← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 19 OF 65

Sashe 19

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 5 min read

Ahankali yatura k'ofar parlourn yashigo cikin nutsuwa"hannunsa guda yana rik'e da wayarsa kirar iphone 13"gudan hannunsa yana cikin Aljihun wondonsa"gaba d'aya parlourn hayaniya Akeyi sbd cike yake da friends d'in sady"be kalli ko waceba ya nufi Inda sady take tsaye tana k'ok'arin had'a mp"yaya farooq ga friends d'ina sunzo tayani murnan bath day d'ina"kuma gashi tanimu be zoba balle yafara yi mana pics d'in"ta fad'a tana kallonsa"wasu dg cikin y'an matan suka gaishesa"Amma banda in'am da hankalinta na wajensu farida suna fira"Amsawa yayi yana d'an kallonsu sbd ko zaiga beauty d'in nan"Aikuwa cikin sa'a suka had'a ido da in'am"yadinga kallonta bbu ko k'iftawa"ta d'auke kanta da sauri"ya kalli sady yana fad'in zanje na kirashi ta waya sai yazo ya muku"ina mommy?"tana cikin d'akinta"okay zo muje na baki sak'o"dato ta Amsa ta biyosa"tasha gayunta cikin gownt An mata make up kamar Amarya"ga k'aton cake nata da drinks Asaman wani table babba"suna fitowa dg cikin parlourn farooq yace"yasunan y'an matan nan guda 2 masu kaya iri d'aya??"d'an murmushi tayi tace"inaga MARYAM YAKUBU da NAFEESA IBRAHIM kake nufi"miye sunan farar?"maryam Anace mata In'am"gaskiya sady tamun babyn ina sonta wlh tunda na ganta"yafad'a yana lumshe ido"sady ta dinga murmushi tana fad'in oh yaya yau wace rana da kanka kace kana son budurwa??"gaskiya naji dad'i zan maka campaign"Amma saika cikamun jakata"karki damu muddin ta Amince nine kawai nasan meye zan baki"ita kuma gudar Abdul na ciki"yafad'a yana murmushi"sady tace"shikenan ta wuce ciki"batayiwa su in'am zancenba"suka cigaba da shewarsu da rawa dayin y'an ciye ciye"sosai In'am ta zage tanata rawa sbd wak'okin na music ne dana kuma Ado gwanja"sai wajen k'arfe 6 pm Aka fara yimusu pics suda k'awayensu"kasancewar dama hutu Akeyi Anjima ba'a had'uba"gaba d'aya nafeesa da In'am sun shagala sun manta da zancen komawa gida"har Akayi magrib basu luraba"sai bayan Angama pics d'in wasu na cewa zasu tafi sannan in'am ta janye labule ta lek'a window taga dare yayi"gabanta yafad'i ta duba wrist watch d'inta k'arfe 7:45 pm"mun shiga ukku nafeesa! isha'i tayi...

Akid'ime nafeesa ta mik'e tsaye tana fad'in tashi muje gida Allah yasa yaya Aliyu be dawo ba"In'am kasa mgn tayi ta mik'e tsaye tana gyara mayafinta" sady na kallonta tace"k'awata badai tafiya ba?"In'am tace"tafiya mana zamuyi har isha'i tayi bamu fargaba"kar muyi laifi Agida"to shikenan muje yaya farooq yamik'a munku gida ko?"shiru In'am tayi batace komaiba har suka fito haraban gidan"farooq da Abdul na zaune samqn wata jar mota"suna ganinsu suka diro"kasancewar ko ina da haske A gidan"sady na murmushi tace"yaya dan Allah ku mik'asu GRA nasssarawa"ta fad'a tana cika musu hannu ta musu godiya"In'am kuwa kamar tayi musun shiga motar"saita tuna yanzun idan sun fita kafin su sami nafef k'ilan 8 pm ta wuce"kushiga mana"cewar farooq yana bud'e musu back sit yana murmushi"sai kallon In'am yakeyi"bbu musu suka shiga"Abdul yaza gaya yashiga gefen me zaman banza"farooq yaja motar cikin nutsuwa kafin yace" hjy in'am kunyi shiru keda nafeesa ko?"nima Abinda zance kenan Abokina"cewar Abdul"gaban In'am yafad'i tana mamakin ta yaya yasan sunanta?....kuna mamakin jin sunanku Abakina ko? hakane gaskiya munyi mamaki"cewar nafeesa"Abdul yayi y'ar dariya yace"to kucire mamakin"idan bbu damuwa muna son ku bamu contact naku"gaskiya bamuda waya kwanan nan dai zamuyita"In'am ke baza kiyi mgn ba?"cewar farooq"d'aure fuska tayi batace komaiba"duk yadda farooq yaso In'am tayi mgn k'in magana tayi har suka iso Anguwar GRA nassawa.....
yaya Aliyu na shigowa office yaja computer daya saita da CTV camera"yafara dube dube har yagano room d'in daya kai In'am jiya"Anan yaga yadda sukayi fad'an nasu itada nafeesa ajiya da dare" murmushi kawai yayi yana jin nafeesa na k'ara samun matsayi na y'an uwantaka Azuciyarsa"ya fahimci tana jin zafin Abinda In'am ke nunawa Akansa"yakuma lura In'am har yanzun k'uruciya na damunta"saidai ransa yabashi nan gaba harda nafeesa Acikin masu yimasa campaign d'in soyayyar sa awajen in'am....yajima yana tunani har yafara duba patient"sai wajen 12 yatsaya yayi break fast sannan yaci gaba"be baro Asibitin ba sai wajen 4:30 pm"sadda ya iso gida biyar saura"part nasa ya wuce yayi wanka yashirya cikin k'ananun kaya yanufo part d'in ummi sbd yayi lunch Acan" kuma yaga y'ar rigimar tasa"yasan dai yanzun ta dawo dg wajen lallen"yana wannan tunanin yashigo cikin parlourn ummi"mukhtar da Abokinsa Abdallah suna zaune suna kallo"cikin ladabi suka gaidashi ya zauna kan kujera yana danna waya yana satar kallon d'akin In'am"ina *maryam*?

Abinda yafad'a kenan Atak'aice"basu nan itada nafeesa"naji ummi tace"mommy ta Aikesu"shiru yaya Aliyu yayi bece komai ba...ummi ta fito dg cikin kitchen tana cewa"Aliyu kadawo ne?"Eh ummi miye kika girka?"Abinda kakeso ne"yana dining Area ko Aka maka Anan??

Ah ah ummi bara naje can"dato ta Amsa ta koma kitchen"yaya Aliyu yatashi tsaye yanufi dining area yaja kujera ya zauna"haka nan yaji zuciyarsa tak'i Aminta da fitar yaran....bayan yagama cin Abincin yafito yana duba time shidda saura"kan resting chairs dake bakin k'ofar parlourn ummi Anan ya zauna har shidda ta ida Amma su in'am basu dawo ba"tashi yayi yafita dg gidan yashiga gidansu"kai tsaye part d'in mommy yanufa"yasameta zaune tana azkhar sai yaran zqinab da sukazo musu juma'a suna zaune sunata wasa"(Affan da Amrah)suna ganinsa suka nufesa suna fad'in Uncle! hannunsu yakama ya zaunar dasu Ajikinsa suna masa surutu" mommy dai na murmushi tace"kadawo ne Aliyu?"Eh ina nafeesa?bata nan, tana gidansu k'awar su mai suna sady wai tana bathday yau"shine har yanzun bata dawo ba mommy?meyasama Aka barta taje?"wlh Aliyu magiya tamun bazatayi dare ba"kuma na mata warning k'arfe 6 ta dawo"to Ai harda maryam suka tafi sun sanarwa ummi kece kika Aikesu..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! wato dan ubansu k'arya sukamin?"tashi tsaye yyi yana fad'in muddin magrib tayi suna waje jikinsu zai gaya musu"yana fad'in hakan yafita...
Chapter 19 · 0% Book details