayi ya soma kai komo dan sosai abin ya taɓashi, bai taɓa zaton zai damu ba in yaji Sameeha zata yi aure, amma sai gashi ya samu kansa cikin mawuyacin hali har yake jin da zai ganta a gabanshi sai ya rufeta da mari saboda kishinta daya ji yana fusgarsa har wani hucin zafi yake fitarwa, ya kasa haɗa tunaninsa guri guda dan gani yake kamar Hauwa ƙarya take yi, saboda a ganinsa yayi wuri ace Sameeha tayi aure dan bata jima da fita idda ba, amma kuma ƙila ko auren huce takaici zata yi domin ta bashi haushi, haka ya dinga haɗa tunani ya rasa matsaya sai kawai ya yanke shawarar kiranta, ya isa centre table ya ɗauki wayarsa ya duba agogo takwas saura, ganin dare bai yi sosai ba yasan idonta biyu, sai ya danna number ɗinta nan take kuwa ta shiga ya kara a kunne.

*
Sameeha.
Chapter 51 · 0% Book details