← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 37 OF 65

Sashe 37

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 8 min read

Aliyu Adinga hak'uri da kai zuciya nesa dan Allah"wannan ai yaro ne k'arami bama sa'anka bane ga yadda naga idonuwansa"hakane Abba ina wuni??"lafiya qlau Alhamdllh"ina Alh (Abba) kwana2 mun rabu da gaisawa"yana nan lafiya qlau yana kasuwa "to masha Allah"dg haka Alh d'ahiru ya tura k'ofar get d'in gidansu In'am yashige ciki"yana k'ok'arin shiga cikin parlourn gidan in'am ta fito"gaidashi tayi ta wuce"shima dama kwana 2 yarabu da zuwa yaga family d'in d'an uwan nasa"suma kwana kuma 2 basu lek'a suba"shine yau yalek'o su Ayi zumunci....

In'am cikin nutsuwa ta fito k'ofar gidan"ta sami yaya Aliyu tsaye jikin bangon gidan yana waya da brr Ahmed"tsayawa tayi gefensa tayi k'asa da kanta tana tunanin itada farooq har Abada"tasan insha Allah tunda yaya Aliyu na nan be isa yacutar da itaba.....my Angel shine kika tafi kika barni ko?"taji Amon tattausan muryanshi Abayanta"Ayya yaya Aliyu wajenka fa zanje dana fito yanzun sai kuma na ganka"ta fad'a cikin shagwab'a batare data kallesaba"lumshe ido yayi sbd jin tsikar jikinsa na tashi sakamakon jin muryarta"murya can k'asa yamatso dab da ita yana cewa"wannan yaron shine farooq?"Eh shine"meyasa kika maresa my Angel?"ina ganin fad'anki yayi sauk'i Ashe baki dena ba?duk yafad'a yanata kallonta"kanta Ak'asa tace"laifinsane yaya Aliyu"kuma ni yanzun bbu ruwana dashi nama goge number d'insa bayan nayi blocking"duk wanda zai fad'i magana marar dad'i Akanka koya nuna jin zafinsa Agareka! banida mak'iyin daya wucesa Aduniya yaya Aliyu"bansan meyasa da yawan wasu mutane sukeyima zumuncinmu kallon ba zumuci bane kare kare ne??.....ajiyar zuciya yasaki domin kalamanta ba k'aramin dad'i da kwantar masa da hankali sukayiba"cikin taushin murya yace"dama haka nake da irin wannan matsayin Awajen Aminiya ta?"tana d'an murmushi kanta ak'asa tace"kaa wuce haka yaya Aliyu" hakane my Angel"idan munga hakan saimu share komu d'auki matakin dayake daidai"iya Abinda nasani ban damu da rayuwar kowaba balle har na zauna nayi tunanin ya wane ke rayuwa"dama yana zuwa wajenki?"ah ah be tab'a zuwaba sai yau"kawai dai skul yake zuwa idan zai d'auki k'anwarsa"shiru yayi yana nazari"sbd bejin zai iya barin yaron hakanan tunda har yayi sanadin zubar hawayen ta"karki koma kuka sbd wani banza dg yau kina jina?"yabani haushine yaya shiyasa"bana son ganin kukanki my Angel"yanzun yaushe zaku gama paper d'in?"saura 5days fa yaya"ranar Wednesday in sha Allah zamuyi final"d'an murmushi yayi yace" Allah yakaimu lafiya"saidai baza kuyi wasu bidi'oi ba"batace komaiba tayi shiru"muje my Angel Asibiti nakeso na koma dg can zan tafi masallaci"yak'are maganar yana k'ok'arin kama hannunta"tayi saurin b'oye hannun nata tana murmushi"yatab'e baki yayi gaba ta biyosa Abaya"parlourn mommyn yanufa"yasami ta shirya masa komai kan carpet"nafeesa na zaune a parlourn tana chats"kallonta yayi yace"ina mommy?"bacci ta kwanta"okay yafad'a ya zauna"In'am ta shigo da sallama"suka had'a ido da nafeesa"ta gallah mata harara"ita kuma tayi murmushi ta tashi tsaye tabar parlourn"satar kallon sa tayi yana danna waya"wai yaya Aliyu koda yaushe kana latsa waya dan Allah?"beyi mgn ba yadai d'ago kansa ya kalleta yaga tayi k'asa da kanta"d'an murmushi yasaki yana tunanin tunbe furtaba yafahimci tana jin kunyarsa inaga yafurta to??.....yaya mezan zuba maka kaci? ta katse masa tunani"Aransa yace"my Angel tayi hankali kenan?"be gama wannan tunanin ba ya ganta tsugunne tana duba komai cikin nutsuwa ta fara seving nashi"shidai yana binta da kallon k'asan ido"tamkar hankalinsa ba'a wajenta yakeba"bayan ta zuba masa komai ta tura masa gabansa"ita kuma ta zuba kunun gyad'a cup guda da chips rabin plate"batare data zuba farfesun kayan cikin sanuwa ba.....yaya pls bissimilah! kallon komai yayi ya kalli na gabanta"d'aure fuska yayi yana kallon ta"tayi k'asa da kanta Ahankali tace"dan Allah wannan ya isheni yanzun"kasan banacin Abinci da yawa "kuma yajin danaga baka so shima bana ci sai idan yazama dolene nakeci kuma kad'an nake ci.... shikenan my Angel"Amma kinsan inaso ki zama y'ar lukuta kina gudu da k'yar"dana biyoki sainayi saurin kamaki ko?"Amma ke baki son cin Abinci"kai yaya sbd kamun mugunta shiyasa kakeso nayi jiki?"ta fad'a tana fara kurban kunun Akunyace"shima yana murmushi yayi Bismillah yafara cin Abincin"Ahaka seif yaturo k'ofar yasamesu"gaida yaya Aliyu yayi"in'am ta gaidashi yashiga kitchen"Aransa yace"dama nasan sonta yakeyi shiyasa ya hanani kulata"da wannan tunanin ya d'akko ruwa da lemo a fridge yafita"In'am kuwa cin yanga takeyi"harma yaya Aliyu yagama sannan ta idar"da kanta ta kwashe kayan ta mayar kitchen"ta dawo parlourn tayi tsaye"zoki zauna mana"yaya gida zan tafi kar ummi ta nemeni"shiru yayi bece komaiba"yaya !

Yes"yafad'a yana k'ok'arin sqka k'wayar idonsa Acikin nata"ita kuma tak'i yarda"tanata kallon k'asa"shikenan kije kibar Amininki da kewarki"idan natafi masjeed wace Addu'a zan yimana??"duk wacce ta dace damu mana"shikenan kingama mgn"yafad'a yana danna waya taji k'arar shigowar message Awayarta"tana dubawa taga shine yaturo mata credit na 5k"yaya kai.....pls my Angel banason godiya ko korafi"duk Abinda zan miki ina miki ne dan Allah"so bana son doguwar mgn"kije gidan Anjima zan kiraki lambun gidan nan"to yaya Amma yaushe zamuyi wasan dakace?"d'an murmushi yasaki yace"sai Anjima k'ilan"batayi mgn ba tafita dg cikin parlourn tana jinta cikin nishad'i"sadda ta shigo gida ta sami ummi d'akinta tana duba kayan tsarabar d'azun daya bata"dogayen rigunane kala 2 irin na k'asar"sai kayan shafa da turaruka masu masifar tsada"girgiza kanta ummi tayi tace"In'am hidimar Aliyu gareki yafara bani tsoro"meyasa bakya k'in Amsa wai??"wlh ummi dana nuna hakan yanzun ya d'aure fuska yace"ban d'aukesa yayana ba"kuma shi dan Allah yayimun"jeki mayar da kayan d'aki kije ki kama ma laure girki"nima nadan huta"dato in'am ta Amsa ta d'auki ledar ta fita"ummi tasaki Ajiyar zuciya"Aranta tana musu fatan Abinda yafi zama Alkhairi ga rayuwarsu.....
***********
mama gaje ce zaune a parlourn hjy wasilah"Abinciccika na more rayuwa gasunan gabansu A Ajiye samqn center table"sun gama ci sun rage saura"hjy wasilah na kallon mama gaje tace"yanzun saura wata 2 ki shekara da shiga k'ungiya"kuma Alokacin zaki koma bada jinin wani shak'ik'inki.....ban ganeba?"bayan lawal dana bada saina kuma koma bada wani?"ta fad'a fuska bbu walwala"gabanta na bugawa"k'warai kuwa dole ki bada"meyasa kikeyin Abu kamar yau kika shiga k'ungiya?"kin manta na sanar miki saika bada shak'ik'anka kashi biyu sannan kafara bada bare duk shekara"to Amma kinsan dai bazan iya bayar da zubaida ko hamza ba wlh"to ke kika sani saidai idan ke za'a zuk'e jininki"da kike wata mgn can"baga hjy hauwa nan ba yayarki" miye Amfanin ta Awajenki yanzun? kawai ki gama da ita shine bayani" kamar yadda kika kai lawal suka masa saddabaru yadawo gida washe gari yamutu"to itama haka zaki mik'ata"ko kuwa Adole tsakanin zubaida da Hamza ki bada mutum guda....shiru mama gaje tayi tana tunani"can talabartawa hjy wasilah irin koran da Abba yamata....to Ai takwana gidan sauk'i"idan kin tashi kaita waya zaki mata tazo gidanki dg can ki wuce mana da ita"king
a bbu wanda zai zargeki"koda kuwa Asibiti suka kaita"to Amma mezance mata harta Amince tazo gidana muje can??"ki bari lokacin yayi mana"kima godema Allah da hakan yafaru"sbd idan hakan be faruba za'a san tare kuka fita washe gari tarasu"eh kuma hakane"Amma wasilah idan naga bayanta banida wani shak'iki me mahinmanci Agareni kamar ita"dg ita saini wajen iyayenmu har sukabar duniya"sauran dangi dana uwa dana uba garemu...karki manta gaje duk darajar iyaye batakai ta kowaba Amma naga bayan iyayena ni"sbd haka kima dena wannan tunanin zai sakq miki tausayi Aranki"shikenan Ai"dg haka suka cigaba da wata firan suna jin duniyar tazamo musu sabuwa.....
washe gari yakama satday....
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
SONE KO K'IYAYYA
45&46
.......washe gari yakama satday bbu office"yaya Aliyu tun bayan sallar Asuba ya kwanta yanata baccin gajiya sbd jiya sai 10 pm yabaro Asibiti"sai wajen 9 am ya farka dg baccin"idanuwansa basu sauka ko inaba sai kan pic d'in In'am"yasaki d'an guntun murmushi yana fad'in my Angel rigima nasan dai yanzun kin tashi dg bacci"yafad'a yana tashi zaune"dg shi sai boxer"masha Allah!

Dr Aliyu Akwai k'iran in garman namiji Ajikinsa"gaba d'aya jikinsa Amurd'e yake duk gashine "wayarsa yajawo yana hamma"sbd bayajin zai iya shiga wankan batare da yaji muryar gimbiyar tasaba"number d'in ta yalalubo fuskarsa cike da Annuri yayi dealing...."In'am na d'aga wayar tayi masa sallama cikin siririyar muryarta"lumshe ido yayi yana rungume pillow Ak'irjinsa sannan ya Amsa yana fad'in my Angel kin tashi lafiya?"lafiya qlau yaya nah"saidai ni harna shirya nayi break fast banda kai"da gaske kikeyi?"Eh mana zaune nake d'akina yanxun haka"to shi yaya Aliyu meyasa baki tashe saba koda ta waya?"yafad'a murya can k'asa"kai yaya Aliyu nasan ko bacci kakeyi kana hutawa saina katse maka?ko kana Asibiti ne tunda Aikinku bbu hutu"?ah ah yanzun na tashi dg bacci"wanka zanje nayi nazo na gaisa da Aminiyata na Amshi Abinda ta Ajiyemun ko?"to yaya idan kazo zamuje gidan yaya Ahmed sai naga baby??"my Angel wai yaushe kika fara son yara har haka?nidai yaya zaka kaini?"tafad'a cikin kukan shagwab'a"saurin kashe wayar yayi ya rufe ido"yatura lip nasa na k'asa cikin bakinsa yanata tsotsa"yana shafa sumar samqn kansa"yafi mintina 10 Ahaka kafin yabud'e lumsassun idanuwansa yana fad'in my Angel kinaso kitayar mun da hankali da wannan shagwab'ar taki"bayan ina samu ina lallab'awa da rayuwata kafin kizo mu ding.....ringing d'in wayarsa ta katse masa mgn"d'an tab'e baki yayi yana kallon fuskar wayar"yaga bak'uwar number ce"tsaki yaja ya mik'e tsaye sbd yasan be wuce cikin yaran dake cewa suna sonsa ne"shi Abunma har tsoro yake basa"na halin wasu y'an matan yanxun da babu kamun kai balle tarbiyya"yana wannan tunanin yasaka kayan wanka jikinsa Amace yashiga bath room"yafi mintina 20 Aciki"yagama wankan Amma yayi kwance cikin ruwan d'umi daya cika a bathtub"idanuwansa Arufe yanata tunani"kafin dg bisani yafito dg cikin ruwan ya d'aura towel iya k'ugunsa yafito....
Chapter 37 · 0% Book details