← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 2 OF 65

Sashe 2

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

Ai na sanki Autar ummi baki barin saita kwana"yanzun ki tashi kije d'akin nafeesa kiyi sallar kizo kici Abinci"idan yadawo ki bashi hak'uri k'ilan ya k'yaleki"dukda nasan bazai dake kiba" zaidai miki hukuncin dayafi duka ciwo"sbd dama haka yake ma duk yaran nan in sun masa laifi"ni mommy na k'oshi ! dan Allah karki sanar masa banciba "ta fad'a tana tashi tsaye"bbu ruwana baza'ayi wannan k'aryar da niba"kije kiyi sallah An fara kira"kamar in'am tayi kuka haka taji"batace komaiba ta nufi d'akin nafeesa, ta sameta harma tayi Alwalah tana shimfid'a prayer mate zata kabbara salla"tab'e baki in'am tayi ta d'auke kanta"k'awata kenan ! ni banyi fushi dakeba kece zakiyi dani?"bansan meyasa kike nuna haka ga yaya Aliyu ba"bana jin dad'in hakan"karki manta kema fa yayankine?"niba yaya bane"garinma zan bari sbd matsawarsa"tafad'a cikin masifa tana nufar bath room ta shiga....nafeesa ta tab'e baki tana fad'in saiki sanya niya"dg haka ta kabbara sallarta..

Alh Ibrahim da Alh yakubu Abokan junane tun suna yara har girmansu"su haifaffun garin kanone kowa nasu na Acan"tun suna yara suke Abota"har Allah yasa sukayi Aure"da suka tashi gina gadaje sai sukayi Ajere ga gidan wannan ga gidan wannan"sukayi auren so da matansu hauwa(umma) da maimuna(ummi) "da farko zamansu lafiya suke cikin had'in kai matan"mazajensu na kasuwancinsu"shekarar su guda da Aure hauwa ta haifi d'anta Aliyu"Amma maimuna shiru bata haihuba"tunda Aka haifi Aliyu maimuna ta d'auki son duniya ta Aza masa" tana bashi kulawa kamar itace ta haifesa"sai hauwa na goyon d'ayyaba y'arta ta biyu sannan maimuna ta haifi d'anta sulaiman "shekarar sa biyu ta haifi yusuf"sannan mukhtar sai Auwal sai maryam Autah (in'am) "hauwa kuwa bayan d'ayyaba sai isma'il ,da ruk'ayya sai Auta Abdul hakeem"farkon Abinda yafara k'ok'arin had'a tsakanin hauwa wato umma da maimuna wato ummi"shine Alh ibrahim yanuna yana son k'awar maimuna da aure wato binta(mommy)"nanfa Akayita tashin hankali hardai Akayi Auren"hauwa da binta suna zaune kowa na harkan gabansa bbu ruwan kowa da kowa"hauwa ta k'ullaci ummi sbd a ganinta itace silar da Akayi mata kishiya"sunjima Awannan gidan "dg nan sukabar wannan Anguwar da suke sbd kowane yasami budi sosai"nassarawa G R A suka koma gidan Alh Ibrahim na kallon gidan Alh yakubu"wanda Alokacin itama binta ta haifi yara 3"saifullahi, zainab mahmood da cikin nafeesa suka koma"lokacin itama ummi nada cikin in'am"gaba d'aya umma da ummi basa shiri"danma ummi bata biye mata"sai Abin yazama mommy da ummi ke shiri"su kuma Abba da Alh hidimar gabansu sukeyi"gaba d'aya yaran gidan sun taso cikin had'in kai da girmama juna"zaka d'auka tamkar dangin junane na jini"kuma wannan zumuncin nasu yasaka Alh ibrahim (Abba) zai iya iko da d'an Alh yakubu(baba)shima zai iya iko danasa y'ay'an"gefe guda kuma Abba na tsawatarwa umma ta rage k'iyayya ga ummi Amma bata denawa"tunda yaran ummi dana umma suka tasa suka fahimci tsakanin iyayen nasu mata bbu shiri"Amma haka be damesuba zumuncin su sukeyi yasu yasu"tunda in'am ta tasa ta fahimci umma bata son y'ay'an umminta da ita ummin tata"sai tayi baya da zuwa part nata"idan sun had'u ta gaidata da k'yar take Amsawa"Ayanzun haka Anyiwa zainab da d'ayyaba Aure da ruk'ayya suna gidan mazajensu"yayinda Alh yakubu yarasu shekara 3 da suka wuce"wanda hidimar komai ta family d'in sa ta dawo wajen Alh Ibrahim"dukda yanada dangi da y'an uwa" wanda Alh Ibrahim yaso ya Auri ummi itace tak'i yarda"kuma mommy taso hakan sosai Aranta"Amma ummi sbd gudun Abinda zaije ya dawo sbd hjy hauwa ta hak'ura Amma badan bata soba.....hjy hauwa tanada k'anwa mai suna gaje uwarsu d'aya ubansu d'aya"yaranta biyu , Hamza da zubaida"Hamza zaiyi 24 yrs"zubaida zatayi 20yrs"mama gaje talakace lik'is Agidan haya suke zaune"da taimakon Aliyu da umma suka dawo gidan kansu"yakuma d'auki nauyin karatun hamzan"sosai hakan yayiwa mama gaje dad'i sbd macece ita mai son Abin duniya da had'ama da handama"ita kad'aice wajen mijinta mlm lawal dake sana'ar siyar da faskare"duk Abinda zai kamata bata godewa sai tayi hange"kuma mama gaje itace ummal aba'isin haddasa k'iyayyar ummi Azuciyar umma"tana tunzurata data ware kanta karta Amince da mommy kishiyarta da kuma ummi"yayinda Akwai wani buri da mama gaje taci Azuciyarta"wannan kenan.....yayinda hjy fatima maihaifiyar Alh ibrahim tana gidan zaune part d'inta daban" "kasancewar shikenan d'anta guda Aduniya...

In'am (maryam) wacce taci sunan kakarta"wato mahaifiyar Alh yakubu"tun tasowarta ta taso da k'iriniya da rashin ji"gata shagwab'abb'iya sbd Autace"saidai Allah yamata brain me d'aukar abu"tanada k'ok'ari boko da islamiya"tun last year sukayi saukar Alk'ur'ani me girma"yanzun SS 2 suke, sunyi exams suna hutu"dasun koma SS3 zasu shiga itada nafeesa"in'am batada k'awa konace Aminiyar data wuce nafeesa"dan sun shak'u da juna sosai"sai kuma wata sa'adiya da class nasu guda da ita"in'am bata shiri da yaya Aliyu"sbd kaf shine babba Acikin wannan zuri'a"yanada ikon hukunta kowa acikin y'ay'a kuma dole Amasa biyayya"kuma baya wasa da yaro"gashi gaba d'aya yafi yima in'am mugunta da takurata "tana jin haushinsa sbd hakan"tana kuma k'ok'arin nisantar Inda yake kodan sbd ummansa"shekara 2 da yayi baya nan ba k'aramin dad'i in'am tajiba"in'am farace ba jaba"kuma ba doguwa bace ba kuma gajera ba"batada jiki sbd batason cin Abinci sai kayan kwad'ayi"Allah yamata shan yajin tsiya"yaya Aliyu ne kawai ke tursasata taci Abinci"Adole zataci" tana kuka tana jin haushinsa"Ayanzun data fara girma kyawunta da baiwar surunta ke fara fitowa"dukda tana Ahaka da yawa maza na nuna suna sonta bata damuwa dasu"uztaz nasu yayi mugun mutuwa a soyayyar in'am shiyasa kullum islamiya yake mata tambaya sbd yaji siririyar muryarta yana kuma tsoron furta mata yana sonta"yayinda ita kuma haushi yake bata sbd sajensa irin na yaya Aliyu ne...Acewarta"
Aliyu ibrahim mai tubarau matashin.....
mu had'u a next page idan anyi zazzafan sharhi"tsaftataccen labarine me tsayawa azuciyar me karatu da sakq nishad'i
hanzarta biyan naki ta wannan hanyar dan adama dake atafiyar bbu cizon yatsa sbd free page 5 ne kawai
wannan book d'in nakudine
Normal grp 300
Vip grp 1000
Special people 2k wato 3pages in a day
zaku biya kud'in ku ta wannan acc number
2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne
banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira
Y'an nijar kutuntub'i wannan n
+227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f
dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba
SONE KO K'IYAYYA??

It's rometic love story
Story & written
by mommyn fareesa
Dedicate to zee h wada
kiji dad'in ki ta wajena
Free page 3&4
........Aliyu Ibrahim mai tubarau matashin saurayine me jini ajika"wanda duniya ke damawa dashi sbd baiwar ilimin likitanci da Allah yabashi"d'an kimanin shekara 35 ne aduniya"tun yanada 32 yrs ya kammala karatunsa anan gida nigeria yafara aiki awata private hospital"dg baya kuma mahaifinsa da marigayi suka fara gina masa tasa asibitin"ba'a fi wata biyu da gama ginataba da bud'eta Allah yayima baba rasuwa"bayan rasuwar tasa da wasu watanni Aliyu yatafi london k'arin karatu"yanzun yazama babban likitan mata"kuma Alhmdllh takardunsa sunyi kyau sisai"Aliyu dogone wankan tarwada"kyakykyawa n gaske ne ajin farko"akwai cikar haiba da kamala atare dashi"beson surutu da hayaniya"sannan be cika yawan mgn ba sai akan Abinda yashafi aikinsa" miskiline na bugawa ajarida"da yawa na fad'in basu tab'a ganin murmushin saba"baya kula mata ko kad'an duk kuwa irin nacin mace dason ta shige masa"sannan baya Amsar haihuwa Atsarinsa"sbd baya son kallon private part d'in wata"Aliyu yanada hak'uri sosai da kauda kansa ga abubuwa"amma be iya fushi ba"bashida Aminnan da suka wuce Ahmed da safwan aduniya"safwan likitan kunne ne a Asibitin Dr Aliyu yake aiki"yayinda Ahmed lauyer ne me zaman kansa"safwan beda aure"Amma Ahmed yanada mata tasleem da yarinya guda hafsat"sunan me tubarau yasamo asaline tun sadda Aliyu ke yaro be wuce 12 yrs yake saka tubarau"kuma bawai wata matsala ce garesaba"ah ah kawai yana ra'ayine"har zuwa girmansa kuma be denaba"hakan yasa friends nasa ke kiransa da me tubarau"ak'allah baya rasa glasses 24 nasa ad'akin sa"Aliyu har yanzun be tab'a soyayya da wata y'a mace ba"tun bayan yagama karatunsa na likita Abba yamasa zancen aure yanuna ba yanzun"dg lokacin Abba yasa mishi ido kawai"yakuma sha alwashin sulaiman,yusuf, isma'il da saifullahi "duk idan sun sami matan aure zai musu aure tunda sun gama karatunsu suna aiki ma"Dr Aliyu yanada tsafta ta tashin hankali da kuma k'yank'yami"be kuma son k'arya da mak'aryaci"yana son mahaifiyarsa sosai da faranta mata"baya damuwa da yadda take k'in ummi"sbd be manta ba bbu irin wahalar da ummi batayi dashiba yana k'arami har yafara tasawa"yashak'u da ita sosai"kuma ko yanzun komai yakeso adafa masa dayayi mata mgn zata dafa sadda yana nigeria"Aliyu yanada aji k'arshe dan idan yashiga cikin mata kamar su sacesa lolx.....yanada sallaya baka k'irin atsakkiyar goshinsa datake k'ara masa kyau"jikinsa amurde yake sbd kiran jikinsa irinta zakice"hjy kaka da Ali zaki take kiransa" Aliyu baya wasa dakowa agidan"garama yaran k'annansa in sunzo gidan zai d'auk'esu yamusu Alkhairi yayi gaba"ayanzun nafeesa da in'am sune kawai mata suka rage"komai zai musu baya banban tasu"hakama idan yama umma abu suma mommy da ummi yana musu ab'oye"sosai Aliyu yatsani mama gaje sbd yasan tana yima umma hudubar tsiya"sau tari nafeesa zataje ta tambayesa abu ko kud'i zatayi wani hidima dasu"Amma in'am bata iyawa"saidai ta tambayi yaya sulaiman ko yaya yusuf"in suna jin y'an arzik'i su bata"in kuma tayi laifi ko tsokanar fad'a suk'i bata"dama agidan yaya sulaiman ne ke yawan jibgarta"idan Allah yasa Abba na nan taje gunsa ta b'uya ya hana adaketa"hakama kuma tana kaima Abba k'arar Auwal sbd beyin cikakken sati 1 be sakata kukaba ko basuyi fad'a ba"Aliyu shine yasiyi mota agidan ya d'auki driver"duk Inda kowa zaije akaisa"Amma mama idan ta fahimci za'a kai mommy ko ummi Anguwa itama zata tsiro da fitarta"hakan yasa Abba yasiyi mota yakaita gidan ummi sbd idan zata fita ko za'a kaisu in'am skul"sbd yaya sulaiman da yaya yusuf kowane ba'anan gidan yake ajiye motarsaba....abayan part d'in umma d'akin Aliyu yake"yayinda su sulaiman can gidansu in'am sukeda d'akuna"
In'am agaban yaya Aliyu bata iya cewa me tubarau amma abayan idonsa fad'i takeyi"kuma awancan lokacin ranar dazai tafi london yazo parlourn ummi yaji muryar in'am na ihun murna tana fad'in me tubarau zai tafi su huta"shi alokacin dariyama ta bashi"be kuma nuna yaji ta fad'i sunan ba.....wannan kenan nan gaba zakuji wasu abubuwan.....
Chapter 2 · 0% Book details