Sashe 58
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan sallar magrib aka kawo motoci da zasu ɗauki amare, Ikram aka fara kaiwa wanda Sameeha sai da tayi mata rakiya zuwa gidanta dake umguwar sarki, babban filat mai kyau iya ganin mai kallo, yaji kaya na zamani da komai ga sabuwar motarta a tsakar gidan an parker, sai da suka yi sallar Isha'i kafin aka ɗauki Sameeha daga gidan Ikram aka wuce da ita gidan mijinta dake unguwar rimi, wato gidansu Khairy a babban part wato gidan sama dake tsakiya, nan Ibrahim ya gyara mata aka zuba komai akan in an gama biki zai wuce da ita Abuja gidansa dake can dan a Abuja zasu zauna, sai dai ya riƙa zuwa yana duba Hajiya da uwargidansa, can gidansa na Abuja a gyare yake an ƙara zuba masa kaya na buƙata sosai, Abujan da Sameeha ta guda da farko gashi Allah ya nufa dole sai ta zauna a can. Bayan sun isa sai da aka fara kaita sashin Hajiya ta gaishe su kafin aka kawota nata sashin, faɗar haduwarsa ma bata lokaci ne dan falon ƙasa komai nata ne da Yaya Zaidu yayi musu oder, falon sama ne Ibrahim yayi nashi hidimar, su Hauwa dai anga abinda ya kusa sasu suma dan kuwa sun gama santin gidan Ikram da gidan Aminu ko rabin kyansa bai kai ba, sai gashi na Sameeha ya ninka na Ikram kuma gidan sama ne, gida ne da yake da gate kusan uku, gate ɗin farko za a wuce a shiga na biyu wanda za a ga titi gabas kudu yamma, to a titin dake ɓangaren kudu za a miƙe a isa gate ɗin gidan Sameeha, dama sashin Hajiya daga ɓangaren gabas yake a cikin gate na biyu, haka mutune suka dinga yiwa su Sameeha murna domin sun taka gadar nasarar rayuwa, daga bisani aka mayar da kowa gida aka bar amare a gidansu.
Wajen ƙarfe goma sai ga Ibrahim ya shigo sashinsu ba kowa a falo sai ya wuce ɗakin da yake matsayin na Sameeha a nan falon ƙasa, ya tura ƙofa da sallama ya sameta saman gado ta kwanta a gefe, shigowarsa yasa ta miƙe ta zauna tana amsa sallamarsa, ya zauna a gefen gadon ta shiga gaishe shi ya amsa fuska sake yana cewa.
Barka da baƙunta amayar Iro, kiyi haƙuri an barki ke kaɗai a hankali zaki saba. Bari na watsa ruwa ina zuwa.
Ya faɗa yana miƙewa, sai Sameeha ta tareshi da cewa.
Dan Allah ina so ka bani lokaci kaÉ—an zamu yi wata magana.
Ibrahim sai ya koma ya zauna yana sauraren ta, jakarta dake gefe ta ɗauko ta ciro wayar Ikram ta buɗe wajen massage ta miƙa masa tana cewa.
Ɗazun da yamma aka turowa Ikram wannan saƙon shine nace bari na fara tattaunawa da kai dan bamu faɗawa kowa ba.
Ya amsa wayar ya karanta ya ƙara karantawa cike da mamaki, bai ce komai ba sai wayarsa daya ciro a aljihun gabar rigarsa ya danna number ɗin Shamsu ya kirashi, yana ɗauka yace.
Ka isa gida ne?
Eh na iso amma Ikram tana ta kuka tunda na shigo, sai maganganu take faÉ—a mini na rasa ina zancenta ya dosa.
Oka gamu nan zuwa.
Abin da Ibrahim ya faÉ—a kenan, ya kalli Sameeha yana cewa.
Tashi mu je gidan.
Hmmm ai shiyasa na amsa wayar dan nasan halin Ikram ba tada haƙuri wlh, kuma sai da nace mata tabar komai a hannuna shiyasa ban tun kari kowa da maganar ba sai kai yanzu.
Tashi dai muje In Sha Allah zamu gano wacce ta turo da wannan saƙon.
Ya miƙe yana gyara mazaunin babbar rigarsa, Sameeha ma miƙewa tayi dan da mayafi a jikinta suka fito tsakar gidansu ga motar daya sauka yanzu, ya buɗe mata mazaunin kusa dashi ta shiga ya rufe kana ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya kunna mota tare da hon mai gadin sashin ya buɗe masa gate kana ya fice da motar.
****
Najwa.
Tunda ta koma gida ta ƙasa komai sai saƙa da warwara, gani take in tabar Ikram da Shamsu sun ci bilis, shiyasa ta kashe wayarta gabaɗaya dan kar a dameta da kira, tana buƙatar zurfafa tunaninta akan hukuncin da zata ɗauka akansu, har wajen sallar azahar tana a kwance, da kyar ta miƙe ta gabatar da salla tana zaune bisa dadduma, dabarar turawa Ikram text ya faɗo mata, sai ta miƙe da sauri ɗan har wani kuzari ta samu saboda a yau tana so Ikram da Shamsu kar suyi kwanan farin ciki, dadduma ta naɗe ta zari jakarta ta fice zuwa bakin titin layinsu shagon mai sayar da layin waya, ta sayi layin MTN sabo mai register kana ta dawo gida ta saka layin a ƙaramar wayarta sai ta soma rubuta tex ɗin, data gama tayi saving ta aje har sai da aka yi sallar La'asar kafin ta turawa Ikram tana dariyar mugunta.
Yau za a ci amarci da tashin hankali dan nasan Ikram ba tada sauƙi sai ta ɗaga masa hankali, Ni kuma haka nake so, kuma zan cigaba da tura mata saƙo yadda rikici zai cigaba da wanzuwa har sai Shamsu ya nima wacce ke tura sako, idan ya nima mu haɗu na bashi dama daga nan na shigar da nawa buƙatar, Wlh zan iya fasa auren Aminu In dai ya amince da aurena.
Cewar Najwa a zahiri kamar mai taɓin hankali, ɗan sosai shaiɗan ya ƙara samun gurbi a zuciyarta yana haska mata Shamsu yafi Aminu shine ya dace da ita a yanzu. Haka ta dinga saƙa da warwara har aka yi sallar magrib, tayi zaton Ikram zata kira layin amma shuru hakan yasa ta kashe wayar da layin ke ciki ta kunna asalin babbar wayarta data kashe ɗazun, ita kaɗai a gida kamar mayya, dan inna can zata kwana kamar yadda itama take kwana akan, tasan mazan gidansu sai dare yayi zasu shigo tunda ba abinci zasu samu ba a gidan, har aka yi isha'i tana a haka, data idar ne ta fita zuwa waje ta siyo biredi da ruwan bunu ta dawo ta haɗa tea mai kyauri ta sha ta kwanta, a haka har barci ya ɗauketa da tunani barkatai.
Shamsu da Ikram.
*Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.*
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
38.
Ikram da Shamsu.
Ya shigo da abokansa su uku falon yace su jirashi, sai ya isa bedroom ɗin Ikram akan ya kirata su gaisa amma sai ya samu ɗakin a rufe, ya buga bata buɗe ba sai ya shiga kiranta a waya yana ringing amma ba a ɗauka ba, ya shiga yi mata magana akan tayi haƙuri ta buɗe amma ta nuna tamkar bata cikin ɗakin, cikin sanyin jiki ya dawo gurin abokansa yana basu hakuri akan amarya ta ɓoye kanta, basu wani damu ba sun san ko wace amarya da kalan na ta salon dan haka suka yi masa sallama suka wuce, har mota yayi musu rakiya da suka wuce ya dawo ciki ya isa ɗakinsa ya watsa ruwa ya saka jallabiya kana ya ɗauki extra key a drower ya fito ya isa ɗakin Ikram yayi sa'a ta cire key a jikin ƙofa, yana sakawa ya buɗe ya shiga, Ikram tana ganinsa ta zabura ta miƙe tana cewa.
Karka kuskura ka matso kusa dani in ba haka ba zanyi maka abinda baka taɓa tsammani ba, Shamsu nayi dana sanin aurenka kuma kasa a ranka ba zaka taɓa samun abinda kake so a gareni ba, ka fita bana son ganinka.
Ta ƙare maganar a tsawace tana kuka ganin yana matsowa kusa da ita, tsananin mamaki yasa Shamsu kasa magana dan ya rasa ina maganarta ya dosa balle ya iya hasko inda matsalar take, cikin dakiya da danne damuwa ya soma cewa.
Haba amaryata ki kwantar da hankalinki ni babu abinda zan yi miki, yanzu ki zauna muyi magana.
Babu maganar da zan ɓata lokaci nayi maka domin ka gama ɓata rawanka da tsalle, na dai gaya maka baka isa ka samu abinda kake nima a guna ba, da zaka fita dana fi jin daɗi dan bana ƙaunar ganinka.
Shamsu yana shirin yin magana sai wayarsa da ya saka a haljihun gaba ta soma ƙara, sai ya ciro yaga Ibrahim ne ya ɗauka da sauri har suka yi magana kana ya kashe wayar yana duban Ikram.
Yaya Ibrahim da Anty Sameeha suna hanyar zuwa nan, duk da ban san dalilin zuwansu ba amma hakan yana da yanada alaƙa da wannan rikicin da kike yi mini, dan haka ki daina kuka koma miye gaskiya zata yi halinta In Sha Allah.