← Book details So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 29 OF 65

Sashe 29

So Ne Ko Kiyayya Part 1 Complete Hausa Novel. · about 7 min read

Awashe garin ranar Aka tashi dajin rasuwar mahaifin safwan Alh d'ahiru"Abin mamaki kuma da yamma Akace mijin mama gaje yarasu"Abin yabama dr Aliyu tsoro"yanaso yasanarwa brr Ahmed ganin mama gaje dayayi ta fito A wannan motar ,ga kuma rasuwar mijinta data mahaifin safwaan yakama rana guda"beso ya zurfafa zaton Abinda beda tabbas Akansa"hakan yasa bema brr Ahmed zancen ba"saidai mutuwar mahaifin safwan da Aikin daya Ajiye yak'ara tabbatar musu yana cikin k'ungiyar Asiri tayin kud'in jini dumu dumu...tun bayan rasuwar mlm lawal mama gaje taci gaba da facaka da kud'i"Hamza da zubaida na yawon tambayarta wane irin kasuwancine takeyi haka??

Amma saita nuna musu kud'i Ai Aliyu ya bata tayi had'in gwiwa da wasu y'an company suna kasuwanci"dg zubaida har Hamza basu yardaba"sannan kuma suna mamakin yadda ta nuna mutuwar ubansu ko Ajikinta"Asalima da gari ya waye sukaga gawarsa sai Akace Akaishi Asibiti"ta dinga fad'a tana cewa jayayya sukeyi da hukuncin Allah....

Ayanzun y'an Anguwar suna yawon zund'enta sbd ganin ta canza Amma basuga tana wata sana'aba....
************
kwanci tashi inji masu iya mgn sukace Asaran me rai"In'am da nafeesa na karatu bbu kama hannun yaro"sun gama first term sun shiga second term har Anyi hutu"yanzun da sun koma zasuyi last exams su gama"tsakanin yaya Aliyu da In'am sai hange daga nesa"sai suyi sati 2 basuga junaba"saidai shi kullum saiya ganta lokacin tafiyarta islamiya ko kuma dawowarta"zai zauna Amota yaganta sannan yatafi"Amma yadena shiga gidansu sbd bin umarnin ummansa"gaba d'aya yaya Aliyu yak'ara komawa shiru shiru"ita kanta umma Abinda tayi yadameta"sbd Aliyu dg gaisuwa da tambayarta Abinda take buk'ata bbu Abinda ke k'ara had'asu"sai da dare yazo yamata saida safe...to kusan Abba ma haka yake mata"baya sake mata fuska ko fira da ita"Abincinta baya ci"gaba d'aya itama cikin damuwa take"shi kuwa Abba Aganinsa yi mata zancen Abinda tayi yanzun bashine fa'idaba yabarta sai nan gaba tukum"idan yamata maganar yana ganin zatayi zaton ummi ce tasanar masa da wani Abu game da ita"shiyasa gaba d'aya ya d'auke mata wuta....Abangaren farooq da in'am kuwa duk yadda take k'in kulashi baya fushi haka yake bibiyarta"bbu laifi kuma yanzun tana d'an kulashi"yanaso yafara zuwa gidansu fira wajenta tace"yabari suyi SSCE"yanzun haka Abba yabama yaya sulaiman kud'i dasun koma hutu yasiya musu wayoyi sbd exams......Ayau misalin k'arfe 10:11 am"ummi na zaune a parlourn ta ita kad'ai tana kallon tauraruwa TV"Aka turo k'ofar parlourn Ahankali"mayen k'amshin turaren Aliyu me tubarau yacika parlourn"ummi ta kalli k'ofar da mamaki tana Amsa sallamarsa"ya wanku cikin sabbin suit dark blue"wanda sukayi bala'in haska choco colour d'in fatar jikinsa"kallo d'aya zaka masa kasan hutu da jin dad'in rayuwa had'e da wayewa na yawo A jinin jikinsa"tun dg bak'ar suman kansa zuwa lallausan zagayayyen sajen fuskarsa selk'i da d'aukar ido sukeyi sbd gyaran da suke sha"yana sanye da takalmi sawu ciki dark blue da Agogon fata d'aure A hannunsa"yadad'e da tubarau bak'i"ummi fuskarta Asake take fad'in Aliyu ne?"Eh nine ummi"yafad'a yana d'ukawa ya dafa kujerar dake gefensa yaz are glass d'in yana fad'in ina kwana ummi??lafiya qlau Aliyu fita zakayi ne?"yana satar kallon k'ofar d'akin in'am yace"Eh sallama nazo yimiki ummi"zanje k'asar Cairo nayi wani course na wata ukku nadawo"masha Allah!

Allah yatsare yabada sa'ar Abinda Akaje yi Aliyu"ya Amsa da Ameen cikin jin dad'in Addu'ar tata da ganin k'imarta Azuciyarsa"ya mik'e tsaye yana k'ara kallon k'ofar d'akin In'am Akaro na biyu"ummi na lura dashi tace"kuma baka kirani kasanar mun ba"dako dambun nama ne namaka katafi dashi ko?"karki damu ummi Addu'ar ma dakika mun tayi dan ita nafi buk'ata dg haka yajuya tanata masa fatan Alkhairi yafita....ke In'am! kina ina?"gani ummi"cewar In'am dake lab'e d'aki tana jin maganar yaya Aliyu"fitowa tayi tana gyara d'an kwalinta"maza kije ga yayanku can zaiyi tafiya ki masa fatan Alkhairi ki dawo"dato In'am ta Amsa ta fita k'afarta ko takalmi bbu"tana sanye da lace d'inkin doguwar riga....saida ta had'a da gudu"sannan ta hango yaya Aliyu gab dazai isa bakin get"wanda kuma koda yafito dg cikin parlourn saida ya juyo yaga zaiga in'am? sai "yaga bbu ita"kuma beso yatafi be gantaba"kawai saiya Ayyana Aransa yanzun idan yafita zai turo Auwal yakira masa ita"sbd yaga su Auwal d'in zaune k'ofar gida....yaya Aliyu! takira sunansa da d'an k'arfi"cak! yatsaya"kusan second 5 kafin yajuyo cikin nutsuwa yana kallonta ta cikin eye glass nasa"tamkar tasan kallonta yakeyi"sai tayi k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta"maryam! yafad'a tamkar bashine yayi maganar ba"d'ago kanta tayi taga ya mik'o mata dogon hannunsa guda.....bata san lokacin data tafo Aguje ba ta fad'a Ajikinsa ta fashe da wani irin kuka"wanda kawai tsintar kanta da yin kukan tayi Amma bata san dalili ba......yaya Aliyu wata iriyar kasala da mutuwar jiki yaji lokaci guda"kasan ransa kuma farin cikin kasancewar Ahaka ne"yashafa bayanta cikin tattausan muryanshi yace"kukan na meye my Angel?"idan natafi Ai zan dawo ki dinga ganina ko?....*my Angel*? in'am ta maimaita sunan Aranta"shi kuwa sai bayan ya furta yatuna bata sanba yasaka mata wannan sunan "d'ago hab'arta yayi ta lumshe idanuwanta tana tsuke d'an bakinta"yaja karan hancinta yana fad'in kukan ya isa haka"yafad'a yana saka tafin hannunsa yagoge mata hawayenta"sosai In'am taji kunyar rungumesan datayi"da sauri ta fara k'ok'arin janye jikinta dg nasa"saiya rik'eta yana fad'in harkin gama yin sallamar da yaya Aliyu naki?"turo baki gaba tayi tace"to Amma ai yaya bakace ina nake ba ko?"ta fad'a b'ata fuska"beyi mgn ba yacikata ta dawo gefensa"yazare glass d'in dake fuskarsa"tayi saurin yin k'asa da kanta"gaba d'aya yanayin dayake jin kansa Aciki yahanashi iya furta mata komai"saidai yana ganin tabbas Angel tashi itama tafara jin makamancin Abinda yakeji Akanta....ya d'auki kusan second 10"kafin ya tattaro jarumta cikin cool voice d'insa yace" "maryam!

I'm sorry kinji?"koda baki zoba inada niyar turowa Akiramun ke"da mamaki ta d'ago kanta ta kallesa sbd tunda take dashi be tab'a fad'a mata wannan kalmar ba"yes kiyi hak'uri bance kizo muyi sallama ba ko?"shiru tayi tak'i mgn"to fad'amun waye yaturoki muyi sallamar?"ummi ce"iya Abinda ta fad'a kenan tayi shiru"ki koma gida nizan tafi"Allah yatsare hanya yabaka nassara yaya Aliyu"Ameen" thank you my lil sis"tayi d'an murmushi har beauty point d'inta na lotsawa"ta juya Aguje tabar wajen tana murmushi"shima murmushin yasaki yanajin kamar yabita ya rungumeta"dan wannan hugging d'in nasa datayi sai yaji kamar karta bar jikinsa" saidai yasan rashin dacewar hakan data tuna yasaka ta cikasa...gaba d'aya jinsa yayi cikin farin ciki dajin k'arfin gwiwar tafiyar"yana fitowa dg cikin gidan"mahmood da Abdul hakeem da Auwal suka biyosa suna masa fatan sauka lafiya yamusu Alkhairi me yawa"ya shiga back sit driver yaja suka nufi air port....

In'am kuwa daidaita nutsuwarta tayi sannan ta shigo cikin parlourn"dataga ummi bata nan zaune"saita nufi d'akin ta"samqn bed ta fad'a tayi kwance ta lumshe ido"jikinta nata k'amshin turaren yaya Aliyu"kodai yaya watace dai yake nufi da my Angel??ta fad'a Afili tana tashi zaune"sbd tayi mamakin jin sunan"sannan Ayau yadda yamata mgn cikin taushin murya da sakin fuska Abin yabata mamaki....sai kuma ta tuna kalaman ummi datake fad'in"idan dai Allah yayi Aliyu shine mijinta baki isa ki hana ba.....wai suna nufin sona yaya Aliyu keyi??kai ba haka suke nufi ba"nida yau ne kawai yama fara sakemun fuska"sai kuma tayi shiru tana tuna yadda Asiya y'ar Ajinsu ke yaba kyawunsa da had'uwarsa"har tana fatan inama zai sota"tsaki taja sbd bata san meyasaba idan Asiyar na irin wannan zancen haushi take bata....bata gama wannan tunanin ba nafeesa ta shigo d'akin da murna tana k'wala mata kira"ta kalleta tana fad'in lafiya irin wannan kira??"kefa ba'a miki gwaninta"to yaya Aliyu ne yabani leda biyu d'azun"yace"na baki guda na d'auki guda Amma sai yatafi zan baki"ta fad'a tana mik'a mata babbar leda fara tayin shopping"jikin In'am A sanyaye tace"Amma nafee kinsan ummi fa ta hanan...kinga basai kin nuna mata ba ki Ajiye cikin ward rope naki kawai"tunda dai yatafi babu zancen ki mayar masa"shopping ne yamana wlh"kai yaya yanada kirki sosai"duk wacce ta Auresa taji dad'i"sbd ya had'u ga iya d'aukar wanka"kawai matsalarsa rashin mgn da fara'a da bayayi...shiru dai In'am tayi batace komaiba tana tunani ta fara duba ledar"nafeesa kuwa fita tayi"biscuits, chacoolates,sweets, chiweengum dasu big bom,da snacks"sai turaruka"sai rafar y'an 200 guda 1 daga k'asa"Allah sarki yaya Aliyu"ada ina maka kallon mugu"Amma yanzun kanada kirki"dama banida kud'i"kosu yaya sulaiman nace su bani kud'i sai Anjamun rai"idan kuma nace ummi ta bani tayita tambayata miye zanyi da kud'i?"ta k'are maganar tana sauka dg samqn bed d'in ta d'auki ledar tasaka A ward rope ta rufe......ta nufi bathroom sbd tayi wanka....
Chapter 29 · 0% Book details