← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 98

Sashe 70

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sallar magrib ne aka zo da motar ɗaukar amarya, Hauwa da Laure da sauran dangi dasu aka zo ɗaukar amarya, dan a lokacin ne suka ga ya dace su bayyana kansu yadda su Sameeha zasu kurɓi gumar mamaki, sai dai abinda basu sani ba sun riga da sun san Aminu ne mijin Najwa, shiyasa suka yita baza ido su gansu amma ba ko ɗaya hatta ummansu ma basu ganta ba, hakan yasa suka yi zargin ƙila sun sani, sai bayan sallar isha'i aka basu amarya, koda ƙanwar baban Najwa Salima wacce take aure a Kano ta kama Najwa ta kaita ɗakin Inna akan ko zata ƙara yi mata faɗa, cewa tayi.

Allah ya kaita gidanta lafiya ya sadata da alkhairin gidan ya rabata da sharrinsa. Zaku iya tafiya.

Daga haka taja baki tayi shuru Najwa kam ko irin kukan nan ta rungumo inna bata yi ba, sai ta miƙe ta fice dan hankalinta yayi gidanta a kaita kawai saboda ta gaji da takurar innar, inna kuwa siriri hawaye ne ya sauko mata tana tunanin makomar auren 'yarta wanda har yanzu zuciyarta ta kasa kwanciya da shi, haka aka saka Najwa a mota suka wuce da ita gidanta tare da 'yan rakiyar 'yan uwa da ƙawayenta, sai dai dangin Inna da yawa babu wanda yaje dan sosai lamarin ya bata musu rai, wasu ma yamma nayi suka bar gidan, dangin Baba ne da su basu ga aibun auren ba sune suka yi shagalin biki cikin farin ciki da rakiyar amarya.

*****

Sameeha.

Suna isa gida Zaidu ya saka Anwar ya É—auko katuwar tamarba ya shimfiÉ—a musu a tsakar gida, nan suka zauna kowa yana mayar da numfashi mai cike da damuwa, umma ce ta katse shurunsu da cewa.

Zaidu da kai da Ikram banji daÉ—in abinda kuka aikata ba, koma meye ai aure suka yi ba haramci ba, sannan ma Aminu baya tare da Sameeha.

Amma umma ai wannan cin amana ne wlh koda ya rabu da ita, ya rasa wacce sai aura ba sai Najwa hakan bai dace ba, itama munafuka in ba ta saka son zuciyata ba ai tasan ana barin halak dan kunya.

Cewar Ikram tana share kwallarta, Umma ta dubeta tana cewa.

Ai ni kun gama zubar mini da mutunci tunda kuka yi abin kunya a gidan biki, ko ba komai Najwa 'yar uwarku ce bai dace in rai ya ɓaci hankali ya gushe ba, to ma da Aminu ya je ya ɗauko wacce bamu sani ba ai gwara ya aura wacce muka sani kodan tarbiyyar yaran nan su Abi.

Kefa umma gabaɗaya bansan meyasa kika kasa hango laifin Najwa ba, to bari kuji a ɗan nazarin dana yi na gano komai daya faru a tsakanin mutuwar auren Sameeha. Idan nace muku Najwa tana da saka hannu dumu dumu wajen yiwa Sameeha sharrin lesbian wlh babu musu ko kaffara, domin an saka bikin Najwa wata shida bayan mutuwar auren Sameeha, kuma wlh Najwa tana da masaniyar Aminu ne mijin da zata aura, zan iya ce muku Najwa bakinta ɗaya dasu Hauwa dan in har Hauwa bata yarda ya auri Najwa ba hakan bazai taba yuwuwa ba, bikinta saura wata hutdu aka saka nasu Ikram wanda akayi da wata biyu kafin aka zo aka yi na Najwa yau, kenan akwai wata a ƙasa, ko Aminu bai san Najwa ce matarsa ba ko kuma ya sani da biyu ya yarda dan ya ƙuntata miki Sameeha. Amma 'yan uwan Aminu da Najwa da saka hannunsu a cikin sharrin da aka yi miki aurenki ya mutu.

Wlh na yarda da kai yaya domin biri yayi kama da mutum, domin lokacin da aka yi walimar dawowar su Anty Sameeha naga yadda Najwa take shige musu suke magana banga wata alamar hantara ko rashin mutunci a tsakaninta dasu ba kamar yadda suke nuna mini. Ina kyautata zaton Najwa tana son Aninu tun lokacin data fara zuwa gidan ta ganshi, wataƙila son duniyarta yasa ta ke ganin zata iya aurensa, amma gaskiya zata yi halinta In Sha Allah.

Cewar Ikram, Sameeha kam zuwa yanzu hawaye take yi dan har lokacin bata fita da mamakin Aminu ba da Najwa, kuma ta hango ƙamshin gaskiya a manganun su Zaidu, umma ta nisa tace.

Ina fatan duk kan abinda yake a rufe Allah ya bayyana shi, mu daina maimaita maganar dan ƙara ɓatawa mutane rai zai yi, Ikram in da ƙarfi a jikinki tashi ki dafa mana ko taliya ce tunda bamu ma ci abincin gidan bikin ba muka baro, kuma rana tayi hantsi ya duba ludayi.

Umma bari na dafa ni zan iya.

Cewar Sameeha tana miƙewa, Zaidu ma ya miƙe ya wuce ɗakinsa cike da tunani, umma sam bata son ana maganar amma daya fita ya bincika gaskiya, sai dai yadda tace abar maganar shima ya barta, Ikram kam wayarta ta ɗauka ta shiga charting da mijinta tana faɗa masa abinda ya faru, Umma kuma ɗaki ta shiga ta kwanta doguwar kujera tana huta gajiyar data kwasa a gidan biki, sosai lamarin auren Aminu da Najwa ya dameta amma ta danne hakan ne dan kar yaran su shiga damuwa, saboda abin baiyi mata daɗi ba ko ba komai Najwa ta nuna ba tada mutunci da kara, yadda suka ɗauketa ita ba haka ta ɗauke su ba. Haka suka yini jugum jugum har yamma, a lokacin ne yayan babansu yazo gidan ya bawa Umma Haƙuri akan abinda ya faru, ta nuna ita ba damuwa Allah ya ƙaddara Najwa matar Aminu ne kuma In Sha Allah ba zata yarda zumunci ya lalace ba a kan haka zata yi magana da yaranta, sai yayi mata godiya ya kuma bawa Sameeha Haƙuri itama tace babu komai ya wuce, haka ya tsaya suka sha hira sai gabda magrib ya bar gidan.

Gidan Aminu.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

44.

Aminu barci barawo ne ya ɗauke shi anan doguwar kujera sai kiran sallar asubahi ne ya tashe shi, ya miƙe ya fara yin wanka kafin ya saka jallabiya ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari yayi haske wajen shida da rabi, ya shiga falonsa ya zauna ya ɗauki wayarsa ya kira Junaid yayan Najwa, har kiran ya kusa tsinkewa kafin ya ɗauka cikin muryar barci, suka gaisa kana Aminu ya ce.

Dan Allah ina so zan baka saƙo gurin su Inna, ka sanar dasu su shirya ƙarfe takawas zuwa da rabi suje gidansu Sameeha zamu haɗu a can akwai muhimmiyar maganar da za muyi.

Ok ba damuwa In Sha Allah zan sanar dasu.

Yauwa nagode.

Aminu ya faɗi haka kana ya aje wayar, Junaid cike da mamaki ya tashi ya zauna yana tunanin me zaisa Aminu yace su inna suje gidansu Sameeha, da alama wani babban al'amari ne duk yadda aka yi, lamarin ya ɗaure masa kai wanda yasa ya kasa komawa barci sai ya cigaba da danne danne a waya da nufin zuwa anjima kaɗan sai ya sanar dasu inna tunda akwai sauran lokaci, kuma shima zai bisu dan ayi komai akan idonsa. Aminu kuwa miƙewa yayi ya shiga bedroom ɗinsa ya sauya kaya zuwa shadda ɗinkin tazarce, ya saka hula ya feshe jiki da turare sai ya ɗauki waya ya kira driver ɗinsa akan ya kawo masa mota, driver yace yana hanya ya kusa ƙarasowa, sai ya kashe wayar ya dawo babban falo ya zauna yana ɗan duba abu a waya.

Najwa.
Chapter 70 · 0% Book details