← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 12 OF 65

Sashe 12

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 4 min read

da burgeta sukayiba" sai sukayi kamar masoya....nishin in'am da fad'in wayyo kaina shine yadawo da ita tunanin data lura"sannu zai dena"taji Amon tattausan muryanshi yana driving d'in Ahankali yana kuma satar kallon in'am data jingina bayanta ajikin kujerar"ta lumshe idanuwanta tana rawar sanyi"nafee kuwa sai sannu take mata har suka iso katafaren Asibitin Dr Aliyu"ko parking d'in kirki be gamaba yafito Atare shida nafeesa"yana waya da dr marwan Akan Abud'e masa wani room na musammun"wayar yasaka aljihun jeans nashi bayan yagama"yana bud'e k'ofar cikin taushin muryarsa yace"MARYAM zaki iya fitowa?"shiru tayi"kamar fa bata numfashi ko yaya?"cewar nafeesa dake tsaye bayansa"beyi mgn ba da sauri yazuro kansa cikin motar yana d'ago fuskarta yatsareta da firgitattun idanuwansa yana kallo Atake ya fahimci suma tayi"be furta komai yasureta gaba d'ayan ta yafito da ita dg cikin motar"nafee na mamaki ta rufe motar tabi bayan yaya Aliyu daya wuce reception da wani irin mugun sauri"gaba d'aya masu ganin likita da masu jinya da nurses d'in dake awajen suna kai da kawowa Aka bishi da kallo Ana mamakin wacece wannan me matuk'ar sa'a da dr Aliyu yayi dakonta?"wanda kallo d'aya zaka yimasa ka hango damuwa Atare dashi"kai tsaye Amenity room 10 yanufa da In'am wacce batasan Inda kanta yakeba"suna shigowa ya kwantar da ita samqn bed yana kallon nafeesa data shigo yace"ina zuwa dg haka yafice dg cikin d'akin da sauri"taja ajiyar zuciya tana fad'in ikon Allah wai duk rashin lafiyar in'am d'ince ta tashi hankalin yaya haka??"bata rufe bakiba wata nurse da dr salma suka shigo cikin d'akin"da alama gulma ta kawosu"nafeesa na kallonsu basuyi sallama ba"kuma sunata kallon in'am dake kwance samqn bed"shiru tayi tana jiran taji meye zasuce??.....dan Allah bewar Allah miye matsayin wannan patient d'in Awajen doctor pls?"cewar dr salma sbd ta gane fuskar in'am itace yazo da ita last 2 days harta harareta"nafeesa ta yatsina fuska dan itama ba kanwar lasa bace"tana binsu da wani irin kallo na mamaki tace"duk suna wajen koyon sallama su Amsar tambayoyin naku....bata rufe bakiba yaya Aliyu yashigo da sauri cikin d'akin yana rik'e da wasu ledoji"yana ganin sister hakeema da dr salma yahad'e rai"Atake duk suka daburce"sbd doctor Akwai kwarjinin tsiya"key d'in motarsa ya mik'ama nafeesa yana fad'in kije ki bud'e ki kamun takalmin maryam"dato ta Amsa cikin ladabi ta karb'i key d'in ta fita"tana fita shi kuma yanufi gefen bed d'in yana kallon in'am yazaro abinda zai buk'ata Aledar.....Ayya doctor naga tana jin jiki ko?"banza ya musu yana duba wrist watch nasa batare day a kalli gefen dasuke ba yace"hakeema you are fire! kije khalil yabaki takarda(PA) d'insa"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! na shiga ukku menayi doctor ka koreni?"3 minit na baku kuje ku bani waje"ke kuma saura laifi guda kibar Aiki nan har Abada"yafad'a yana kallon salma"kafin yaci gaba da cewa"Akanme zakuzo kumin tsaye Anan?"kiranku nayi ko kuwa gulmace ta kawoku?"dan Allah kayi hak'uri katai.....karma ki wahalar da kanki kuje ku bani waje"ya k'are maganar cikin zafin rai"yana fad'in hakan yamatsa ya cirema in'am hijab nata duk tayi zufa"hakan yayi daidai da shigowar nafee"jiki Asab'ule su dr salma suka fice"nafeesa ta Ajiye takalmin ta zauna kan wata farar kujera"yaya Aliyu na Aikinsa yana zancen zuci"drip yasaka mata"sannan yamata Allurai guda biyu"kafin yashige bath room"be jimaba yafito da towel jik'e da ruwa"ya zauna Agefen kan in'am yafara danna mata Asaman goshi da gefen wuyanta"yana mata dubarunsu na likitoci sai gashi numfashinta ya daidaita ta bud'e idanuwanta tana ganin jiri da d'akin na juya mata"dg nan kuma bacci ya d'auketa"yaya Aliyu yasaki Ajiyar zuciya ya sauka dg samqn bed d'in ya shanya towel d'in samqn k'ofar bath room"ki zauna da ita zanje nayi sallah"yana fad'in hakan yafita"kai tsaye office nashi ya nufa"bayan ya zauna ya kira ummi"bugu biyu ta d'auki wayar tana masa sallama"ya Amsa yana fad'in ummi abama sulaiman ruwan zafi da Abinci yakawo idan ta farka saita ci"to shikenan Aliyu yanzun zai kawo in sha Allah"sannu da k'okarin d'awainiya"Allah yasaka da Alkhairi.....ummi ki denamun godiya dan Allah"dg haka yakashe wayar yana lumshe ido had'e da shafa tattausan suman kansa fuskar in'am na masa gizo"yad'an saki guntun murmushin daya fito masa da kyawunsa yana fad'in na kasa binne Abinda ke zuciyata game dake *my Angel* raina bani yakeyi kamar zaki guji *me tubarau* naki"Idan kika gano matsayin dakike dashi Azuciyarsa"naso na hak'ura dake Maryam ko dan problems d'in cikin gida Amma zuciyata ta kasa hak'uri"Ayanzun dana furta miki kalmar SO shikenan kin Ida gama rainani"dama Ayanzun fama nakeyi dake....be gama wannan tunanin zucin ba"wayarsa tayi ringing"Abin mamaki yaga safwaan ne"k'in d'aukar wayar yayi"dan shi yau tunda yazo Asibitin bema ganshi ba"baya so idan yana tsaka da tunanin Angel tashi wani ya katse masa"toilet d'in dake cikin office d'in yashiga yayi Alwalah"bayan yafito yatafi masjeed.....
Chapter 12 · 0% Book details