← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 10 OF 65

Sashe 10

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 5 min read

Maryam!* gaban In'am yafad'i tayi saurin fitowa daga cikin motar jikinta na wani irin kirma...."Adaidai lokacin da bahbah ke k'ok'arin jan motar"yayi saurin kallonta da alamar rashin gsky Afuskarsa"saidai kafin yayi mgn harta fice dg cikin motar"ta madubi ya hango Aliyu me tubarau tsaye yana jifar mota da wani irin mugun kallo"atake yak'are ma manyan k'wanjin me tubarau kallo" gabansa yafad'i sbd wani irin shakkarsa da yaji"yatabbatar sukayi Arba dashi saidai wani bashi ba"jiki na kirma yajawo k'ofar yarufe"da wani irin mugun gudu yaja motar jikinsa na b'ari yabar wajen"wanda tun kafin yatafi yaya Aliyu dake tsaye ya haddace number d'in motar....tunda in'am ta fito dg cikin motar yake jifarta da wani irin mugun kallo irin na tuhuma"ak'asan ransa kuma yana jin be yarda da wannan motar ba"ita kanta in'am dukda tana yarinya" yadda taga yaja motar Aguje yatafi ta tabbatar da bashida gaskiya kenan"gaba d'aya sai taji wani irin mugun tsoro Aranta"tama manta data yiwa yaya Aliyu laifi na gudowa da tayi dg office nashi be sani ba.....tana wannan tunanin ta iso gefen motar sa"wanda A time d'in data shiga motar bahbah shi kuma yaya Aliyu ya shigo layin zaiyi parking ya lura da ita zata shiga"shine yafito da sauri sadda bahbah yaza gaya ya shiga yagansa Amma bega fuskar saba" bayansa kawai yagani"shine dalilin daya saka yak'wala mata kira....da lumsassun idanuwansa yatsareta dasu yanata kallonta"Amma fuskarsa Ad'aure take tamau"wanda hakan ba k'aramin kyau da kwarjini yak'ara ma doguwar fuskar tasaba..... k'asa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta"yayinda k'amshin turarensa ke dukar mata hanci"cikin y'ar siririyar muryarta mai cike da yarinta tace"dama yaya bakai bane ka turo wancan mutumin yazo ya d'aukeni??"beyi mgn ba yabud'e driver sit yashiga"itama zaga yawa tayi ta shigo side d'in me zaman banza"sai bayan yatashi motar kafin Anutse yace"miye dalilin daya sakaki shiga waccan motar?"yafad'a kamar bashine yayi maganar ba......sanar masa tayi yadda Akayi"shiru yayi yana tunanin to waye wannan ,kuma meyake nufi akan in'am??"kallonta yayi fuskarsa bbu Alamar wasa yace"bance ki sanarwa kowa komai ba"kina jina?"sannan dg yanzun karki koma yadda ki shiga motar wanda baki saniba koda yace"nine na turosa"dato ta Amsa"motar ta d'auki shiru kowane da irin kalar tunanin dayakeyi"can kuma dr Aliyu yatab'e baki yana fad'in na lura Acikin 2days d'in nan dana dawo Nigeria kin maidani wani Abokin wasanki ko?"ban isa nace kiyi yadda nake soba sai kin mun musu"nace ki bari nazo shine kika tafi?"to yanzun Inda banzoba yatafi dake fa??"ke gaba d'aya in baki sani surutu kika b'atamu raiba bakijin dad'i ko maryam?kanta Ak'asa ta fashe da kuka tana fad'in kayi hak'uri yaya nadena wlh"kaga ko Aji ban shiga ba"duk wannan mugun malamin yadakeni nida sauran
alibai sbd mun makara "ta k'are maganar tana zaro dogayen fararen hannayenta dg cikin hijab"duk sunyi jajir da shatin duka"d'auke kansa dr Aliyu yayi yana tura red lip nasa na k'asa cikin bakinsa yana tsotsa"yayinda in'am ke kukanta"har ta gaji tayi shiru"tama zata bazaice komai ba"bayan shud'ewar wasu y'an mintina sai taji yace"Inda atare dani kika bari mukaje bbu Abinda za'a miki"shi kuma in bacin yana wawa miye Amfanin dukan mace?Idan kunyi laifi su saka kuyi punishment mana"bafa su sakawa yaya"harfa bayana zafi yakeyi"Anjima idan nazo dole na ganshi"duk ranar daya koma dukar mun ke" wlh rayuka zasu b'aci koda kuwa laifi kikayi.....shiru yayi sbd beso maganar ta fito fili ba"in'am kuwa tayi mamakin kalamansa"shi kuwa koma kallonta yayi yace"kimun shiru kona fasa miki baki"ke baki gajiya da kuka"kin mayi break fast Ad'azun?"shiru tayi kanta Ak'asa"Ahankali tace"kaida bbu ruwanka dani "yaushe rabon da kace nayi break yaya Aliyu?"beyi zaton zata fad'i hakan ba"saiya tab'e baki yana fad'in maganata kikeji ne dazan damu da wacce ke mun kallon ina takurata?"zancena dake na k'arshe duk ranar da ina miki mgn kina mun musu aranar zan baki mamakin daban tab'a bakiba"ad'azun meyasa zaki harari wannan yarinyar?"bata girmekiba ?"shiru tayi batace komaiba"shi kuma yaja tsaki yaci gaba da driving nasa"sun kusan isowa gida zasu wuce ya kalleta yana fad'in zakisha ice cream?"ah ah"ta fad'a badan kuma bata soba"sai dan sbd wannan fad'an daya mata"ita kuma tak'i bashi hak'uri"beyi mgn ba yaci gaba da driving nasa"Abakin get d'in gidansu ya tsaya"ta fito dg cikin motar batare data ko kallesaba"shi kuma yajuya akalar motar yanufi Asibiti..... in'am na shigowa ciki" ummi na ganinta ta fahimci kuka tayi"ajikinta tazo ta fad'a tana fad'in dukan makara aka mana yau ummi"kuma wlh yaya yace"saiya musu mgn ko laifi nayi kar akoma dukana"Amma bbu ruwana dashi fa"dan Allah nidai yadena kaini islamiyar kawai....idan kin gama surutun kije kiyi break fast, sai kiyi wanka ki gasa jikinki"yau kece zakiyi Abincin rana"to shikenan ummi zanyi Amma bazan zubama yaya Aliyu ba"kedai kika sani In'am"cewar ummi tana tunanin labarin da in'am ta bata wai zaiyi mgn kar akoma dukanta koda tayi laifi"wad'annan Abubuwan da Aliyu ke nunawa game da in'am masu kama da SO da K'IYAYYA"ranta bata yakeyi son in'am yakeyi ya b'oye ne dai sbd tsoron ummansa da kuma yaga in'am yarinya ce"ita Inda suna shiri da hauwa(umma)wlh zatafi kowa son Aliyu da In'am suso juna har zuwa suyi Aure"sbd kyawawan halayen Aliyu"to tasan da kamar wuya haka yafaru"bataso yafarunma sbd in'am ce kawai y'arta mace Aduniya bara taso ta ganta cikin damuwa da k'unci ba"Amma ta tabbatar wannan takurawar da kulawar dayake mata na SONE"saidai kuma ta fahimci kamar hakan na sakq in'am d'in jin haushinsa.....da wannan tunanin ummin ta tashi ta koma ciki....
Chapter 10 · 0% Book details