← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 98

Sashe 85

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun bayan bikin Najwa ta soma laulayi kaɗan kaɗan sai dai kwaɗayi yafi yawa a ciki, da suka je asibiti likita ya tabbatar tana da shigan ciki wata ɗaya har da sati biyu, farin ciki wajen Shamsu ba a magana haka ma su Khairy sunji daɗin labarin dan Shamsu ita ya fara faɗawa ta sanar dasu Hajiya, nan suka yi musu fatan alkhairi da sauka lafiya. Musamman Hajiya ta aika cousin ɗin su khairy Zainab wacce take gabanta domin ta riƙa taya Ikram ayyukan gidan tunda har lokacin ba a samar mata mai aiki ba, kuma itama bata so domin tace tana tsoron masu aiki saboda abinda ya samu Sameeha. Umma ma taji daɗi labarin cikin, nan ta soma ɗawainiya da ita dangin kayan kwaɗayi tana aika Zaidu yana kai mata. Sameeha kuwa taso zuwa Kaduna dan ta ganta amna Ibrahim ya hana dan baya so tayi nesa dashi ko kaɗan, a waya dai suke magana tana jin lafiyarta. Kwana biyu daya wuce ne taci wani alale data saka Shamsu ya siyo mata a wani rastaurant taci shine ya sakata gudawa da amai duk ta galabaita, dalilin zuwanta asibiti kenan aka bata gado, Hajiya data samu labari ba ƙaramin faɗa tayi wa Shamsu ba akan me yasa bai faɗa ba tasa anyi mata a gida bata son suna cin abincin wajen nan saboda basu san yadda aka haɗa shi ba, nan ya bara haƙuri akan bazai kuma ba, shima a tsorace yake saboda kar cikin ya zube dalilin haka, sosai yaji haushin kansa daya sayo mata abinda ya illatata. Umma kam Ikram ɗin ta yiwa faɗa akan in ita ba zata iya dafawa ba me yasa bara kirata ta girka mata ba, taso ta zauna jinyarta amma su Hajiya suka ce ta barshi wata dattijuwa mai girka abincin gidan Hajiyar itace ta zauna da ita tare da Zainab, kuma tana samun kulawa sosai dan har ta fara dawo da jikinta data rame a lokaci guda.

Inna tana isa ta wuce dakin da aka kwantar da ita nan asibitin garkuwa, wanda yake ita kaɗai ce a ciki ba wasu marasa lafiyan. Ta samu umma ma tazo tana zaune tana matsa mata akan tasha tea ɗin da aka haɗa mata amma taƙi sha, tana ganin inna da Kwanko ta haɗiye miyau dan dama tasan Inna zata kawo mata abu bata faɗa musu bane, inna suka gaisa da umma da Zainab dan baba Jimmai ta koma gida ta dawo, nan Ikram ta gaisa da inna tace cikin zaƙuwa.

Allah yasa kunu da ƙosan ne Inna kika kawo mini.

Aiko shine, da wuri na tashi na haɗa komai saboda ke, muma dashi muka karya babanku yace a yi miki ya jiki yana nan zuwa su Junaid ma suna ƙara yi miki ya jiki.

Ina amsawa Inna, ai basu daÉ—e da fita ba ma yaya Junaid É—in kika zo.

Dama sunce zasu biyo su duba ki. Ga kunun ki fara sha saiki aje tea É—in da naga baki son sha.

Aiko gashinan ina ta godo da ita taƙi sha ashe tasan da zaki kawo mata abu. Ni wainar fulawa ma nayo mata taci kaɗan wai sai anjima, kuma ita ta saka nayi mata

Cewar Umma, Inna tayi dariya tana cewa.

Kin san ko wani juna biyu da nashi laulayin ita kuma a haka yazo. Allah ya rabasu lafiya.

Amin suka amsa Ikram dai tuni ta fara shan kunu da Zainab ta zuba mata a kofi tana yagar ƙosai cike da farin ciki. Inna kuma ta samu wajen zama tana bawa umma labarin dawowar Najwa dama abinda ya faru, umma tace cikin jin daɗi.

Ai wlh Zulai gwara data dawo gurinki domin tarbiyyar yanzu dole sai uwa, balle Saleema itama yaushe tayi hankalin, nasan ba ƙaramar taɓara zata bari Najwan tayi ba, kuma kema karki takurata ki riƙa janta sosai a jiki kina nusar da ita rayuwa In Sha Allah zata gyara halinta.

To zanyi Haleema ai ya zama dole na rungumi ƙaddara tunda Allah ya jarabceni da Najwa, nima wlh tun sanda ta tafi da aka kwana biyu sai naji gidan yayi mini faɗi, naji son ta dawo amma ban furta ba na cigaba da addu'a.

To Allah ya shirya mana ita, in banda Abin Saleema ai ba a nuna wa yaro dole, taya zasu tilasta mata auren wani basu suka haifeta ba da kuma ranku, sun so kansu da yawa.

Umma ai maganinta kenan dama wlh an É—aura auren muga ta tsiya.

Cewar Ikram, umma ta danƙara mata harara sai ta sunne kai tana ɗan murmushi ta cigaba da karyawa, inna tace.

Daina hararanta halin Najwan ne sai kaji kamar ka nakaÉ—a mata dukan tsiya. Yanzu ta dawo zan sha surutu da fama, Allah ya bani ikon cin wannan jarabawar.

Ameen amma ki daure ki jata a jiki sosai kuma banda yawan faɗa irin su Najwa lallaɓasu ake yi Zulai.

In Sha Allah zanyi haka.

Nan suka cigaba da tattaunawa daga bisani kuma Innar tayi musu sallama ta tafi.

****

Binafa.

Hotunansu da wasu suka ɗauka shine suka yi sharing a facebook tare da labarin abubuwan da suka aikata har aka yanke musu zaman gidan kaso, a wannan lokacin duk wanda basu san da labarin ba a danginsu sun sani, wanda Nafeesa ma a facebook ɗin ta gani tayi matuƙar girgiza da lamarin wanda hakan ya ƙara mata shiga hankalinta ta kuma kama aurenta, musamman momynsu ta kirata a waya ta kuma ja mata kunne akan ta kama mijinta da aurenta da kyau dan ga abinda ya samu Binafa nan gwanin tausayi, Nafeesa ta tabbatar mata da zata kama kanta da aurenta gabaɗaya dan yanzu duniya ta koya mata hankali sosai. Hakan yasa ta cigaba da kyautatawa mijinta suka buɗe sabon shafin soyayya, da yake Sadi shima ba baya ba gurin tsafta dan sosai yake gyara kanshi saboda suji daɗin mu'amala, kuma yasan Nafeesa tana son namiji ɗan gayu yadda yake ganin samarinta a da suna zuwa fes dasu, shima ya ɗauki damarar yin duk abinda zai riƙa burgeta dan ya samu Zuciyarta.

Sameeha itama ta samu labarin abinda ya faru saboda Zaidu ne ya gani a facebook yayi mata copying ya tura mata a WhatsApp dan bata yin facebook, nan tace sakayya ce daga Allah ko haka Allah ya barsu ya gama wanke mata zuciya ta kuma ƙare da fatan shiriya. Umma ma ta gani dan Zaidu sai da ya nuna mata tace sakkayya ce kuma dama wani hisabin tun a duniya Allah yake yinsa, Ikram ma ta gani ita Allah ya kara tayi musu tare da fatan Allah ya cigaba da tona asirin masu hali irin nasu. Najwa ma data gani dariyar mugunta ta riƙa yi tana Allah ya ƙara, ashe gwara ita tunda a iya saki nata ya tsaya suko gashi nan har da zaman gidan yari, cewa ma tayi hakan shine ya cancanta dasu dan sun kaune hanya da yawa, gwara ita zunubinta kaɗan ne, nayi ƙoƙarin kiran Nafeesa dan suyi maganar su Binafa, amma sai yaƙi shiga kwata kwata bata gane tayi blocking ɗinta ba.

Su Binafa tunda suka shiga gidan yari suka gane shayi ruwa ne, saboda a cikin sati biyu jikinsu ma sai da ya tabbatar da sun shigo wani ƙaulin siraɗin rayuwa, sunyi duhu da rama ga wasu ƙuraje da suka fara fito musu a jiki da kwarin da suke cizonsu na rashin sabawa, Hanan dai wahalar tafi nunawa a jikinta dan ita fara ce kuma tana fama da nimoniya, ciwon ya fara damunta tana shan maganin da ake bata a nan gidan, duk da haka 'yan gidansu Binafa suna yo musu aiken abubuwan buƙata amma baya wadatar dasu, fatan su a fitar dasu ne daga gidan, sai dai sunga babu wannan halin.

***

Najwa.

Da yamma ta ɗaura girkin dare harta tuƙa tuwo ta ɗaura miya, tana zaune a tsakar gida tana danne danne a waya, sai ga kira ya shigo tana dubawa taga Mujaheed ne da ta yi masa saving, ta ɗaga kafin tayi magana ya rigata..

Gimbiyata shine ko ki kira ni kiji ya na ƙarasa gida.

Kayi haƙuri nima ban samu zama ba tunda na iso gidan ina fama da aiki, inna ta sakar mini komai.

Ayya karki damu soon zan rabaki da gidan ki zo ki huta a gidana.

Hmmmm ya batun tafiyarka?

Ina ban je ba ai, na tabbatar musu bana son companyn, dad É—inmu yace abinda nake so shi za a yi mini.

Ikon Allah, kace zaman ƙasar Dubai dai ya tabbata.

Sosai ma kuwa sai ki shirya domin dake zani, anjima ina nan zuwa hira in ba zan takura ki ba.

Ba matsala sai ka zo.

Ta faÉ—a tana wani fari da ido na jin daÉ—i, nan yayi mata sallama suka aje wayar Inna tana fitowa daga daki tace.

Waye kuma kike waya da shi.?

Najwa tayi 'yar dariya kana tace.

Kwanan nan In Sha Allah inna zan kuma yin wani auren, kuma ga dukkan alamu na dace dan yace ba a ƙasar nan zan zauna ba, kinga kuwa In Sha Allah mijina sai yafi na Sameeha balle Ikram da take wani nuna mini isa.

Hmmm Najwa ke dai su Sameehan nan ba zasu fita a bakinki ba ko, ba dan Allah za ki auren ba sai dan ki fisu, wai ke yaushe zaki yi hankali ne Najwa, hassadarki tana nimar ta saka ki hauka ko, Allah yasa ki gane.

Haba inna ke da zaki tayi mi murna kike yi mini faÉ—a kuma.

To Najwa Allah yasa mutumin kirki ne shi, yasa kuma ba ƙarya yake yi miki ba.

Wannan yafi ƙarfin yayi mini ƙarya ki dai yi mini fatan Alkhairi.

To Najwan Inna Allah yasa alkhairi a tsakaninku, nima wlh zan so ki yi auren nan hankalin kowa ya kwanta in ga 'yan jikokina kin haifa mini kyawawa masu irin fuskarki.

Kai inna har kin sa naji kunya.

Najwa ta faÉ—a tana rufe ido cike da jin daÉ—in maganar innar, Inna girgiza kai tayi tama rasa a wani shafi zata aje Najwa, wauta ce da ita ko yarinya ko kuma rashin hankali ko kuma son zuciyarta ya rufe mata ido bata gane komai, addu'a tayi mata a zuciyarta tana cewa Allah yasa mutumin arziki ne yake nimanta.

*****"

Mujaheed.
Chapter 85 · 0% Book details