← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 8 OF 65

Sashe 8

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

It's rometic love story
Story & written
by mommyn fareesa
Last free page 9&10
.........*me tubarau* na shigowa parlourn ummi yasami in'am na zaune kan kujera ta cire hijab tana kallo a TV"Auwal na zaune yana chats"da sauri in'am ta kallesa sbd jin motsin shigowar sa dan bataji sallamar saba"wani irin kallon data sha jinin jikinta ya Aiko mata dashi idanuwansa sunyi jajir....murya na kirma tace"wlh yaya bayan na fito dg motarka na shigo ciki na samesa da masu gadi suna mgn shine yatsayar dani....wayace ki tsaya to?"shiru tayi"yana dg tsaye murya bbu alamar wasa yace" bama shiba duk wani dana koma ganin irin haka keda shi wlh Aranar sai kin sani....yana fad'in hakan yaja tsaki yasa kai yafita yabar musu daddad'an k'amshin turarensa"ummi dake sauraren komai tana a kitchen ta fito parlourn tana kallon in'am"wacce keta b'ata rai tana gunguni tace"to sarkin rashin ji me kikayi?"cikin shagwab'a ta sanarwa ummi yadda Akayi"Atake ummi ta fahimci dalilin yaya Aliyu na canzawa in'am islamiya"batace komaiba jikinta Asanyaye ta nufi kitchen"Auwal da in'am suka bar parlourn sbd suyi sallar magrib....yaya Aliyu kuwa cikin gida yakoma"yana k'ok'arin wuce window d'in umma yatafi part nasa"yaji muryar Abdul hakeem Abayansa yana cewa yaya kazo inji umma"juyowa yayi ya kalli yaron da zasuyi age mate da Auwal"saima Asannan yatuna mama gaje d'azun ta ganshi da in'am"bece komaiba yajuya yanufi parlourn umma"babu kowa Acikin parlourn sai ita tana zaune"fuskarta Ad'aure"ta Amsa sallamar sa"gefen kujera ya zauna yana fad'in umma sannu da gida"yauwa"d'azun ina kukaje kaida wannan yarinyar in'am??"kansa Ak'asa yace"Abba ne yace"na kaita islamiya sbd yacanza mata"tab'e baki tayi tana fad'in duk Abinda zan gaya maka game da maimuna da zuri'arta bakaji ko?"shiru yayi bece komaiba"taja tsaki tana fad'in ubanku nason ya aureta kai kuma tanaso ta manna maka y'arta duk Ataru a mallakeku ko?"to wlh ahir d'inka da shiga sabgarsu"dan Allah umma kiyi hak'uri ki dena d'aukar hud'ubar mama gaje"sannan ni ummi saita kama nake shiga part nasu"MARYAM kuma bbu ruwana da ita"shiru tayi can kuma tace"d'azun hjy ta shigo tana kumfar baki tunda kadawo bakaje ka gaishetaba"nafaje da safe tana bacci"saika sake komawa karka jamun tace"ko nice na hanaka sbd kasan mitar wannan tsohuwar"dato kawai ya Amsa ya mik'e tsaye yana fad'in zanje masallaci"Allah yatsare ta fad'a shi kuma ya fita.....bayan sallar isha'i In'am ta yita jiran da
wowar yaya Aliyu Amma shiru be dawoba"ummi har coffee ta dafa masa Amma be zoba"dama haka in'am keso ta dafa taliya da manja da yaji taci......
mama gaje ranta Ab'ace suka bar gidan umma"suna fitowa bakin titi zasu tari Adaidaita wata had'add'iyar mota tayi parking gefensu aka zuge glass d'in motar"Atake fuskar wata dattijuwar mace ta bayyanah"mama gaje ta zaro ido cikin mamaki tace"ikon Allah kamar hjy wasilah??"Aikuwa nice gaje"mama gaje ta zaro ido tana fad'in kece kika koma haka"yaushe rabona dake??"Aikuwa nice k'awata"zan wuce naga kamar kece"saina tuna kuma yayarki hjy hauwa anan Anguwar take"wannan zubaida ce ta girma haka?"aikuwa itace"zubaida ta gaisheta"ta amsa tana fad'in ina zakuje haka?"kedai bari gida zamuje tunda Allah yayimu talaka"y'ar uwata uwa d'aya uba d'aya ta gujeni sbd bani dashi"hmm! shegiya nera kenan"wacce ke sawa Adama dakai koda ba'a so"cewar hjy wasilah tana sakin wani shegen murmushi ta bud'e k'ofar me zaman banza tace"ku shigo na saukeku Agida"bbu musu mama gaje ta shigo ta zauna gefenta tana sauke ajiyar zuciya sbd sanyin AC da taji"zubaida ta shigo back sit ta zauna"Ahankali mama gaje ke kalle motar da suturan jikin hjy wasilah da kuma kallon fatar jikinta"Atake ta tabbatar hjy wasilah ta sami duniya"wanda ada tasan tuyan k'osai takeyi"mak'ocin hjy wasilar shine yabiya mata makka"ada taso tak'i zuwa ta Amshe kud'in shi kuma yace"indai zataje zai biya in bata zuwa shikenan(makka kiran Allah) haka taje ta dawo Amma ba wani Abu ta mallakaba"to kuma dg nan mama gaje bata koma jin labarin taba sai yau data ganta....wai ni kuwa hjy wasilah miye sirrin dan Allah?"ina kika koma da zama?"ga wannan zuk'ekiyar mota dan Allah"ni kuwa kullum muna a fatara da talauci"banida burin daya wuce naga na zama hamshak'iya kamar irin haka ko fin haka.... y'ar dariya hjy wasilah tayi tana fad'in tuni na sanki da wannan burun k'awata"in kuma kinaso tofa zai tabbata in zaki iya rufe sirrinmu ki kuma bi dokoki.....yo ni kuwa in dai zanyi kud'i me zai hana?wane irin dokoki ne ?"shiru hjy wasilah tayi tana yin parking tace"zubaida d'an fita muyi mgn"dato ta Amsa ta fita"mama gaje na washe hak'ora tace"yimun bayani y'ar uwa dan Allah"gaskiya banaso na sanar miki kizo kice baza kiyiba"Amma kije kiyi tunani nan da kwana 2 shin komai nace kiyi zaki iya sbd kiyi kud'i?"in har kinji zaki iya tozan kaiki Inda yadace"Amma bakinki k'anin k'afarki kiyi shiru karki sanarwa koda y'ay'an kine"ni wlh dakin gayamun tun yanzun basai na waniyi shawaraba"ah ah garadai kiyi"bara na miki kwatancen gidana Inda nakoma saiki sameni Acan"dg haka ta sanar mata Inda ta koma"ta zaro dubu goma ta bata kyauta"hannu na kirma mama gaje ta Amsa tana fad'in yau da alama zanci kaza da dare kenan?"ta fad'a tana godiya sukayi sallama.....tofa wata sabuwa inji y'an cah cah
zaune safwaan yake a get house nasa dayake kawo matan banza"su Aikata sab'on Allah suyi shaye shayensu"yaronsa mai suna bahbah dake zaune agefensa yana shan sigari ya kallah" yana nuna masa pic d'in in'am awaya yana fad'in itace wannan yarinyar bahbah....wlh raina yagama bani Abinda *Aliyu me tubarau* ke nunawa akanta SONE ba K'IYAYYA ba"na kuma tabbatar da cewa "muddin na lalata rayuwar yarinyar nan zan dasa mik'i na bak'in ciki da b'acin rai Azuciyarsa"bayan nayi kud'i zan fito gaba da gaba na nuna masa nine na aikata haka Akanta"ta haka zai game ni babban mak'iyin sane"kaga sai zuciyarsa tayi bindiga kenan?"kai ogah kana fire wlh"to shifa brr Ahmed?

Ayanzun ni bana yin ta Ahmed sbd beda ko rabin Abinda dr Aliyu *me tubarau* ya mallaka Aduniya"tun jiya danaga yarinyar nan wlh acikin yunifoam ,naji kuma muryarta sha'awar ta ke bujuromun.....wata dariyar shakkiyanci bahbah yasaki yana fad'in bbu damuwa zanyi yadda ka buk'ata zuwa jibin"yauwa ka gane kenan"zakaje islamiyar kafin Atashi ka tsaya data fito" ka nuna mata Ai Aliyu yaturoka ka maida ita gida"data shigo ka watsa mata powder hankalinta yagushe"Akamun ita nabiya bukatata mu y'ar da ita bakin titi da Asuba"batare dataga fuskataba sbd kaga ta sanni"karka damu ogah duk za'a yi haka"indai zakayi biya me kauri"karka damu bahbah"Amma ogah naga yarinya ce sosai batama gama cika babbar budurwaba?"hakane Ajiyane na mata pic Awaya ta be sani ba"ban damu dako yaya takeba"fatana burina yacika akan mak'iyi na"dg haka suka dinga dariya suna shan shisha.....
kimanin kwana 2 kenan da zuwan uztaz gidansu In'am"washe garin ranar da yazo yaya Aliyu bashine yakai in'am islamiya ba, yaya sulaiman yace" yakaita ya d'akko ta"bayan An taso ta ganshi Awaje shida brr Ahmed suna mgn ta gaidasu yak'i Amsawa"brr Ahmed ne kawai ya Amsa"sosai taji haushin Abun Aranta"da dare yazo suka gaisa da ummi yake sanar mata yayi busy ne shiyasa jiya da dare da yau be shigo ba yaci Abinci"nuna masa tayi bbu wata damuwa"Amma ranta yabata akwai dalili...

Washe gari da safe yakama wednesday ne"kuma Aranar yaya Aliyu zai koma office yafara aiki"tun wajen 7:35 am ya gama shiryawa cikin suit farare"yayi kyau har yagaji"jikinsa na fitar da ni'imtaccen k'amshi"saidai fuskarsa Ad'aure take tamau"ummi yakira ta waya yasanar mata Amasa kunun gyad'a zai Aiko a Amsa"bayan yagama wayar ya zauna a parlourn sa yana dannan laptop...k'ofar Aka turo"miskilin be d'ago kan saba saidai yaji y'ar siririyar muryarta tayi sallama"koma had'e rai yayi be kalletaba ya Amsa sallamar kamar an masa tilas"ta russunah gefen k'afafuwan sa tana fad'in yaya ina kwana?"d'ago kansa yayi yamata kallon second 10 ya d'auke kansa yana fad'in kece kika zo ko turoki Akayi?"turoni Akayi! sbd yaya ban san meyasa ba idan na gaisheka baka Amsawa?... yad'auki wasu few seconds kafin cikin sautin kamulalliyar muryarsa me dad'in Amo ya furta"bana son ita gaisuwar taki" kije ki gaida wannan k'azamin gajeran mutumin me yellow d'in hak'ora (uztaz) "Amamakinsa sai yaji sautin murmushin ta tana fad'in daka san yadda yake bani haushi da bace hakaba yaya"ni yanzun nagama shiryawa"kije sulaiman yakaiki ni Asibiti zanje"Akwai fa sauran lokaci dan Allah"ko jiya yaya sulaiman masifa yadinga mun Amota"kamar zai dakeni"ni wlh bana so yakaini yaya kai zaka kaini.....ta k'are maganar cikin shagwab'a"yaya Aliyu kuwa nata kallonta ta cikin bakin tubarau nasa"azatonta masifa zai mata sai kawai taga ya mik'e tsaye yana fad'in saiki tashi muje na mik'aki"batace komai ba ta tashi tsaye ,itace ta fara fitowa sannan shi yafito"Aransa yana addu'ar Allah yasa kar umma ta ganta"da wannan tunanin ya rufe k'ofar yabiyo bayan in'am"parking lot yasameta tsaye gefen motarsa"suna mgn da nafeesa itama da yunifoam Ajikinta"nafeesa na ganinsa tabar wajen"yatab'e baki yana fad'in magulmatan banza"bud'e k'ofar driver sit yayi yashiga"itama ta bud'e gefen me zaman banza ta shigo ta zauna....bayan sun hau samqn titi in'am ta kallesa tace"yaya An bamu Assignment kuma ni ban ganeba"idan mun dawo zaka mun??"bazan yiba"shikenan"ta fad'a bata koma cewa komai ba"sbd yabata haushi"yaci gaba da driving d'in wayarsa tayi ringing ya d'auka yasaka hands free"hellow doctor pls ankawo wata yarinya emergency pls ta k'onene...yaji muryar dr salma"saidai da wayar safwaan ta kirashi sbd tasan idan layin tane bazata samuba sbd yyi blocking nata"gani nan zuwa yanxun"Abinda yafad'a kenan atak'aice yakashe wayar"In'am ta tab'e baki tana jin mugun haushin wacce sukayi wayar da ita"bata gama wannan tunanin ba taga sunyi hanyar Asibitin sa"yaya yakuma da haka?"banza yamata yak'i mgn"8 d'in fa ta kusa kar nayi latti"ko kuma kabarni na shiga adaidaita.....
Chapter 8 · 0% Book details