Sashe 37
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Meye aibin gidan mahaifina? wlh a nan za a yi bazan taɓa gujewa gidanmu ba, tunda shima da kyanta ba ruwana da wani ƙarya.
Hauwa ta matso kamar zata buge mata baki ta matsa da sauri.
Wato aure zaki yi amma bakinki bai mutu ba ko Ummu Salma, zaki ci ubanki ne namiji sai ya koya miki hankali, Laure muje mu zauna mu sake shawara.
Salma dariya tayi mata dan halin Hauwa sai ita, suka wuce zuwa sashin Laure suka É—aura zancensu daga inda suka tsaya.
...
Haka aka ɗaura auren Salama aka kai ta Hayin Banki, gidanta mai kyau two bedroom filat da bayi da komai a ciki dan haya mijinta ya kama. Anyi biki yayi daɗi amma a gurin su Hauwa ba haka suka so ba, dan duk burin da suka ci bai auku ba, haka dai aka gama lafiya kowa ya watse daga 'yan cikin gari har 'yan ƙauyensu da suka zo kowa ya tafi.
*****
Sameeha.
Zazzaɓi sosai tayi dan har sai da aka kwantar da ita a asibitin dake nan kusa dasu tayi jinyar kwana biyu dan ko abinci bata iya ci, sai yawan kuka da rashin samun barci, ba komai yake damunta ba sai rabata da yaranta da suka yi, tayi tunanin Aminu zai dawo dasu amma koda tayi waya da Salma tayi mata Allah ya sanya alkhairi take faɗa mata ma ya tafi dasu Abuja, tun umma tana rarrashinta har sai da ta rufeta da faɗa tana cewa.
Maza ki kashe kanki abanza gashi can shi Aminu ya cigaba da rayuwarsa, da yaran sun dameshi da yanzu ya dawo miki dasu, idan ma zaki cire ranki dasu gwara ki cire ki samawa kanki lafiya.
Amma umma sai kace zaman ƙiyayya nake da Aminu da zai yanke mini irin wannan hukuncin.
Sameeha ta faÉ—a idonta na ciko da kwalla ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi akan doguwar kujerar É—akin umma, Ikram zata yi magana sai ga sallamar Inna da Najwa sun zo gidan, suka shigo suka zauna Umma tana yi musu lale, nan suka gaisa sai inna ta É—aura da cewa.
Na dawo in duba jikin Sameeha ne, wannan yarinya Allah yasa kin ci jarabawarki, ina mamakin sakin da Aminu yayi miki hakanan ba da wani laifin azo a gani ba.
Da yake su Umma sunki faÉ—ar komai game da sakin Sameeha saboda gudun surutu, umma ta É—aura da cewa.
Ai ta samu lafiya, amma ta dai kasa sakawa kanta haƙuri ne akan yaranta.
Dole ta ji ciwon rabuwa dasu Halima, uwa da 'ya'yanta ai sai Allah, yayi saurin rabata dasu wlh ,madadin ya barsu in ta samu miji sai a mayar masa dasu. Allah ya saka miki ya zaɓa miki miji nagari Sameeha sannu ko.
Cewar Inna da matuƙar tausayawa, Najwa tace cikin damuwa.
Anty Sameeha Allah ya baki lafiya ya baki wanda ya fishi dan Aminu bai kyauta ba, yadda naji ma su Hauwa sai murna suke yi har da cewa zasu aura masa wacce ta fiki.
Wani murmushi Sameeha tayi wanda ya kuɓuce mata dan rabon da tayi shi ma ta jima.
Wlh zanyi murna su samo wacce ta mini din, dan dama Aminu ai sai wacce ta fini ya dace ya aura, dan haka bana baƙin ciki wlh, Allah ya nuna mana rai da lafiya.
Ta ƙare tana wani murmushi, umma da Ikram sun fahimci inda maganarta ta dosa suma murmushin suka yi, wanda Najwa bata so haka ba taso ace sunji haushi musamman Sameeha ta ƙara shiga damuwa. Sai taga akasin haka, nan suka cigaba da hira har kusan sallar Magriba kafin suka bar gidan. A daren Ranar kuwa Sameeha ta samu barci dan sosai ta yi ƙoƙarin ya kice damuwa ganin shima Aminun da yayi sakin ya cigaba da lamarinsa ya mance da ita, karin abinda yasa ta saki yadda taji wai aure zasu yiwa Aminu, tasan ko ya amince to lalai saiya ƙunsa musu baƙin ciki tunda yasan bai da lafiya, tayi ma mamaki da bai sanar da 'yan uwansa rashin lafiyarsa ba, hakan yana nufin ya cigaba da ɓoye maganar kenan.
...
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tun ana kwanaki aka zo mako aka dawo wata, Sameeha tana ta warwarewa bisa maganganun da Umma suke yi mata na kwantar da hankali da kuma ƙarfin addu'a. Wajen La'asar suna zaune a tsakar gida bisa tabarma umma ta kalli Sameeha tana cewa.
Ohh yanzu fa har kinyi wata uku da kwanaki Sameeha, rayuwa kenan kamar komai ba zai wuce ba ga dai shi mutuwar aure ya tabba har kin fita idda. Allah ya kawo miji nagari sai na haÉ—a ki da Ikram idan saurayinta ya fito.
Aure kuma Umma? ai bana tunaninsa a nan kusa, ni wlh zan iya zana a haka ba aure kuma ba abinda zai dame ni. Makaranta ma nake sha'awar komawa.
Aiko baki isa ba dan ba a gidan nan zaki zauna mini ba, da rai na da lafiya bazan zuba miki ido ki kashe kuruciyarki ba a banza. Makaranta kuma sai dai islamiya ba dai boko ba dan ba zan amince ba.
Cewar Umma, Sameeha tana dariya zata yi magana sai ga Zaidu ya shigo da sallama yana cewa.
Maganar me ake yi ba za a jira na dawo ba ayi dani. Dan na han go farin ciki duk a fuskarku.
Maganar aurenka da Najwa muke yi shiyasa ka ganmu muna ta dariya.
Cewar Ikram cike da zolaya, Zaidu yasha kunu yana danƙara mata harara.
To bari kawai na koma dan bani da hurumi a cikin zancenku, saboda ko a ƙafa aka ɗaura mini Najwa wlh saina kwanceta.
Ya ƙare magana yana zama kusa da Sameeha a kan tabarma da yake babba ce, duk dariya suka saka masa Umma tana cewa.
Rabu da Ikram kasan halinta da tsokana, ni gwara ma daka shigo ina so dama muyi maganar sana'ar da Sameeha zata fara dan zamanta hakanan ba daɗi, kuma sana'ar zai riƙa ɗebe mata damuwa.
Wannan gaskiya ne, to ke Ƙanwata zinariyar gidanmu me zaki fara sayarwa.
Ai yaya ni ina mata sha'awar ta buɗe Saloon dan kun ga ta iya kitso sosai hakan zai sa ta warware saboda hulɗa da mutantr, in yaso sai ta samu wacce ta iya Saloon ta riƙa yiwa mutane tana biyanta, idan ma ta koya ta iya shikenan ko ni zan riƙa kama mata.
Cewar Ikram, sosai suka yaba da shawarar Ikram É—in Zaidu yace.
Me zai hana É—akina dake kusa da gate a rufe shi ta ciki sai a fasa ta waje amayar da shi shago, in yaso sai na koma wancen É—akin na kusa da kitchen a kwashe kayan ciki. Amma umma me kika ce.
Babana hakan yayi dan dama kama shagon shine babban damuwar, tunda É—akinka in aka fasa ta waje yana kallon hanya to ya dace ayi yadda kace, in yaso sai ta fara siyan kayan Saloon É—in a hankali.
Umma maganar Saloon fa yana buƙatar kuɗi sosai, ga gyaran shagon shima kashe kuɗi ne, kuma kinga muna lallaɓa kuɗin hannuna muna rufawa kanmu asiri. Sai dai ko na sayar da motata.
Allah ya kyauta, haba Sameeha sai kace bana raye, ba sai kin sayar da motarki ba ni na ɗauki nauyin gyara miki shagon in yaso kayan Saloon ɗin ki riƙa saya a hankali har ki tara, kuma inna samu kuɗi nima zan riƙa baki kina sayansu a hankali.
Cewar Zaidu, Ikram tace.
Aiko shawara tayi dan haka gobe in Allah ya kaimu Anty zan raka ki kasuwar gari mu fara tambayo kayan, ko kuɗi kaɗan ki riƙe mu fara tsintowa.
Hakan za a yi sai kuje kawai, kinga kya ga gari tunda ba fita kike yi ba.
Waya sani ko ta samo mana bazawari kiji an koma zancen aure.
Cewar Zaidu cike da zolaya, Sameeha tace cikin murmushi.
Haba yaya sai kace kun gaji da ganina a gidan.
Ba zancen mun gaji bane, da sauran ƙuruciyarki wlh ba zamu zuba ido mu riƙa kallonki ba. Ikram tashi ki saka mini abinci, wai me kuka dafa ne yau.
Tuwon shinkafa miyar shuwaka, Allah yasa zaka iya ci.
Cewar umma dan tasan baya son miyar a cewarsa É—aci yake yi masa.
Ya zanyi dole haka zan tusa tunda na koma agola É—an kishiya, Allah yasa kun wanke da kyau bata wannan É—acin.
Aure kawai zaka yi ka huta muma mu huta da ƙorafinka. Ana zancen Najwa kana cewa baka so.
Cewar umma, sai duk suka saka dariya suka cigaba da hira cike da raha babu wata damuwa a tare da su, dan Sameeha tuni ta dangana ta barwa Allah lamarinta.
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
25.